AMFANI GUDA TARA (9) DA GYEDA KE YI A JIKIN MUTUM:


AMFANI GUDA TARA (9) DA GYEDA KE YI A JIKIN MUTUM:

Mafi yawa daga cikin mutane ba su da masaniya kan amfanin da gyada ke yi a jikin mutum.

Gyeda da muka raina tana dauke da sinadarai na nutrition kamar haka:
- Calories
- Protein
- Fat
- Carbohydrate
- Calcium
- Phosphorus
- Iron
- Thiamine (B1)
- Riboflavine(B2)
- Niacin

Ga amfanin gyeda a jikin dan Adam:

1. Gyada na kare mutum daga kamuwa da cutar bugawan zuciya.

2. Gyada na dauke da sinadarin ‘vitamin B3’ wanda ke taimakawa wajen hana mutum mantuwa.

3. Yana dauke da sinadarin ‘Phylosterols wanda ke kare mutum daga kamuwa da cutar daji.

4. Yana kuma kare mutum daga kamuwa da cutar siga.

5. Ana samun sinadarin ‘Folate’ wanda ke bunkasa kiwon lafiyan mata masu ciki.

6. Gyada na kara karfi a jiki.

7. Yana bunkasa girman jikin mutum musamman yara domin yana dauke da sinadarin ‘Protein’.

8. Gyada na gyara fatar jikin mutum da hana saurin tsufa saboda akawai sinadarin ‘vitamin E’ a ciki.

9. Gyada na faranta wa mutum rai musamman masu yawan fushi.

Lafiya uwar jiki

Post a Comment

0 Comments