Ki Kaucewa Yin Wadannan Abubuwan Idan Ba So Kike Ki Kori Mai Sonki Da Aure Ba:


Ki Kaucewa Yin Wadannan Abubuwan Idan Ba So Kike Ki Kori Mai Sonki Da Aure Ba:

SHARE 💕
#tsangayamalamtonga 

Wasu kananan abubuwa da baki ma san zasu iya zameki matsa a soyaya ba sai ki ga sun zama.

Irin wadannan kurakure mazan da sukasan abunda suke yi basu cika kauda kai a kansu ba muddin suka fahimci mace da su.

Ga wasu abubuwa kanana guda 3 da zasu iya koran miki manemin aurenki.
 
1:Waya: Wayar hannun nan da kike gani zai iya rabaki da wanda kike so har abada.
Mazan da sukan ciwon kansu suna auna macen da suke so ne da aure ta yadda take amsa wayoyin wasu mutane idan suna tare da ita.

Wasu matan basa jin kunyar sheka karya idan suna waya da wasu mazan na daban. Akwai mazan da suke yiwa wadanda take waya da shi tsawa ko nuna isa da gadara, duk wannan yana kallo. Ba burgeshi kike ba.

Wasu matan idan suna hira da mazansu banda charting da wayansu babu abunda suke yi, bama sa baiwa mai son nasu hankali da lokaci domin yin hira. Wannan dabi'ar na iya koran miki namiji.

Sannan akwai matan ko mace mai kasuwancin aikin banki bata kaisu daukan waya ba. Duk lokacin da mai sonta zai kirata tana waya da wasu. Idan ma yana tare da ita kowa ma kiranta yake. Idan wannan halin naki ne ina tabbatar miki zaki kori maisonki.

2: Musu: Akwai matan da suke da dan karen musun tsiya har akan abunda ma basu sani ba yi suke kawai saboda girman kai da kada a nuna rashin wayewarta.
Akasarin masa basu da dabi'ar jimre yin musu da mace koda kuwa ta fisu hujja. Maza sukan dauki mace mai yawan musu tamkar matar da bazata yi biyayya bane ga mijinta, wannan yasa idan namijin da yasan abunda yake ya fahimci kina da musu, zai iya cikawa wandonsa iska koda kuwa ya kai kudi gidanku. 

3:Mita: Maza suna matukar tsoron mace mai mita. Mata masu mita suna daya daga jerin matan da suke kashe mazajensu da ransu. Gara mace mai musu da auren mace mai mita.

Don haka kI guji yawan mita a matsayinki ta mace. Duk abunda akayi idan ya wuce a manta da shi a kiyaye gaba. 
 
Wadannan sune wasu daga cikin kananan abunuwan da zasu iya koran miki manemi kamin ki ankara. 

Da fatan zaku kiyaye musamman 'yan mata da kansu ke fuska ba zaurawa ba da ana samun sauki na irin wadannan dabi'un daga garesu.

Post a Comment

0 Comments