Kada Ka Kuskura Ka Furtawa Matarka Wadannan Kalaman:
SHARE 👵
#TsangayarMalam
Akwai wasu kalamai da ko a wasa bai kamata ka furtawa matakarka su ba. Amma ana samun wasu mazan da kai tsaye ko shakka basa ji suke furtawa matansu su.
Idan kana son zama lafiya da girmamawa da matarka. To ka guji furtawa Matarka Wadannan Kalmomin kamar haka:
1: Baki Iya Kwalliya ba: Bama matarka ba, ko kanwarka ka fadawa wannan kalmar sai kunyi gaba na dan lokaci. Don haka kula, kada ka sake ka furtawa matarka wannan kalmar.
2: Baki da kyau: Shima yana cikin bakaken kalmar da mata ba sason jinsu daga bakin mazajensu.
Mace duk muninta a wajen mijinta ya dace ace tana da kyau gani. Don haka ka kula.
3: Kinfi karfina: Kalmace dake nunawa mace bata jin maganar mijinta. Don haka duk abunda ya dorata akai bata hawa.
Koda hakan ne wannan kalmar ba zai taimakawa wajen gyarata ba sai ma ingizata ta ci gaba da maka rashin dacewa.
Mata masu natsuwa sun tsani mazansu su furta musu wannan kalmar.
4: Na So Ace Na Auri Mace Mai Iri Kaza: Furtawa matarka wannan kalmar tamkar cin fuska ne da kuma nuna mata ba irinta kaso ka aura ba.
Hakan bai dace ba ga duk wani namijin kirki ba ya furtawa matarsa wannan kalmar.
5: Zantukanki Babu Mai Dadi: Baki iya hira ba, bakinki kamar kashi. Dukkanin wadannan kalaman basu da kyau ka furtawa mace su.
Idan macece mai sakin magana ce ba tare da la'akari da wanda take magana dashi ba nuna mata yadda ya dace tayi amma ba furta mata bakar magana ba.
6: Kinada Bakin Hali: Tabbas akwai mata masu wannan halin. Amma mundi aure ya hadaka da ita, dole taci albarka aure ka sakaya furta mata irin wannan kalmar kai tsaye.
7: Kanwarki Tafiki Kyaun Hali: Kalma ne na shiga tsakanin matarka da 'yar uwarta. Kalma ne da zai iya jawo zargi da rashin natsuwa da kanwar matarka da matarka zata shiga.
Furtawa matarka wannan kalmar tamkar kana nuna mata cewa zaka iya rabuwa da ita ka auri kanwarta idan mara aurece.
8: Baki Da Mutunci: Kalma ne na cin mutuncin matarka kai tsaye. Kalma ne da zaka tunzura mace ta maida maka martani. Don haka ka kiyaye furtawa matarka shi.
9: Haka Aka Koya Miki: Kai tsaye zagin iyayen matarka ne amfani da wannan kalmar.
Kalmace na cin mutuncin surukanka da suka amince maka suka baka yarsu. Fadawa matarka wannan kalmar babu daraja ko mutunci a cikinsa.
10: Baki Da Daraja A Wajena: Abunda ya bambamta wannan kalmar da saki niya. Kalma ne dake nuna ka yi sallama da matarka. Kalamin yana nuna tamkar babu ruwanka da ita duk abunda zata yi taje tayi.
Dukkanin wadannan kalaman ko da wasa ba kalmai bane da magidanci zai furtawa matarka komin irin bacin rai daya shiga.
Da fatan maza magidanta zasu rika amfani da hanyoyin gyara ne ba batancin ba.
0 Comments