DAUSAYIN RAMADAN (DARASI NA 17)


DAUSAYIN RAMADAN (DARASI NA 17)

7- Abin da ya halatta ga mai I’tikafi:
ya halatta ga mai I’itikafi ya tsaftace jikinsa. Ma'ana ya goge bakinsa da aswaki ko da man goge baki na bature. Sannan zai iya fita ya je ya yi wanka zai iya taje kansa, zai iya yin alwala, za a iya ɗaura masa aure, amma sai dai matar ba za ta tare ba, zai iya siye ko siyarwa, amma fa ba wai ya shiga harkar kasuwanci gadan-gadan kamar yadda yake yi a kasuwarsa ba, zai iya yin rakiya ga wanda ya kawo masa ziyara, amma kada rakiyar ta yi nisa. Haka nan matarsa za ta iya ziyartarsa, yana masallacin zai iya rakata har bakin harabar masallacin, kamar yadda Ummina Safiyya matar Ma’aiki ﷺ ta ziyarce shi lokacin da yake yin I’itikafi a masallaci. Kuma ba zai shiga gidansa ba, koda masallacin da yake yin I’itikafin a kusa da gidan yake, sai dai idan da wata larura ta Shari’a. Sannan zai iya ajiye kayan buƙatunsa a masallacin amma akula da tsaftace masallacin ta wajen share shi, da ƙamsasa shi. Abdullahi Ɗan Abbas ya ce, wanda ya shiga I’tikafi kuma sai ya sadu da matarsa to I’itikafinsa ya warware, sai ya sake sabuwar niyya. (108)
 8. Wajibi mai I’itikafi ya shagala da abubuwa guda uku: ➢ Ya kula da karatun Al-Ƙur’ani mai Girma, ya dage a kan karanta shi sosai.
 Babu laifi ma ya ɗauki wani adadi na sauka da zai yi kafin ya ƙare I’itikafin. Misali, kamar sauka ɗaya, ko biyu, ko uku, idan zai iya.
Amma sai dai kada ya ɗorawa kansa abin da ya san ba zai iya ba, ko kuma zai iya amma sai ya sha wahalar gaske, an fi so ya yi ibadarsa a cikin nishaɗi gwargwadon ikonsa. ➢
Ya shagala da yawan zikiri kamar hailala, tasbihi, takbiri, tahmidi, istigfari ko kuma salati ga Annabi ﷺ da sauran ayyukan ibada. ➢
 Ya mai da zuciyarsa zuwa ga Allah ﷻ, wato ya riƙa tunanin shi wane ne? Wane ne ya yi shi? Me ya sa ya yi shi? A ina yake? Me yake yi? Ina za shi? Kuma mai zai faru? Sannan ya riƙa tunani a kan mutuwa da abin da zai biyo bayanta na tambaya a cikin ƙabari, wanda Mala’iku za su yi masa cewa, wane ne Allanka? Wane ne Annabinka ﷺ? Mene ne addininka? Kuma ya riƙa tunanin ya zai tashi a gaban Allah ﷻ a ranar ƙiyama? Sannan ya riƙa tunanin ƙabari, kuncinsa, duhunsa, micizansa, kunamun cikinsa, zafin cikinsa, kaɗaitar kwanciya a cikinsa, firgicin tambayar cikinsa, daɗewar da za ai a cikinsa kafin ya fito daga cikinsa, da tsayuwa gaban Allah ﷻ da tsoron tambayar da zai yi masa da firgicin rashin sanin amsar da zai bayar, da daɗewar da zai yi a tsaye a gaban Allah ﷻ kafin a sallami kowa, da auna ayyukansa a kan sikelin nan mai adalci. Da firgicin rashin tabbacin a wane hannu zai karɓi takardun ayyukansa, a dama ne ko a hagu, da tsoron haɗuwa da waɗanda ya cuta ko ya ɗanne haƙƙinsu, ko waɗanda ya ha’inta, da firgicin hawa kan siraɗi, da tunanin yana daga cikin waɗanda za su iya tsallakewa lafiya, ko yana cikin waɗanda miyagun ayyukansu za su afka su cikin wuta, sannan da tunanin yana daga cikin waɗanda za a bari su sha tafkin Al-Kausara, ko yana cikin waɗanda za akora a hana su sha, da dai sauran makamantan waɗannan. Ya Allah ﷻ ka iya mana.
ZA mu ci gaba insha Allah.

Post a Comment

0 Comments