Sako Ga Duk Wata Mace Mai Aure:
#tsangayarnalamtonga
SHARE 🔔
Idan har kinada aure, kina zaune da mijinki. Ga wani sako ne na tunatarwa da zai taimaki zaman aurenki.
1: Kada ki daga muryarki sama dana mijinki a lokacinda kuka samu matsala.
2: Kada ki yadawa duniya wani illa ko nakasu da mijinki yake dashi.
3:Kada ki rika kwatanta mijinki da wasu mazan a hali, dabi'a da wadata.
4: Kada ki musgunawa na kusa da mijinki saboda baki shiri dasu.
5: Kada ki gaza wajen sauke hakkokin mijinki dake kanki.
6: Kada ki sakarwa 'yar aiki, kanwarki ko kawarki aiyukan dasuka dace ki yiwa mijinki da kanki koda bashi ruwan sha ne.
7: Kada ki sauyawa mijinki fuska saboda ya shigo gida bada bakar leda ba.
8:Kada ki zama mai almubazaranci a gidan mijinki.
9: Kada ki bari wasu su fahimci kinada matsala da mijinki.
10: Kada ki bari kawayenki su kusanci mijinki kut da kut.
11: Kada ki takaitawa mijinki lokacinki.
12: Kada ki hana mijinki gabanki saboda kina fushi dashi.
Da fatan wannan tunatarwar zai yi muku amfani.
0 Comments