Wani Abu Daya Kamata Ka Sani Game Da Matarka:


Wani Abu Daya Kamata Ka Sani Game Da Matarka:

SHARE ⏳
#Tsangayarmalamtonga 

Ya dace duk wani namiji ya fahimci wasu abubuwa da suke tattare da dabi'a na mata. Wadannan abubuwan sun hada da:
 
1: Duk Wata Mace Tana Iya Yin Kuskure: Ka zama mai yafewa matarka domin tana iya yin kuskure.

2: Matarka wani bangare ne na jikinka ka kula da ita da kyau.

3: Ka dauki matarka itace abokiyarka takut da kut yi shawara da ita.

4: Matarka itace farin cikinka, ka kyautata mata.

5: Matarka ba baiwarka bace ka girmamata. 

6: Duk yadda matarka take akwai wani na can na sha'awar ta. Rike ta da kyau da mahimmanci.

7: Matarka na bukatar lokacinka. Rabu da latsai latsain wayarka bata lokaci.

8: Matarka nauyinka ce kula da bukatunta.

9: Matarka sarauniyarka ce kada ka kaskantar da ita a gaban mutane.

10: Matar ka itace komai naka. Kada rika mu'amala da ita ba sai lokacin bukata ba.
 
Don haka ka kula da wadannan abubuwan Idan kana son ka samu zaman lafiya a gidanka.

Post a Comment

0 Comments