Wasu Abubuwa Masu Mahimmanci Da Suka Dace Ma'aurata Su Fahimce Su:


Wasu Abubuwa Masu Mahimmanci Da Suka Dace Ma'aurata Su Fahimce Su:

SHARE 💏
#Tsangayarmalamtonga 

Akwai wasu abubuwa kanana da muke manta dasu ko bamu cika daukansu da mahimmanci ba a al'amuran zaman auren.

Wadannan abubuwan kuma da zamu rika kula dasu zasu Inganta mana rayuwar aurenmu.

Wadannan abubuwan ga su kamar haka:

1: Ma'aurata su daina daukan kansu sun tsufa ko sun girma da nunawa junansu kauna da soyayya irin na baya.
Duk yawan haihuwa ko shekaru bai kamata ace sun hana ma'aurata mure soyayyar junansu ba.

2: Yana da kyau ma'aurata su rika yiwa junansu nuni akan wani kuskure da guda yayi akan sani ko kuma da ganganci.
Duk wani abunda guda yayi da bai yiwa guda dadi ba su nuna korafinsu cikin mutuntawa da kaunar juna.

Wani lokacin akwai wasu abubuwan da za a ga ma'aurata guda na yiwa guda da basa son abun amma sai su kasa fitowa fili suyi magana. Wannan ba tsari bane na zaman tare. Fito fili yi bayani domin neman gyara.

3: Wani abun mamaki za a ga ma'aurata sun jima suna zaman aure amma da wuya su iya fadin halayensu.

Yana da kyau mace ta fahimci halayen mijinta haka shima. Wanda da zaran yayi ko tayi wani motsi kawai zasu fahimci junansu.

Hakan yana sa ma'aurata su kaucewa batawa juna rai a cikin mutane ko kuma su dadadawa junansu. Domin da zaran guda yayi wata inkiya ko nuna alamun da jikinsu. Dole guda ya fahimci abunda guda yake so.

4:Idan ma'aurata suka yiwa junansu laifi su yi kokarin neman yafiya tare da alkawarin bazasu sake aikata wannan abun ba.
Rashin iya baiwa juna hakuri wani lokacin akan karamar lamari sai ya dawo babba. Ya dace ma'aurata su koyi baiwa junansu hakuri.

5: Sau da dama za a ga ma'aurata suna boyewa junansu abunda ya kamata su sanarwa juna. Kuskure ne babba yin haka saboda halin mutuwa.

Akwai matan da suna sana'a ko wani harkar kudi da mazansu basu sani ba. Wasu matan ma sun mallaki kaddarori amma duk suna biyewa mazansu na aure. Wannan kuskure ne babba.

Haka suma mazan sau da dama suna aikata irin hakan ga matansu na aure. Wasu ma aure suke karawa ba tare da wacce take gidan ta sani ba.

6: Ana samun iyayen da basa nunawa 'ya'yansu mahimmancin junansu.
Wata uwar idan itace Allah Yayiwa wadatar samu fiye da mijinta sai ta yita yin dabi'un da yaran zasu fahimci ita ce take musu komai ba ubansu ba. Wasu matan ma har zagin mazajen nasu suke yi na rashin katabus a gaban yaransu. Wanda hakan zai sa yara su daina ganin girman mahaifinsu.

Haka nan wasu mazan duk kuwa da dawainiyar gida akansu yake. Sai sun nuna isa da gadara akan wani abun da zasu yiwa matansu a gaban yaransu tamkar wani alfarma suke yiwa matan nasu.

Ana samun mazan da duk wani abunda suka yiwa matansu sai gori ya biyo baya. Akwai ma masu fadin kalamai marasa dadi ga iyayen matansu. Duk irin wadannan abubuwan dole ma'aurata su kiyaye su.

7: Kada ma'aurata su kasa fitowa fili su sanarwa junansu irin abubuwan da suke bukatar guda yana musu, da abubuwan da basa so kamin lokacin da za a aikata wanda ba a son. Shi kuma wanda akeson idan anyi sai a yabawa juna.

8: Kada ma'aurata su dauka sunyi tsufan da bazasu rika yiwa junansu kwalliya ba. Haka nan su daina fita unguwa ko yawon ziyara saboda yanzu sun haihu ko sunyi shekaru.

Duk yawan shekarun mace ko namiji suna bukatar wanda zai nuna musu soyayya na gaskiya baya ga na abunda suka haifa. Don haka yana da kyau wasu abubuwan da aka saba yi ana ango da amarya bai kamata a watsar dasu ba saboda an jima da yin aure ba.

9: Akwai wani lokacinda mutum yakan tashi yaji bayajin dadin komai, ya kuma rasa abunda yake masa dadi. Muddin ma'aurata sun fahimci junansu, suna da hanyoyin dadadawa juna a irin wannan yanayin. Ba yanayi bane da guda zai dauka saboda shi gudan yake hakan. Wannan yanayi ne da yake samun Dan Adam komai gatansa domin a nuna masa zaman duniya ba daidai yake da Aljanna ba.

10: A lokacin kuka tabbatar da kuna kara shekaru a zaman aurenku. Ku tabbatar kuna kara neman kusanci da Allah.
Kada ku zama iyayen dake koyawa yaransu zuwa wajen bokaye da maluman tsubbu. Ko koyawa yaransu zalunci da makamantansu.

Ku zama iyaye masu neman kare kawunansu dana Iyalansu daga wutan jahannama.
 
Wadannan sune wasu abubuwa kanana da manya da ma'aurata basu cika kula dasu ba.

Da fatan za a kula.

Post a Comment

0 Comments