Hanyoyin Kauce Wa Daukar Ciwon Sanyi (INFECTION):
Daga Bilkisu Tijjani
Da Yadda Uwargidan Za Ta Kare Kanta
Jima’i hanya ce da aka fi saurin daukar ciwon sanyi ga wanda yake da ciwon sanyin mace ko namiji, idan kai baka da ciwon in har ka yi jima’i da me ciwon sai ka/ki kamu, shi ya sa ake son a dinga gwaji kafin a yi aure ko karin aure ga maza masu auren mata sama da daya.
Maganin jima’i ga mai ciwon sanyi shi ne kuna gamawa dama kin tanadi tafasasshen ruwan zafinki da gishiri sai ki sa ruwan zafin a buta sannan ki zuba gishirin kadan, sai ki dan surka shi da ruwan sanyi kadan haka amma ya zama za ki iya sa hannun ki saboda kar zafin ya yi yawa ya kona ki.
Amma dai ya zama yana da dan zafi sai ki gasa gabanki da shi sosai, idan ya gasu ke da kanki za ki ji dadin jikinki idan kina yin haka ba za ki kamu da cutar ba. Shiga bandakin da yake da kazanta, ko kuma wanda kowa da kowa yake shiga, misali kamar gidan wanka na kasuwa (Public Toilet) shi ma yakan haifar da wannan cuta, ‘yan uwa sai a kiyaye wa.
0 Comments