Wata amarya yayin biki


Wata amarya yayin biki (tsohuwar ajiya)

Amina Abdullahi

Ranar biki babbar rana ce a rayuwar kowace mace kuma a wannan ranar kowa yana son ya ga irin kwalliyar da za ta yi.

Ko ’yan gidan su amaryar suna son kare mata kallo a wannan rana. Wadansu amaren tsabagen son gyaran jiki har gyaran ya yi yawa ya feso muso da kuraje a fuska duk da a da ba su da kurajen.




Don haka ne a yau muka kawo muku yadda amaryar gobe za ta kintsa kanta kafin ranar biki.

 • Amaryar gobe ta kasance tana yawan shan ruwa. Sirrin hakan shi ne kada jikin ya yankwane.

Kuma yana da kyau ta rika shan kankana sosai da cin su latas da ’ya’yan itatuwa domin gyaran fatar jikinta.

Ana so amaryar gobe ta fara wannan shirin tun ana bikinta saura wata uku. Ta san irin man da za ta shafa da irin abincin da za ta rika ci.

Idan amaryar gobe ta wuce shekara 20 yana da kyau ta rika kwaba fiya da zuma tana shafawa a fuskarta domin warkar da kananan kurajen fuska kafin ranar biki.
Idan shekarunta sun wuce 25, yana da kyau ta rika yin dilke domin cire dattin fuska kuma hakan na rage mata shekaru a fuskarta.

Yana da kyau ta sayi magungunan Turawa na gyaran jiki (supplement) wadannan magunguna suna dauke da sinadaran bitamin A da E da kuma na omega3 wanda aka fi samu a man kifi. Wadann magungunan suna sanya fata sulbi da laushi.

A samu man shafawa mai kyau tsayayye wanda za a rika shafawa a tsawon wannan lokaci. A rika shafa wannan man akalla sau biyu a rana.

Yana da kyau amaryar gobe ta samu lokacin yin barci sosai kuma ta rage shiga rana domin gyaran fata da kuma hutu.

Ta rika amfani da soson hoda mai tsafta ba mai dauda ba, domin rage haifar da wasu kurajen fuskar.

Domin samun fata mai haske a samu Kurkum da ruwan lemon tsami da man zaitun kamar rabin karamin cokali da madara ta shafa a fuskarta na tsawon rabin awa sannan ta wanke. A kullum ta rika yin hakan safe da yamma. Lallai za a ga canji.

Post a Comment

0 Comments