DAUSAYIN RAMADAN (DARASI NA 15)


DAUSAYIN RAMADAN (DARASI NA 15)

Nan da kwanaki kaɗan za ka ji ana shirin shiga iitikafi, to duk abin da za ka yi ya kamata Kasan shi a ilmnace, domin ka yi yadda ake ake buƙatar sa a addini. 
Daga cikin manyan ibadu da aka fi yin su a cikin watan Ramadhan ita ce, ibadar I’itikafi, kamar yadda bayani zai zo nan gaba, da farko dai sai mu ce:
 1. Mene ne I’itikafi a harshen Larabci da kuma ma'anarsa a Shari'a? 
2. Mene ne hukuncin yin I’itikafi?
 3. Waye ya kamata ya shiga I’itikafi?
 4. Mene ne rukunnan I’itikafi? 
5. A ina ake yin I’itikafi? 
6. Mene ne manufar yin I’itikafi? 
7. Mene ne sharuɗɗann yin I’itikafi?
 8. A wane zamani ake yin I’itikafi? 
9. Mene ne yake ɓata I’itikafi? 
10. Wane amfani ake samu a cikin yin I’itikafi? 11. Abubuwan da suka halatta ga mai yin I’itikafi.
 12. Shin za a iya yin I’itikafi a wajen watan Ramadhan?
 13. Shin za a iya yin I’itikafi babu azumi?
 14. Wacce irin ibada mai yin I’itikafi zai mayar da hankali wajen yin ta? 
15. Mene ne ya halatta mai I’itikafi ya aikata? 16. Da yaushe ake shiga I’itikafi? 
17. Da yaushe ake fita daga I’itikafi?
  18. Mutum yana iya fasa I’itikafi bayan ya fara? 
19. Shiga I’itikafi da guzuri da sauran kayan buƙata.
1- Ma'anar I’itikafi: ma'anar I’itikafi a harshen Larabci shi ne zama wuri ɗaya, ko kuma lazimtar aikata wani abin kirki ko na banza. Amma ma'anar I’itikafi a Shari'an ce shi ne, mutum ya zauna a masallaci ko ya kawwame kansa a masallaci yana aikata wasu ayyukan ɗa'a, domin neman yardar Allah ﷻ ko neman ƙarin kusanci da Allah ﷻ maɗaukakin sarki. 
2- Hukuncin yin I’itikafi: shi dai I’itikafi tabbatacce ne a cikin Al-Ƙur'ani da sunnar Ma’aiki ﷺ da kuma ijma'in malamai. Hujjar yin sa a cikin Al-Ƙur'ani ita ce faɗin Allah ﷻ, inda yake cewa: ) Ma’ana: “Kada ku rungume su (mata) alhali kuna I’itikafi a masallatai.” Hujjar yin sa daga hadisi ita ce hadisin Ummina A’ishah inda take cewa, Manzon Allah ﷺ ya kasance yana yin I’itikafin kwana goman ƙarshe, na watan Ramadhan, haka ya ci gaba da yi har Allah ﷻ yakarɓi ransa. (104) Malaman musulunci gaba ɗaya sun tafi a kan Shari'ancin yin I’itikafi a watan Ramadhan.
 3- Matsayin I’itikafi: hikimar da ta sa aka Shar'anta yin I’itikafi ita ce, domin mutane su koma ga Allah ﷻ, saboda gafalar da suka yi a tsawon shekara da tarin zunubban da suka aikata a tsawon shekara, to sai ake so su kawwame kansu a wani muhimmin wuri mai ƙima da daraja a wajen Allah ﷻ wato masallaci, don hanyar yawaita zikiri da karatun Al-Ƙur'ani, yawaita sallar nafila, yawaita istigfari, salati ga Annabi ﷺ da yawaita tunanin makoma da kuma lissafin yadda rayuwa za ta kasance nan gaba. Daga cikin wasu malamai masana suna cewa hikimar I’itikafi shi ne ka yanke alaƙarka da kowa ka jingina kanka ga Allah ﷻ, wato ka duƙufa wajen neman ƙara kusanta kanka ga Allah ﷻ.
ZA mu ci gaba insha Allah.

Post a Comment

0 Comments