Matakai Rashin Mutunci Da Maza Suke Yiwa Matansu Idan Zasu Yi Saki:


Matakai Rashin Mutunci Da Maza Suke Yiwa Matansu Idan Zasu Yi Saki:

SHARE 👥
#TsangayarMalam 

Kusan kashi 60 na mazan da suke sakin matansu suna dawowa suyi ta binsu da neman su dawo musu.
Wasu matan saboda irin yadda namijin yayi mata saki na wulakanci take kin yarda ta sasanta da shi.

Ga wasu matakan da ya dace kabi kamin ka saki matarka.
 
1: Kada ka sake ka saki matarka ba tare da bata damar ta gyara laifinta ko kuskurenta ba.
Wasu mazan da zaran matarsu ta musu abunda bai dace ba ko abunda basa so kawai sai saki kai tsaye. Duk namijin da yayi irin wannan saki sai ya dawo yana bin matarsa ta dawo masa. 

2: Akwai mazan kwata kwata basa shigowa da wakilan matansu ko wasu na kusa da ita da take jin maganarsu a lokacin da suke da wani matsala. Haka nan kawai sai dai suji ya sakar musu 'ya ba tare da basu damar shigowa cikin matsalar domin gyara.
Irin wannan sakin yana sa namiji ya gane kurensa bayan ya yinshi. Hakan kuma bai dace ba. 

Ka ta tabbatar da ka baiwa waliyan matarka dama har sai idan abun yafi karfinsu.
 
3: Ana samun mazan da suke yin saki babu wani dalili saboda nuna isa kawai. Wasu kuwa abunda sukayi sakin akai bai kai ya kawo ba amma sai su furtawa matansu kalma na sakeki.
Dole ne, kamin namiji ya saki matarsa yasan cewa yana da hujja kwankwara da zai iya fada a gaban kowa. Ba sai yayi kuma daga baya ya rika cewa hannu aka sa masa bai ma san yayi ba. 

4: Akwai mazan da suke sakin mace cikin fushi ko bacin rai. Duk namijin da yayi hakan kuwa daga baya sai ya gane kurensa.
Bama saki ba, ko abunda bai kai saki bane kada ka taba yinsa a lokacinda ranka yake bace. Ka natsu kasan abunda kake yi kamin kayi sakin.

5: Haka nan akwai mazan da suke sakin matansu a gaban iyayensu ko waliyansu. Wannan cin fuska ne bai dace ba. Koda kuwa shi ya nema kada kayi hakan.
Sakin mace a gaban iyayenta tamkar ka samu yaro ne da bai maka laifin komai ba a gaban iayensa ka rika zamga masa bulala. 

 
Wadannan wasu ne daga cikin sakin da maza suke yiwa matansu na rashin kyautawa. Zamu ci gaba da kawo su a darasi na gaba.

Post a Comment

0 Comments