DALĨLAN DA KE SABBABA JINKIRIN AURE


DALĨLAN DA KE SABBABA JINKIRIN AURE
══════ ❁✿❁ ═══════
(1) SHARRIN-ALJANU.
Yana daga Sharrin Aljanu Mazansu Ko Mãtansu, Idan Suna Son Mutum Sukan hana Shi Yin Aure, Ko da Sun barshi yana Soyayya Amma da Zãran Amfãra Maganar Aure Sai Maganar ta Lãlãce.
══════ ❁✿❁ ═══════
(2) TALAUCI.
Talauci Yana daga Cikin Abin da Yake Dãkatar da Mafi Yawan Samari da 'Yan-Mãta Sãmun Dãmar yin Aure da Wuri, Wata Tana Matuqar Son Aure , Amma Mahaifinta bai da Hãlin da Zai Iya Aurar da Ita, Haka Wani Saurayin yana Son Aure Amma Talauci ya Tãka Mai Burki.
══════ ❁✿❁ ═══════
(3) RA'AYI.
Ra'ayi Shi ma yana Sabbaba Jinkirin Aure, Ni Sai Mai Kuɗi, Ko Sai na Gama Karãtu, Ko Sai na Sãmu Jali Mai Qarfi, Ko Sai Na Samu Kalar da ta dãce dani, Ko, Ko, Ko, Ko,....etc
══════ ❁✿❁ ═══════
(4) TASĨRIN YAUDARA.
Wani Ko Wata, Idan Suka Aminta da Wanda Suke So, Daga Bisãni Sai Yaudara ta Shiga Tsakãni, Daga Nan fa Sai Su Tsani Soyayya da Maganar Aure Su Koma Karãtu. Ko Kuma Wata Harkar, Har Sai Sun dena Jin Zãfin Raiɗaɗin Cin Amãnarsu da Aka yi.
══════ ❁✿❁ ═══════
(5) RASHIN LAFIYA.
Wannan Ya Shãfi ɓangaren Sha'awa, da Rashin Lãfiyar Jiki, Domin Zãka ga Wasu da Hãlin Yin Auren Amma Kuma Sam Basa ma Son A Musu Maganar Aure.
══════ ❁✿❁ ═══════
(6) BIYE WA AL'ÃDA.
Sai Anyi Akwati Set Kaza, Sai Anbiya Sadãki Naira Kaza, Sai, Sai, Sai, Sai,...etc
══════ ❁✿❁ ═══════
(7) SÃBON ALLAH (S,W,T)
Yana Sabbaba Jinkirin Aure Fiye da Zatonku, Kai yakan Haramta wa Mutum Sãmun Dãmar Yin Auren Ma. Dõmin Aure Rahama ne, Rahamar Allah Kuma Ba'a Sãmunta ta Hanyar Sãɓa Masa.
══════ ❁✿❁ ═══════
(8) QADDARA.
Wasu duk yadda Suka Kai ga Son yin Aure, Idan Lokacin da Allah ya Qaddara Musu bayyi ba, Sai Kaga Sun daɗe Basu yi Auren ba.
══════ ❁✿❁ ═══════
Duk Wanda Yake da Wata Lalũra Ko Wata Matsala Acikin Abin da na Lissafa, Yã Allah Ka Taimake Shi Gurin Warware Matsalar Shi.
NA BARKU LAFIYA.

Post a Comment

0 Comments