๐พ๐๐๐๐ ๐๐ผ๐๐๐..๐๐ผ๐๐ฟ๐ผ ๐ผ๐๐ผ๐๐ ๐๐ผ๐๐ ๐ฟ๐ผ ๐๐๐๐๐พ๐๐๐๐...
Akalla a kowacce shekara ana samun sama da case miliyan daya da rabi (1.5 million cases per year) na cutar infection kuma mafiyawan cases din mata ne. Kuma wadanda kawai sukaje asibiti banda wadanda sukaki zuwa da wadanda ke neman maganin gargajiya (federal ministry of health 2019)
Cutar sanyi ko infection cuta ce da ta addabi mutane da yawa yan sama da shekara 15 mata da maza. Cutar tana kama wajen fitsari ne ga mata da maza..
๐๐๐ ๐ ๐ ๐๐ฌ๐ค ๐๐ช๐ฉ๐๐ง?
1. Kwayoyin cutar bacteria kamar su
Nesseiria gonorrhoea, escherichia coli, streptococcus aureus da sauran grand negative da grand positive bacterias.
2. Kwayoyin cuta na fungus da kashe kashen su..
๐ฅ ๐๐๐ฎ๐๐ฎ๐ ๐๐ ๐ ๐๐๐ช๐ ๐๐ง ๐๐ช๐ฉ๐๐ง?
1. Ana daukan cutar sanyi ne tsakanin macce da namiji, duk wanda keda cutar yana iya likawa wani lokacin saduwa,
2. Ana iya dauka cutar idan kin saka panties din mai cutar ko gajeren wando mai cutar.
3. Idan mai cutar taje toilet ๐ฝ da buta ๐ซta kama ruwa idan hannun ta ya taba gaban ta sai ta riko butar ta fito da ita, ke kuma kika dauki butan kikaje kika taba gaban ki. Kema zaki dauka ta wannan hanyar..
4. Kama ruwa da ruwan dake dauke da wadannan cututtukan ko wanka cikin pool dinda keda gurbatattun ruwa.
Akwai hanyรตyi da yawa da ake iya daukan wannan cuta batare da macce ko namiji sunyi sex ba
๐ฅ ๐ฅ ๐ฅ Amma bincike bai tabbatar da ana iya daukan wannan cuta dafa shiga toilet ba... Kamar yanda wasu kecewa toilet infection..
๐ผ๐ก๐๐ข๐ค๐ข๐๐ฃ ๐๐ช๐ฉ๐๐ง
1. Jin zafi lokacin da ake fitsari
2. Jin zafi lokacin saduwa
3. Rikitarwar alada ga mata
4. Fitar wasu ruwan kamar madara kamar majina masu wari ga mata ko maza
5. Kaikayi ga gaban macce ko namiji
6. Rashin sha'awar jima'i ko daukewar sha'awa ko bushewar gaba ga macce..
7. Jin ciwo a kasan cibiya ga maza ko ciwon gafe gefen ciki ga mata
8. Yawan fitsari akai akai amma fitsarin baya zuwa da yawa.
๐๐ช๐ฌ๐ ๐จ๐ช๐ ๐๐๐ ๐ ๐๐ข๐ช๐ฌ๐ ๐๐ ๐๐ช๐ฉ๐๐ง ๐ ๐ช๐ข๐ ๐ข๐ ๐ฎ๐๐จ๐?
mata sunfi maza saurin kamuwa da wannan ciwon saboda wajen fitsarin macce (urethra) gajeruwa ce kuma tana kusa da farar jikin su (fatar jikin musamman wajen pubic Region waje ne mai saurin gumibda damshi shiyasa kwayoyin cuta suke daddale a wajen.). Maza kuma suna iya kasancewa da cutar amma basu sani ba dan basu ganin alamar komai sai suyi ta zubawa mata cutar.
๐๐๐ฎ๐๐ฎ๐ ๐๐ ๐ ๐ข๐๐๐๐ฃ๐๐ ๐๐ช๐ฉ๐๐ง ๐๐ ๐ ๐ช๐ข๐ ๐ข๐๐ฉ๐๐ ๐๐ฃ ๐ ๐๐ง๐๐ฎ๐?
1. A daina bin mata barkatai ko biyar maza barkatai batare da robar kariya ba
2. Mata a rika canja panties duk bayan wata daya.. Tsaffin ba'a ce kiyi kyauta dasu ba, ki wanke su sa gishiri ki barsu ga rana har tsawon kwana 3
3. Ko yaushe akaje toilet a rika wanke hannaye da sabulu kafin kama ruwa da bayan kama ruwa musamman mata
4. Maza adaina shan magungunan gargajiya da sunann maganin sanyi. Aje asibiti.
5. Mata ku daina wanke gabanku da sabulu musamman dettol, saboda tana kashe normal flora (wato wasu kwayoyin halittu ne masu taimakawa wajen yaki da miyagun cututtuka) kuma ku rika shan nonon shanu, yana taimakawa wajen kara yawan wannan Normal flora din
6. Idan miji yanada cutar to tabbas har matanshi su duka sai kowa yasha maganin kuma zasu kauracewa sex sai bayan anji dama ko kuma idan za'ayi sex din ayi amfani da roba.. Inma yanada budurwa waje itama sai tasha maganin.
7. Koda kunje asibiti an baku magana kun fara shan magani da kawana biyu kukaji sauki toh kada ku daina shan maganin sai ankai 2 weeks.
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA :
https://wa.me/message/2JY5R7B25CTJE1
Copyright BY: Sirrin rike miji
FACEBOOK GROUP: sirrin rike miji
EMAIL: sirrinrikemiji@gmail.com
FACEBOOK PAGE LIKE: sirrin rike miji
WhatsApp: +2348037538596
Follow this link to view our catalog on WhatsApp: https://wa.me/c/2348066627317
JOIN US TELEGRAM GROUP: ๐ท
Zamantakewar aure ga ma'aurata
https://t.me/sirrinrikemij
SHARE ๐ฟ๐
Nagode....๐๐ข๐ ๐ก๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ค๐๐๐
0 Comments