Magunguna 5 da kanunfari ke yi a jikin dan adam (Karanta):
- Kanunfari na daya daga cikin abubuwan da muke amfani da su a matsayin sinadaren kamshi a cikin abinci ko abun sha.
- Ko kun san cewa alfanun sa ya wuce gaban haka?
- Kanunfari na dauke da dumbin sinadaran kara lafiya da magance cututtuka da dama.
kadan daga cikin magungunan da yake yi sun hada da:
1. Magance Ciwon Sikari A wani bincike da aka gudanar a shekarar 2006, an gano cewa kanunfari na taimakawa wajen rage yawan sikarin da ke cikin jini, a don haka yana matukar taimakawa masu ciwon sikari.
Yadda ake amfani da shi Za a iya zuba kimanin gram 10 na dakakken kanunfari a cikin ruwan dumi a sha shi da safe kafin a ci komai, ko kuma a barbada shi a cikin abinci.
2. Magance matsaloli da ciwukan baki Kanunfari da man shi na da tasiri akan kowane irin cuta ta baki, kama daga ciwukan hakori zuwa warin baki ko kumburin dasashi da sauran su.
Dalili kuwa shi ne ya na dauke da sinadaran da ke kashe kwayoyin cuta da kuma rage radadin ciwo. Yadda ake amfani da shi Ga mai ciwon hakuri, za a iya shafa man kanunfari ko kuma a tauna kanunfarin kan shi domin samun sauki cikin gaggawa. Idan kuma mutum ya na fama da warin baki ne, to zai tafasa kanunfarin a cikin ruwa, idan ya huce, za a na amfani da shi wajen kurkure baki bayan cin kowane abinci.
3. Magance ciwon gabobi Kanunfari na dauke da sinadaran da ke rage radadi da kuma kumburi, wannan ya sa ya ke da matukar tasiri ga masu ciwon gabobi Yadda ake amfani da shi Za a nade garin kanunfarin a cikin tsumma mai tsafta a dan dumama shi a wuta, sannan a dora shi a gurin da yake ciwon, ko kuma ana zuba man kanunfarin kadan a cikin ruwan wanka.
4. Magance ciwon makogwaro Kasancewar shi dauke da sinadaren da ke kashe kwayoyin cuta da rage radadi, kanunfari na da matukar tasiri akan ciwon makogwaro. Yadda ake amfani da shi Za zuba kanunfari guda gudan shi a zuma, a barshi na kamar tsahon awanni 8.
Bayan haka sai a sha zumar da kadan da kadan ta yadda zumar za ta na rufe cikin makogwaron da ke ciwo.
5. Magance matsalolin fata Kanunfari na tasiri akan matsalolin fata kamar su kuraje, dabbare dabbare, kumburi da sauransu.
Yadda ake amfani da shi Za a iya hada garin kanunfari da Zuma da lemon tsami ana shafawa a gurin da yake da matsalar.
0 Comments