Wasu Abubuwan Sani Game Da Mace Akan Soyayya:


Wasu Abubuwan Sani Game Da Mace Akan Soyayya:

SHARE 🔭
#Tsangayarmalamtonga 


Akwai wasu dabi'u, kalamai ko aiyukan da zama suke yi domin neman soyayyar mata sai suki samun shiga.

Ga wasu abubuwan da ya dace duk wani namiji ya sansu game da mata a kan soyayya.
 
1: Mace furta mata kalmar 'Ina sonki" bai mata tasiri kamar yadda zata ga son a zahiri.
Don haka idan zaka shekara kana furtawa mace kana sonta koda kuwa zaka iya cutuwa idan ka rasa ta bazata maida hankalinta a kanka gara ta kula mai nuna mata son a zahiri koda a zuciyarsa ba da gaske yake ba. Mace kenan.

2: Duk macen da bata sanka ba ko bata da wani tsammanin soyayya daga gareka. Kana furta mata kalmomi irinsu "my dear, my love, sweetheart". Maimakon ka sata farin ciki bata mata rai zaka bata mata rai ne kawai amma ba tasiri kalaman zasu mata ba a karo na farko kamar yadda wasu mazan suke tunani. 

3: Mace bata son takura daga lokacin da ka furta mata kalmar kana sonta. Ko kuka soma soyayya sabo-sabo ka soma takurata ko kafa mata wasu dokoki ko ka'idoji. Mata basa son hakan.

4: Ba kamar yadda maza suke cewa mata suna son a musu karya kamin su amince da soyayar namiji. Wannan ba gaskiya bane.
Duk wata mace tana dauka duk wani abunda mai sonta zai fadamata gaskiya yake fadi, wannan yasa wasu mazan suke zuwa da kalaman karya amma ba wai saboda mace na son a mata karya ba.

Duk mace tana son namijin da zai fadamata gaskiya. Misali kace mata kana da mata. Ko ka taba aure, ko kanada wacce kuke soyayya yanzu da ita amma akwai matsala.

Idan zaka fito fili ka cewa mace ga aikin da kake yi ko ga abunda kake samu. Muddin ta fahimci gaskiyar ka kake fada hakan bazai hana ta soka ba. Amma ka yiwa mace karya bayan shekaru 10 ta gane sai taji ta tsaneka. Mata kenan. 

5: Maza suna yiwa mata kallon cewa da sun latsa ta zata Bada kai ayi zina da ita. Tabbas mata suna da sha'awar Jima'i suma. Amma ba duk mace bace namijin da bata so ya bata sha'awa ba.
Kashi 70 na maza cikin 100 zasu iya haduwa da macen da basu santa ba suyi sha'awar yin zina da ita. Wannan dabi'ar ga maza dai-dai ne.

Su mata kaso 80 nasu sha'awa baya sasu yin Jima'i dana mijin dabasu sanshi ba. Sai dai soyayya. Mace idan ba karuwance take na sana'a ba bazata taba yarda da namijin da bata son so ba.

6: Mata sunan son kulawa. Yawan kulawa da mace zai sa taji tana sonka koda babu soyayya a tsakanin ku. Haka kuma duk tsananin soyayyar da kuke yi da mace tana iya rabuwa da kai idan baka kulata.

7: Mata basa son namiji mai nuku nuku. Wanda yake boye masu wani abu.
Muddin zata zama mai budewa mace wasu sirrukan, zaka ji ita ma bazata boye maka komai nata ba.

8: Duk irin kwalliya da shiga da mace zata yi. Tanayi ne saboda wanda yake sonta ko take so ko suke soyayya ya gani.
Idan duk mazan duniyan nan zasu yaba da kwalliyar data yi muddin ba kaine ka yaba ba, bakin ciki zata kwana dashi.

9: Maza suna daukan mata duka halayen su da dabi'un su duk daya ne. Mata suna bambamta a hali da dabi'u. Kawai abunda zakayi kayi kokarin gano yadda taka take sai ku zauna lafiya.

10: Duk irin yadda dabi'un mace suke ko halinta, tana iya sauyawa ta dawo yadda namiji yake son ganinta muddin dai tana sonsa.
Wannan yasa cikin sauki wasu mazan suke koyawa 'yan mata shaye shaye. Haka nan kuma ana samun mazan da suke gyara dabi'un wasu matan saboda soyayyar da suke musu har ma su auresu.

 
Da fatan wannan darasin zai taimakawa maza wajen yin mu'amalar su da 'yan matansu ko zaurawansu.

Post a Comment

0 Comments