Bambamcin Dake Tsakanin Masoyin Gaskiya Da Makaryacin Masoyi:


Bambamcin Dake Tsakanin Masoyin Gaskiya Da Makaryacin Masoyi:

SHARE 💕
#Tsangayarmalamtonga 

Muddin namiji ko mace bazasu iya bambamci tsakanin masoya na gaskiya dana karya ba, a kullum zasu rika fadawa cikin matsaloli na soyayya.

Ga wasu hanyoyin da maza da mata zasu iya bambamci masoya na gaskiya dana karya. Duk da darasin yafi karkata ne ga mata. Amma akwai wasu alamomin da maza ma zasu iya amfani dasu.

 
1: Matsoyina na gaskiya yana iya yin komai akanka domin ganin ya biya maka bukatarka.
Amma shi mai soyayya na karya kansa kawai ya sani. Duk wani abu na matsala idan ya taso baza a ganshi ba sai abun ya wuce.

2: Shi mai sonki da gaske ba zai taba furta miki kalamai na karya ko na yaudara ba koda wasa ne.
Amma shi makaryacin masoyi baida abunda fadi sai na karya da yaudara.

3: Duk wani mai sonki na gaskiya zai rika tausaya miki.
Amma shi makaryacin masoyi baida wani aiki sai gallazamiki da kuntata miki.

4: Duk wani mai sonka zaka same shi yana da hakuri kuma yana maka uzuri.
Amma shi makaryacin masoyi komai nasa na fushi ne da bata rai da son ayi fada.

5: Idan namiji na sonki kwantar da kansa kasa yake komai matsayinsa da girmansa.
Amma shi makaryacin masoyi gadara, takama da nuna miki isa sune dabi'un sa.

6:Ita macen data son namiji da gaske zaka sameta da yaba kyauta komai kankantar sa.
Amma macen da son karya take maka, duk abunda zaka mata sai ta raina ga rashin godiya.

7: Idan namiji na sonki da gaske zai rika girmamaki da mutuntaki.
Amma shi masoyin karya baya ganin darajarki da mutunci a sarari da boye..

8: Idan ana maka so na gaskiya zayi kokarin kare mutuncinka ne a duk inda ya kama.
Amma idan soyayyar karyar ce sune ma zasu soma jawo zancen da za a cimaka mutuncin.

9: Idan mace tana maka so na gaskiya cikin karamin lokaci zata yi kokarin ganin ta fahimceka.
Amma ita wacce bata maka so na gaskiya ko lambar wayarka bazata iya kawowa a kanta ba bare ta fahimci wasu halayen ka.

10:Duk wani mai sonki na gaskiya bazai taba nuna miki rashin yarda ba ko zarginki.
Amma namijin dake miki karyar so a kullum cikin rashin yarda dake yake saboda yawan zarginki.
 
Wadannan sune wasu alamun da mata da maza da suke soyayya zasu iya tantance mai so na gaskiya da na karya. Haka nan masu sonka a zahiri na rayuwa da masu cewa suna sonka a baka.

Allah Ya sada mu da masu sonmu na gaskiya .

Post a Comment

0 Comments