DAUSAYIN RAMADAN (DARASI NA 18.)


DAUSAYIN RAMADAN (DARASI NA 18.)

FA'IDOJIN SHIGA I'ITIKAFI.
Babbar fa'ida da mutum zai samu a shiga I'itikafi shi ne ƙarin kusanci zuwa ga Allah da ƙarin tsarin zuciya, da fifita lahira akan duniya, da tunanin makoma. 
1. Akwai tarbiyya da mutum zai samu ta hanyar tattara kansa da zuciyarsa zuwa ga Allah ﷻ baki ɗaya ya karkaɗe zuciyarsa ga barin hargowar duniya da ruɗinta da kawace-kawacenta.
 2. Musulmi zai iya ta ra hankalin sa wuri ɗaya domin ya dace da samun daren lailatil ƙadari. 3. Musulmi zai sabawa kansa haƙuri da zaman masallaci wanda zama ne mai albarka. 
4. Musulmi ya ciru daga wasu miyagun al’adu na cutarwa kamar zaman gulma, yi da mutane, annamimanci, yaɗa jita-jita da ɓata lokaci cikin abubuwan da ba su da amfani, kamar sauraron kaɗe-kaɗe da raye-raye, ka ga zaman I’itikafin ya hana shi faɗawa cikinsu.
 5. Mai zaman I’itikafi zai koyi wasu abubuwa masu amfani na samun nutsuwa da ƙarin yaƙini a zuciyarsa a tsakaninsa da mahaliccinsa, waɗanda za su sashi ya ƙara ayyukan ƙwarai ya guji munanan ayyuka.
 6. Ya san cewa, baya fita daga I’itikafi sai da wani dalili, kamar dai ya sa kansa ne a cikin wani kurkuku domin ya yiwa kansa wata tarbiyya ta musamman wacce za ta sa ya saba da zama domin ƙarin kusanci da Allah ﷻ. 
7. Mai zaman I’itikafi zai ƙudurce a zuciyarsa cewa, zaman ibada yake yi a masallacin, domin neman yardar Allah ﷻ da neman ƙarin kusanci da shi, sannan ya san wannan zaman wata jarrabawace da horo wacce ya koye ta yadda idan ya fito daga I’itikafin zai ci gaba da ita, domin ya riga ya sabada ita. 
8. Zai samu nutsuwa a cikin zuciyarsa da kwanciyar hankali. 
9. Mutum zai iya sauka mai yawa ta Al-Ƙur’ani. 10. Mutum zai iya tuba daga zunubbansa ƙanana da manya waɗanda ya san yana yi, ya kuma nemi gafarar Allah ﷻ a kansa don ya yafe masa. 
11. Mutum zai sabada tsayuwar dare wacce da take yi masa wuya, to yanzu za ta zame masa jiki saboda yawan sallah da zikiri da zai yi. 
12. Mutum zai raya lokutansa a kan bin Allah ﷻ. Waɗannan duka suna cikin irin amfanin da mutum zai sa mu idan ya shiga I’itikafi.

Post a Comment

0 Comments