Kamin Ka Fada Soyayya:
SHARE 😍
#Tsangayarmalamtonga
Kamin duk wani namiji ya soma soyayya akwai wasu abubuwa masu mahimmanci da zai soma yin la'akari dasu.
Kada kawai namiji saboda yaga mace mai kyaun fuska ko diri kawai sai yace zai soma soyayya ba tare da la'akari da wadannan abubuwan masu mahimmanci ba.
Kamin ka shiga fagen soyayya yana da kyau ka yi la'akari da:
1: Shirin Aure: Akwai mazan da suke fadawa soyayya ba tare da sun shirya yin aure ba. Kawai sai bayan sun shiga tsumdum sun fada tsakiyar kogin soyayya sai kuma su kasa iya auren macen saboda wasu dalilai.
A irin haka ne idan wacce yake soyayyar da ita ta samu wanda ya shirya ta aureshi sai kuma yaje yana kukan an yaudareshi ko kuma wani mai kudi ya kwace masa wacce yake so.
Kada Ka sake ka soma soyayya na gaskiya da mace muddin baka shiryawa yin aure ba. Domin zaka batawa kanka lokacine, ka bata mata lokaci ka kuma cutar da zuciyarka.
2: Dawainiya: Koda mace ba mai tambaya bace, koda mace mai hali ce. Koda mace mai abun yi ce. Dole ne mai shirin soma shiga soyayya ya shiryawa yiwa wacce yake so hidima.
Idan ka zama mai mutum ne marashi, ko marowaci ko kuma matsolo, shiga fagen soyayya ba naka bane.
Harka na soyayya ga da namiji dole ne ya shirya tallafawa wacce yake so da kudi ko da wasu bukatun nata. Wannan yasa dole kamin ka shiga soyayya kasan kana iya yiwa wacce kake so hidima idan kuma ba haka ba kana ji kana gani za a rabaka da ita.
3: Kishi: Dole ne idan kana son mace ka zama mai kishinta. Amma kuma dole ne ka zama mai iya nuna kishin nasa cikin hikima da dabaru ba da hauka ko wauta ba.
Komai munnin macen da kake so dole wani lokacin wani zai mata sallama ko ya nemi zantawa da ita. Ko Kuma a kirata a waya.
Idan hakan ya faru idan baka da hikimar tinkaran matsalar kana iya rasa wannan budurwa taka saboda rashin iya kishi.
Don haka kamin ka fada fagen soyayya ka koyi yadda zaka tinkari yin kishi idan hakan ya kama.
4: Kare Mutuncinta: idan har ba zaka iya Karyewa mace mutuncinta ba kada ka shiga soyayya da ita.
Ita mace tana cikin hidima ne da bukata ako yaushe. Haka nan ana iya bijiromata da wasu lamuran da zasu iya firgitata ko zasu taba mutuncinta. A wannan yanayin dole ne ka shiga ka fita domin ganin ka daidaita lamarin ko kare mata mutuncinta.
5: Hakuri: Tun daga lokacin soyayya zaka soma koyan yin hakuri kamin lokacin aurenka yazo.
Soyayya yana zuwa ne da dadinsa da kuma dacinsa. Don haka a lokacin da dacin yazo dole ka zama mai hakuri da danne zuciya.
Ita mace duk girmanta da kankantarta tana iya gumamaka daga baya ta nuna tamkar babu abunda ya faru. Bayan ta barka kanata kumfar baki da haushi.
Wannan yasa idan har baka da hakuri, kada ma ka soma yin soyayya.
Ba kamar yadda kowa yake hangensa da nesa ba. Kowa gani yake zai iya yin soyayya. Mutanen suna ganin muddin masoya suna son junansu babu wata matsala ko damuwa da zai gifta musu.
Abun ba haka yake ba. Shiga fagen soyayya tamkar shiga fagen yaki ne, dole sai da dabaru da kuma kayan yaki, muddin bakada su cikin sauki za a cika da yaki.
0 Comments