Hanyoyin Da Zaki Farantawa Mijin Rai:


Hanyoyin Da Zaki Farantawa Mijin Rai:

#Tsangayarmalamtonga 
SHARE 🌍

Akwai matan dake tunanin cewa ta hanyar Jima'i ne kadai zasu iya farantawa mazajensu rai, wannan ba gaskiya bane. Akwai hanyoyin farantawa maigida dama da wasu matan basusansu ba ko kuma basa amfani dasu.

A darusan mu na baya mun kawo wasu hanyoyin farantawa namiji rai. A wannan karon ma ga wasu hanyoyin da mata zasu iya farantawa matansu rai.

 
1:Duk wani namiji yana son ganin ya isa da matarsa. Duk abunda yace tayi zata yi.

 Idan yace ta bari nan take zata bari. Wannan yakan sa namiji farin ciki da alfaharin matar da yake aurenta.

2: Nunawa mijinki girmamawa musamman a gaban mutane na matukar sanya shi farin ciki.

Maza magidanta suna son ganin matansu suna girmama su ba wai suna tsoronsu ba.

3: Mata da dama basu da dabi'ar yawan sumbatar mazansu. Magidanta maza suna samun natsuwa da farin ciki a duk lokacin da matansu suka sumbace su.

3: Mata na dama suna daukan cewa sune suka fi dacewa a musu kyauta. Wannan yasa da wuya kaga irin matan mu sun sayawa mazansu koda kamfe ne idan sun fita unguwa.

Yiwa mijinki kyauta musamman na wani abun da zai yi amfani dashi a zahiri yakan sa namiji farin ciki na jin dadi.

4: Kamar yadda kike so kulawa, haka shima namiji yake son matarsa ta kula dashi.
Don haka baiwa mijinki lokaci domin kula da bukatunsa na sanya namiji farin ciki. 

5: Mutunta bakin maigida ko naki da musu tarba na mutunci na farantawa duk wani magidanci farin ciki.

Duk matan da ta iya tarairayan baki a gidan mijinta zata mamaye zuciyarsa.
 
Kada ki kasance wata kidahuma wacce batasan yadda zata farantawa miji ba.

Kada ki yarda yawan shekaru ko yara su maidaki tsohuwa. A kullum ki dauki kanki yar shekaru 15 a gaban mijinki.

Post a Comment

0 Comments