SHARE 💔
#tsangayarmalmantonga
Tabbasa ba duk soyayya bane ake samun yin damar ayi aure ba. Kamar yadda ba duk masoya bane suke zuwa domin yaudara ba.
Sau tari wasu mazan dole ke sa suke rabuwa da matan da suke so amma ba domin son ransu ba.
Akwai dalilai da dama da suke hana wasu samarin samun damar auren macen da suka kamu da sonta. Sai dai kuma yadda zasu iya rabuwa da ita ba tare da sun cutu kuma sun cutar ba shine matsalar.
To ga wasu hanyoyin da zaka iya rabuwa da ita cikin sauki.
1: Da farko ka tabbatar da cewa dalilinka na rabuwa da ita babu son rai, wulakanci ko cin amanarta. Muddin ka tabbatar da hakan a ranka to babu shakka zaka samu saukin cire ta a ranka.
2: Kada ka dauka cewa cikin sauki macen da kake so zata iya fice maka a zuciya a farat daya koda kuwa wani irin laifi ko dalilin rabuwa da ita kake da su.
Ka saka lamarin cikin addu'a. Ka yi da kanka ka kuma sa makusantanka musamman iyayenka su taimaka maka. Sai dai lafazinka na namenan Allah Ya shiga lamarin kada ya zama dole rabuwace, kila akwai abunda yake boye da kai baka sani ba kasancewa da ita din ne yafi maka alheri.
3: Ka yi kokarin nisanta kanka da ita. Idan a kullum sai ka kiraka ko sai kaje wajenta, sai ka rage.
Idan kuma itace ke kiranka, cikin kira guda 5 da zata maka 4 su zama missed call guda daya zaka dauka.
Haka idan sakon text ta turamaka kada ka rika saurin bata amsa.
4: Akwai wasu alfarma ko kyautukan daka saba yi mata ka rage kuma ka sauya lokacin Bata ko yanayin bata. Idan a duk Jumma'a kana bata kyautan dubu 5 kayi Jumma'a 3 baka bata ba. Idan ka tashi Bata sai ka bata dubu 2 kuma a ranar Lahadi na Jumma'a ba.
5: Yi kokari cire ko rabuwa da duk wani abunda kasan suna saurin tana maka ita.
Hotuna, kyautukanta, sakonninta na tex duk suna iya sa namiji ya rika yawan tunawa da macen datake so. Haka zai taimaka maka wajen rage radadin rabuwa da ita.
Kada kayi saurin furtawa macen da kuke soyayya kuma rabuwa ya zama dole zaka rabu da ita. Sai dai idan adalilin wata matsalar data bullo daga gareta ne da aka nemi ku rabu.
Wadannan matakan zasu fahimtar da ita sannu a hankali akwai matsala. Daga nan kuma zata soma shirya zuciyarta akan abunda zai biyo baya.
Da fatan ba za a yi rabuwan baran baran ba.
0 Comments