Yadda Zaki Cewa Namiji Baki Sonshi Cikin Girmamawa:
SHARE 🔮
#Tsangayarmalamtonga
Duk wani bil adama yana son yaga an girmamashi koda kuwa shi bai iya girmama mutane.
Mata musamman 'yan mata, sun samu kansu cikin yanayi na kunci saboda yadda kalamansu ya ja musu fushin wasu mazan da suka musu aiki na asiri.
Akwai matan da ba kawai zasu cewa namiji basa son shi bane kadai. Zasu hadane da bakaken maganganu na cin fuska da wulakanci.
Na ga wacce ta taba cewa wani a gaban mu cewa tafi karfinsa, ita ba ajinsa bane. Yace ya nemi 'yan kauye irinsa ya aura. Yau 'yayansu 7 da shi.
Haka nan nasan wacce har yanzun nan Bata samu mijin aure na saboda bakar maganar data furtawa wani.
Cikin girma da mutuntawa, akwai hanyoyin da mace zata iya cewa namiji bata son shi ba tare da ya ji ciwon abun ba.
1: Kada Ki Bashi Amsa Nan Take: A lokacin da namiji yace miki yana sonki kuma ke ya zamana baki son shi, kada ki bashi wata amsa nan take. Kada ki ce masa kin amince domin ki yaudareshi, kada kuma kice masa baki sonsa.
Nuna masa yayi hakuri ya baki lokaci zaki yi shawara da magabatanki. Cikin girmamawa namiji zai amince kuma ya mutuntaki.
Wannan hanyace cikin ruwan sanyi da zaki kaucewa batawa namiji rai wajen nuna masa baki sonsa.
2: Fadamasa Gaskiya: Ba ina nufin ki ce masa baki son shi ba ko bai miki ba. Nuna masa yayi hakuri saboda wasu dalilai ko hujja da zaki bashi.
Akwai matan da ake musu mijin aure, ko suke fidda miji, akwai matan da iyayensu basu daman yin zance ko hira da wasu mazan ba har sai sun kammala karatu. Idan akan wannan tsarin kike sanar masa cikin girmamawa da bashi hakuri.
3: Kada Ki Sa Masa Rai: Kada ki sake a kalaman da zaki yiwa wanda yace yana sonki baki sonshi samasa rai yadda zai yi tunanin kin amince masa ko zaki amince masa nan gaba.
Wasu matan na nunawa namijin da basu so cewa mutum bayakin mutum. Ko matar mutum kabarinsa. Kalmomin da suke yaudaran maza da saka musu rai nan gaba za a samu fahimta.
Wasu matan zasu gayyaci namiji ko su bashi damar yazo gidansu amma daya zo kuma sai suki fitowa bare ma su saurareshi. Hakan na sanya maza hasala da sanya su bacin rai. Kada kiyi hakan.
Gara neman hanyar kaucewa cikin hikima.
4: Yi Masa Godiya: Kamin ki kawo masa uzurinki, ki soma ne da yi masa godiya da nuna jin dadinki akan yadda duk cikin matan duniya nan amma ya nuna ke yake so. Nuna masa wannan ba karamin karamci bane a wajenki. Daga nan kuma sai ki kawo masa uzurinki cikin sauki.
Wannan hanyar bai bakantawa maza rai saboda karramawa da aka musu musu.
5: Nuna Masa Shi Yayanki Ne Shi: Da zaran kin nunawa namiji kina ganinsa a matsayin yayanki,babanki, ko kawunki, nan take zai fahimci baki da ra'ayinsa bama sai kin furta basai kin ce baki son shi ba.
Wadannan wasu ne daga hanyoyi mafi sauki da mace zata iya kin namiji cikin ruwan sanyi.
0 Comments