Wasu Abubuwa 10 Da Zaki Mallaki Zuciyar Masoyinki Dasu:


Wasu Abubuwa 10 Da Zaki Mallaki Zuciyar Masoyinki Dasu:

SHARE 💕
#Tsangayarmalamtonga 

Farat daya soyayya zai iya shiga mutum. Amma kuma samun damar mallakar wannan zuciyar da ake so sai an hada da wasu aiyukan.

Ga wasu abubuwa guda 10 da duk mace zata yi domin mallake soyayyar masoyinta dasu.

 
1: Kada ki kira masoyinki da sunansa shine mataki na farko na mamaye zuciyarsa.
Duk wani namiji yanason yaji mai sonsa ta sa masa suna na musamman da zai rika alfahari da shi. Don haka ki samu suna mai dadin ji da fadi ki sakawa mai sonki.

2: Kada ki sake kiyi shigan rashin mutunci a duk lokacinda zaki hadu da mai sonki da aure.

Mazan da suke son mace tayi shigar banza sune mazan banza da suke son fita da mace yawon banza domin zuwa wajen banza. Amma shi mai son aurenta kishin ganin wani bangare na jikin ta ya bayyana yake yi.
Don haka kada ki sake ki yi shigan banza maisonki da aure ya gani. 

3: Girmama mai sonki yana tsarin da zaki iya sace zuciyar shi da shi.
Babu inda namiji ke burin son auren macen da bata ganin girmansa muddin wannan namijin mai hankali ne.
Don haka nunawa wanda zaki aura girmamawa zaki samu damar shuga ransa.

4: Akwai wasu shawarwarin da mai sonki da aure yake fatan kiyi dashi. Musamman wasu abubuwan da suka shafi kamin aure da bayan aurenku.

Yawan neman shawaran mai sonki akan irin wadannan mahimman abubuwan sukan sa namiji yaji kin kwanta masa.
 
5: Akwai 'yan mata shazumamu. Su dai a basu. Irin wadannan matan gani suke mace tayiwa namiji kyautan wani abu na soyayya tamkar yada kai ne. Wannan tunanine na mace dakikiya. Babu zuciyar da bata son a mata kyuta, kamar yadda kike so a miki kyauta haka nan mai baki yana son ki masa kema.

Ba ana magana akan kyauta na kudi ba. Ko tsummar goge fuska kika saya kika baiwa mai sonki sai yaji dadi. Wannan yasa yiwa mai sonki kyauta yake cikin jerin abubuwan da zaki iya samun soyayyar sa.

6; Ki guji yawan bani bani ga namiji mai son aurenki. Duk yadda namiji ke sonki kina iya koransa da bani bani.
Ba ana nufin budurwa bata neman kudi wajeb mai sonta ba. Abun nufi shine kada ta tsanwala ya dawo tamkar ATM ta maidashi. Hakan zai iya koran namiji. Rashin hakan na iya jawo miki mutunci da kauna a wajen sa.

7: Wasu matan basu fahimci cewa shima namiji idan yayi kwalliya yana so budurwa sa ta yaba masa ba.
Nuna masa yadda shigan ya masa kyau. Zuga irin garin hulansa agogonsa ko takalminsa, yaba turaren daya fesa, saboda ke yayi wannan shigan. Idan kina yiwa namiji haka zaki samu soyayyar sa. 

8:Ki zama mai yawaita godiya ga mai sonki da aure ga duk kankantar abunda ya miki na alheri koda da fatar baki ya miki.
Yawan yiwa mai sonki godiya, a kullum zai kasance cikin son ya baki. Zai rika marmarin ganin ya miki. Zai so yaji kin tambayeshi wani abun. Don haka ki kasance da wannan dabi'ar nan take zaki sace zuciyar namiji. 

9: Ki kasance mace mai sakin fuska tare da yin raha ga namijin da zai aureki.
Kada ki kasance a kullum fuskar ki a murtuke kuma babu eaha a tare dake. Hakan na iya sa namiji ya sauya tunaninsa akanki koda kuwa kina sonshi a ranki.
Duk namiji yanason ganin matar da zai aura mai sakin fuska ce da raha idan ya kama.

10: Ki tabbatar da cewa ki kauce aikata duk wani abun da za ace miki Allah wadai na rashin kyautawa.
Namiji yana son jin macen da zai aura ana yabonta da halaye na gari da kuma kamun kai. Don haka cikin sauki sai ki mamaye zuciyarsa.
 
Wadannan wasu daga cikinsu. Da fatan mata zasu yi amfani dasu domin amfanin kansu.

Post a Comment

0 Comments