BACCI AKAN CIKI]] ((kwanchuyar Rub da Ciki))


[[BACCI AKAN CIKI]] ((kwanchuyar Rub da Ciki))

Mutane da dama suna wannan kwanciya ta Rub da Ciki, Wanda mafi yawa suka mai dashi a matsayin kwanciyar da tafi musu dadi ba tare da sun san cewa kwanciya ce wacce ALLAH baya so ba Kuma Annabi (ﷺ) yayi hani akan hakan ba, wasu daga ciki Kuma sun san cewa ba kyau Amma saboda son zuciya sai kaga suna yin irin wannan kwanciyar ba tare da sun damu ba wasu kuma naganin kawai chemfi ne ba Hani bane daga addini (ma’ana maganganun mutane) ne kawai.

Toh a hakikannin gaskiya babu maganar chamfi, An samo Hadisi ingantacce na hanin daga Manzon ALLAH (ﷺ) akan ita wannan kwanciya ta Rub da Ciki:
.
Annabi (ﷺ) Yace: “Ita dai kwanciya (Rub da Ciki) kwanciya ce ta ‘Yan-wuta, Kuma kwanciya ce da ALLAH yake fushi da ita.” [ sahih Abu dawud ]
.
Hakanan Hadisi ya inganta cikin sunani Abu dawud da Tirmizhi daga Ya'ish Bn ɗuhfatul Gifari (RA) daga babansa cewa: wata rana Annabi ( ﷺ ) yazo wucewa ya same ni a masallaci ina kwance (rub da ciki) sai ya zungureni da ƙafarsa yace kadai na irin wannan kwanciyar saboda kwanciya ce da ALLAH yake fushi da ita.”
.
Hakanan masana bincike sun gano cewa (Rub da Ciki) wajen bacci Yana da matuqar illa ga qashin baya har ma idan an dade ana irin wannan kwanciya akan ciki Yana jawo babbar matsala har ta kai ga lahanta a qasusuwan bayan Dan-Adam, hakanan bincike ya nuna cewa nauyin mutum Yana tsakanin wuyansa ne don haka kwanciya akan ciki na iya jawo jijiyoyi su matsu haka Kuma zai yi wahala gadon bayan mutum ya mike daidai idan ya kwanta ta haka wajen bacci. Wannan ke Kara tabbatar mana da cewa lallai dukkan abunda Musulunci yazo mana dashi na umurni ko hani to lallai akwai fa’ida acikin sa.
.
Saboda haka idan mutum yasan Yana irin wannan kwanciya to yayi qoqari ya daina, Iyaye su ringa Sanya Ido a irin kwanciyar da yaransu suke yi su gyara musu Kuma su daura su akan turba na gaskiya.
.
ALLAAH Yasa mu dace yarabamu da qunchin rayuwa da bashi da gwauranchi AMEEEN..

Post a Comment

0 Comments