Hanyoyin Da Zaka Farantawa Matarka Rai:
#Tsangayarmalamtonga
SHARE 🌍
Wasu mazan suna da matsala wajen yadda zasu farantawa matansu rai. Akwai masu tunanin baiwa mace kudi ko tara mata kayan abinci a gida shi zai sa mace farin cikin zama da miji. Abun ba haka yake ba.
A darusan da muka soma na hanyoyin da maigida zai farantawa matarsa rai, a wannan karon ma ga wasu hanyoyin da za a daura kan wadancan domin baiwa matan mu annashuwa da nishadi.
1: Baiwa mace lokacin ka ya fi mata komai na rayuwa a duniyan nan. Duk wani abun da zaka yiwa mace musamman matarka amma baka da kokacinta, wannan abun ya tashi a banza.
Idan kana so ka saka matarka farin ciki, yana da kyau ka rika samun lokacin na musamman dominta.
2: Ba sai Sallah ko anko ba. Ya kasance kana yiwa matarka sayyaya na musamman na bazata.
Kada kace sai mace ta rokeka sannan zaka yi mata. A duk lokacin da ka fita kaga wani abu daya burgeka a jikin wata mace, idan kana da hali ka saiwa matarka shi.
Hakan nasaka mace farin ciki da kuma cusa mata kaunarka.
3: Ka zama mai barkwanci a gaban matanka. Kada ka zama kai a kullum baka da wani hira sai na jahannama ko na tsoratarwa. Ya zamana kana shigo da hira na ban dariya da barkwanci domin sanya matarka frinciki. Ka maida kanka yaro ko mara wayo domin kawai ka faranta mata rai.
Hakan na sa mata kara son mazansu da kaunar su.
4: Kada ka bar matarka kullum a kulle a gida bata zuwa ko ina.
Ka samu lokaci na musamman kana fita da matarka yawon shakatawa. Idan da hali ma ku bar garin kuje wani garin jiha ko kasar ma kuna iya bari.
Wannan dabi'ar na farantawa mata rai tare da cusa musu kaunar mazajensu.
5: Yaushe rabonka da cewa matarka kana sonta. Yaushe rabonka da yiwa matarka kyawawan addu'a da fatan alheri. Yaushe rabonka da yabon matarka a gaban mutane da kuna ku biyu?
Mata suna shiga matukar farin ciki idan mazansu suka furta musu kalamai na soyaya. Suka yaba musu bare kuma su musu addu'a na alheri.
Da fatan maza magidanta zasu koyi dabi'u da halayen da zasu rika farantawa matarka rai.
Mace ita ma mutunce kamar yadda kake burin ganin ta faranta maka, itama ya dace ka faranta mata.
0 Comments