hanyoyin da jima’i ke taimakawa wajen inganta kiwon lafiyar mace.



 hanyoyin da jima’i ke taimakawa wajen inganta kiwon lafiyar mace.

Likitocin sun ce yin jima’i lokaci-lokaci na kaifafa kwakwalwar mace, inganta gaban mace yadda koda ta tsufa ba za ta samu matsalar yoyon fistari ba ko rashin iya rike fitsari.

A dalilin haka likitoci ke kira ga mata musamman wadanda suka dara shekaru 30 da su rika yin jima’i akai-akai domin inganta lafiyar su.

Ga Abubuwa 10 da jima’i ke yi ga lafiyar mace:

1. Jima’i na kwantar wa mace hankali.

2. Yana karfafa karfin garkuwar jikin mace da zai rika kare mace daga kamuwa da cututtuka.

3. Jima’i na taimakawa wajen kare mace daga kamuwa da hawan jini da cututtukan dake kama zuciya.

4. Yin jima’i akai-akai na karfafa karfin mara ta yadda koda mace ta tsufa ko ta haihu ba za ta rika samun matsalar rashin iya rike fitsari ba.

5. Jima’i na kaifafa kwakwalwar mace da ke inganta yin nazari da zurfin tunani.

6. Jima’i na Kara wa mace sha’awa.

7. Yana taimakawa mace wajen samun barci mai nauyi musamman ga matan da suka dara shekaru 40.

8. Yana kare mace daga kamuwa da cutar mantuwa da Vinci.

9. Kara karfin kasusuwa.

10. Kara dankon soyayya tsakanin mace da mijinta.

Post a Comment

0 Comments