Don kare kanka daga cututtukan Ƙoda yana da kyau kasan waɗannan hanyoyi:
🫁🫁🫁🫁🫁🫁🫁🫁🫁🫁🫁🫁🫁🫁🫁
1. Ka riƙa shan ruwa sosai.💧
2. Rage yawan shan gishiri.
3. Idan kaji fitsari kayi shi ba ɓata lokaci.
4. Daina shan magani ba bisa ka'ida ba. Kada kuma ka riƙa shan magungunan gargajiya ba tsari.
5 Ka rage ƙunatar maiƙo 'musamman' in kana da ƙiba.
6. Kada kasha giya, sigari ko shisha
7. Kar ayi amfani da Allurar Haska fata(bleaching) irinsu Glutathione.
8. Ka riƙa motsa jiki.
9 Ayi ƙoƙarin shan magani idan akwai infection
-Akwai nau'in cututtukan ƙoda kala-kala amma abubuwan da muka faɗa a sama zasu taimaka wajen kariya daga mafi yawansu.
Idan anga fitsari da jini, ko rashin fitsarin ko kumburi da zafi a kuiɓin ciki daga ƙasa-kasa da zazzaɓi, aje asibiti da sauri.
Allah bamu Lafiya🙏
0 Comments