Wasu Abubuwa Guda 5 Da Zasu Iya Yiwa Aure Rugu-rugu:
SHARE ⭐
#tsangayarmalmantonga
Ba kasafai ma'aurata suke burin aurensu ya mutu ba. Sai dai kuma cikin sauki wasu ma'aurata da dama aurensu ke mutuwa Saboda wasu kananan al'amura.
Kamar wasu darusan mu na baya, yau ma ga wasu abubuwan kanana da manya dabsuke iya lalata aure.
1: Rashin sauki hakkin ma'aurata na daya daga cikin abubuwan da a kullum suke kashe Aure.
Wasu ma'auratan sai ma bayan sunyi aure suke kokarin sanin abubuwan da suka rataya akansu na hakki.
Maza da dama sun dauka muzurai, da kawo kayan abinci sune kadai hakkin daya wajaba akansu.
Mata kuma gani suke su baiwa mazansu abinci da biya musu bukata na Jima'i shi kenan abunda ya rataya a wuyansu.
A rashin sanin wadannan abubuwan ne ake samun matsalar da aure yake mutuwa.
2: Ma'aurata da dama basu iya nunawa matansu ko mazansu jin dadin su akan wani abunda aka musu ba.
Wasu na ganin tunda hakkinsu ne a musu babu bukatar suce sun gode.
Maigida ne matarsa zata dafa masa abinci ta kawo masa yaci ya lashe hannunsa amma bazai iya ce mata abincinta yayi dadi ba kuma yana godiya.
Su kansu matan za a fita a nemo musu kayan abinci da kula da lafiyansu amma bazasu iya bude baki suce sunji dadi ba sun kuma gode. Duk takama ake saboda hakkin ne.
Wannan dan karamin abun da ma'aurata suke rainawa yana da tasiri a zaman aure kuma zai iya lalata aure ga guda daga cikin ma'auratan daya fahimci ba a yaba kokarinsa ko nata.
3: Akwai ma'auratan da saboda yadda suka baiwa junansu 'yanci da yarda sai kuma a samu guda yana neman cutar da guda.
Misali akwai mazan da basai matansu sun tambayesu ba suna da damar zuwa wata unguwa domin biyan wasu bukatu nasu ko kuma na gidan nasu. A hakan ne kuma sai mace ta zage yadda mijinta zai soma samun shakku da rashin natsuwa da ita.
Haka nan ana samun matan da basu damu da inda mazansu zasu je ba, bare kuma damuwa da lokacin dawowansu gida ba. Ba kuma suna hakan bane saboda basason mazan nasu bane, sai domin kudun kada su takura musu. Amma sai gaka cewa namiji yayi amfani da wannan damar yana neman wuce gonarsa da iri yadda har matarsa zata soma samun rashin natsuwa dashi.
Irin wadannan halayen cikin lokaci na iya kashewa ma'aurata aurensu. Kamata yayi ma'aurata suyi amfani da damar da suka baiwa junansu yadda ya dace.
4: Kalamai suna da tasiri tsakanin ma'aurata.
Sau tari kalma ce guda daya ake iya furtawa amma sai auren da akayi shekaru da dama ana zaune lafiya ya mutu.
Ma'aurata su kasance suna amfani da kalaman da suka dace a lokutansu na fara'a ko bacin rai domin gudun samun matsala.
5:Babban matsalar da muke samun cikin Zamantakewar auratayya mu shine fifita, aiyukanmu, kasuwancin mu, sana'oin mu, da harkokin siyasan mu fiye da matan mu ko iyalanmu.
Wadannan dabi'un Baga talakawa baga masu hali ba. Baga mata ba, bakuma ga maza ba.
Yanada kyau duk yadda ma'aurata suke son abunda suke yi kada su banzantar da auratayyarsu.
Da fatan ma'aurata zamu gane kuma mu fahimci shi harkar aure idan bazaka iya kiyaye dokokinsa ba gara zama a yi ba.
0 Comments