Shin ana yin amfani da Turmeric (kurkur) tafuskar magani da ƙara lafiya ajiki?
__________________________________________
Ehe,hakika ana amfani dashi,amma bazamu ƙara fahimtar hakaba sai mun ɗan karanta dan karamin bayani akansa da wasi faidodinsa.
Kar kumanta yana da kyau mukoya ma kanmu da matan mu da yayanmu amfani da wasu a abinci, musamman a lokacin da za'a dafa abinci wadannan itatauwa sune;kamar ɗanyar citta,danyan kurkur,ɗanyar tafarnuwa, musamman ɗanyar citta da danyar tafarnuwa domin suna taimaka wa wajen kara lafiya da kuma kariya da kamuwa da wasu cutuka dake kama hanji.
Turmeric yana dauke da wasu sinadarai masu yawa acikin sa yana ɗauke da sinadarin anti-inflamantry da antioxidant.
********************************************
Kuma acikibsa yahada da sinadarin curcumin, don haka ana iya amfani da turmeric don kula da lafiyar alaura,don haka yana kawar da wasu cutuka kamar kumburin gaba,da kurajen gaba etc.
Mu san wadannan fa'idodin turmeric ga lafiyar farji:
_____________________________________________
Amfanin turmeric ga farji
Fitattun fa'idodin turmeric ga al'aura sune kamar haka:
1. Maganin Fungus na Farji.
Curcumin na iya taimakawa wajen kashe yisti na Candida, ko kuma zai iya rage haifuwarsu, saboda yana hana su mannewa ga sel, don haka yana iya ba da gudummawa ga maganin ciwon farji,wato yeast infection,to wannan sinadarin na curcumin akwai shi acikin Turmeric (kurkur)
Yin shayinsa yana taimakawa wajen yakar wasu manyan cutuka kamar colon cancer, prostate cancer,Ko colon of the disease.
Yana taimakawa wajen kewayawar jini,yana kara ma garkuwar jiki karfi.
Yana saukaka matsalolin ciwan kashi daban daban.
Yana yakar taruwar yawan kitse don haka yake saukaka yawan kiba da nauyi.
Kurkur yana ɗauke da sinadarin anti-bacteria,sannan yana hana yawan bushewar jiki musamman ga mata.
Yana saukaka matsalar data shafi gaba ɗaya hanyoyin mafitsara wato Urinary system tun daga cikin koda har zuwa alaura baki daya.
Hakanan ana iya amfani da Turmeric don magance cututtukan da ke shafar farji, wanda ke haifar da zafi da ƙaiƙayi, saboda yana iya rage jin ƙaiƙayi a cikin farji.
2. Sauke alamun PMS
Yin amfani da ruwan 'ya'yan itace na turmeric zai iya taimakawa wajen rage zafi,da wasu matsalolin saboda sinadarin anti-inflamantry dake ciki.
Amfanin turmeric ga farji dangane da yanayin haila shima yana iya kasancewa yana taimakawa:
Rage wasu alamomin da ke haifar da canjin yanayi, kamar:
kumburi.
damuwa.
ciwon kai;
rashin kuzari;
Daidaitawa da daidaita matakan haw hawan haila.
Domin samun fa'idar da ake samu ta hanyar rage radadin jinin al'ada, za a iya shan karamin cokali guda daya tare da madara ko zuma, sannan a ci gaba da wannan al'amarin a kullum har tsawon kwanaki 7 kafin jinin al'ada da kuma kwana 3 bayan gama al'adar.
Amma akan iya haɗa shi da wasu magungunan kamar Ginger da muka kawo jiya, domin ƙara ƙarfi.
Gargadi:
Sannan a kula da Wannan banda shansa adadi mai yawa musamman idan shi kaɗai ne musamman ga mata masu ciki juna biyu,da kuma masu shayarwa,sai dai wanda aka haɗa da wasu itatauwa,shima kaɗan kaɗan ake shansa, sakamakon akwai bambancin da wanda za'a sha zalla.
Gargadi na biyu kada ayi amfani da wanda aka mayar dashi powder,ko akayi masa tiri tare da wasu abubuwan,ɗanye za'a samo Sannan a wanke a kankare kuma,idan ana bukatar garin sa sai ayanka shi sannan abusar dashi.
Amma mu kula da wannan amfani da ɗanyan sa yafi bada faida sosai,sannan musamman a haɗa shi da wasu itatauwa daban to faidan sa yana ninkawa sosai.
Fatan alkhairi gare ku baki ɗaya.
DAGA - Rahamaniyya Islamic medicine and research centre funtua
0 Comments