Yadda Zaka Shawo Kan Budurwa Ta Wayar Hannunta:


Yadda Zaka Shawo Kan Budurwa Ta Wayar Hannunta:

💕
#Tsangayarmalamtonga 

Lokaci na zamani ya kawomu da duk wani al'amarin rayuwa ya koma a wayoyin hannun mu. Haka nan ma yin hira da mace ya dawo ta kafafen sada zumunta na zamani.

Sai dai ba duk maza bane suka san yadda zasu tinkari 'yan matan da suka gani suna so ta wadannan hanyoyin sadarwan ba. 

Mukadda kada lambar Whatsapp dinta, kuna abota a Facebook da sauran mahajojin sadarwa na zamani, yanzu kana shirin soma tura mata sakonni ne na kokarin jan ra'ayin ta da hankalinta domin ta soka. Ga yadda zaka yi. 
 
1: 🤳 Akwai wasu mazan da sallama suke soma yiwa mace suna jiran ta amsa musu daga nan sai su ci gaba da wani sakon. Idan wannan shine dabaranka zaka shekara kana yiwa mata sallama da kyar zaka samu ta kirki da zata amsa maka wannan salaman naka. 
Kana mata sallama wurga mata wata tambayar da dole sai ta amsa maka tambayar idan bazata amsa sallamar ka ba. Duba profile dinta ko status dinta bazaka rasa abunda zaka mata tambaya mai ma'ana akansa ba.

2: 🤳 Samu wani abunda zai sata dariya, labari ko video ka tura mata. 
Kada ka damu da sai ta amsa maka alamun ya sata dariya ko a'a. Muddin ka tura mata hada mata da gaisuwa ba tare da ka jira amsar ba, gobe ma ka sake mata hakan. 
Mata basa manta abunda ke sasu dariya da ko wanda ke sasu dariya. Sa mace dariya yana daya daga cikin hanyar da zai sa ka samu kusanci da ita.
 
3: 🤳 Akwai wasu samarin da mace ta soma kula su sai su soma neman ta tura musu hotunan tsairiaci ko su sunemi tura mata bidiyon shashanci. 
Mace ko 'yar iska ce idan ba ita ta soma nuna maka hakan ba kana iya rasata da wannan wautar da akasarin maza suke yi ciki harda manyan mutane. Ina nufin maza masu shekaru. 

4: 🤳 Kada ka matsawa mace da yawan tambayoyi a farkon soma hiranku muddin ba itace ta bukaci hakan ba. Yawan mata tambaya zai sai ta soma tunanin akwai wani abu daban da kake nemanta da shi amma ba soyayya ba.

5: 🤳 Wasu mazan da sun fahimci mace ta soma basu hadin kai tana hira dasu sai su shiga ja mata aji, idan tayi tura sako sai su jima basu amsa ba. Idan sun tashi bada amsar babu bada hakuri bare kawo uzurin dayasa basu amsa da wuri ba.

Mace na iya watsi dakai a farkon soma hiranku idan ta fahimci kanada wannan matsalar.

 
Zamu ci gaba..............

Post a Comment

0 Comments