Duk Irin Bacin Ranki Kada Ki Furtawa Mijinki Wadannan Kalaman:


Duk Irin Bacin Ranki Kada Ki Furtawa Mijinki Wadannan Kalaman:

SHARE 🔔
#Tsangayarmalamtonga 

Ba duk mace ke iya furta kalamai na hankali ba a lokacinda ranta yake bace.

 Hakan ma yasa sau tari kalamansu alokutan hasala suke jawo musu dasun sani.

Duk irin yadda ranki ya baci kada ki kuskura ki furtawa mijinki wadannan kalaman kamar haka:

 
1: Laifinka Ne: Koda mijinki ne da laifi kada kai tsaye ki furta masa wannan kalmar. Maimakon wannan kalmar kina iya cewa laifinmu ne shi yasa baki ciki.

2: Rabudani: Kalma ce da mata suke yawan furtawa musamman idan ransu ya baci ake kokarin tausarsu. 
Kalmace ta cin zarafin miji ga macen dake fadin hakan. Duk yadda ranki ya baci idan miji ya zo rarrashinki kada ki fizge kice ya rabu dake, ko kuma idan yana so ya miki bayani.

3:Zagi: Akwai mata masu amfani da kalmomi irinsu "mugu kawai, azzakumi, mayaudari ko makaryaci" ga mazajensu. Kalamai ne masu tsauri dauke da rashin mutunci ga duk macen da zata furtawa miji su komai zafin abunda ya mata.

4: Tsakanina Dakai Allah Ya Isa: Kalmace mai sauki amma dauke take da cin mutunci.
Maimakon furtawa miji wannan kalmar kina iya amfani da "Allah Ya biwa kowa hakkinsa idan ni na zakunceka." Ko Kice " Allah na biwa wanda aka zakunta hakkinsa".

 
5: Karya Kake: Shima yana da saukin fadi wajen mata wasu ba basai ransu ya baci ba.
Bama mijinki ba, ko danda kika haifa ne babu dacewa ki karyatashi kai tsaye.
Maimakon wannan kalmar yi amfani da ba haka abun yake ba. Ko baka fahimci lamarin ba.

6: Bazan Sake Yarda Da Kai Ba: Nunawa miji rashin yarda bayan wani matsala ya gifto kece zaki cutar da kanki ganin zuciyarki zata kasa natsuwa da shi.

Maimakon furta masa hakan gara kiyi shuru domin sake bashi wata damar nan gaba kila zai gyara. Amma kina nuna masa daga yanzu babu yarda tsakaninku zaki kara bashi damar ci gaba da wannan abunda ya jawo muku matsala. 

7:Banga Haka A Gidanmu Ba: Wannan zagin iyayen mijinki ne kai tsaye, ki guji furta wannan kalmar ga mijinki a lokacin bacin rai.

Kada ki sake ki kawo zancen gidanku ko na mijinki ko iyayenku a cikin matsalarku wanda babu hakan a masomin matsalarku. 

8: Da Wane Na Aura: Shigo da zancen tsohon saurayinki ko mijinki da kuka rabu ko ya mutu a sabaninki da mijinki wauta ce. Kada ki kuskura ki ambacesu koda sun fishi dadin zama, hakan cin fuska ne da ko bayan kun shirya abun ba zai wuce a ransa ba.

9: Kai Ka Sani: Ita ma kalmace mara dadi da mata suke wurgawa mazansu ita a lokacin bacin rai.
Kalmar babu girmamawa a cikinta kuka gata da kaskantar da mutum wajen wofintar dashi.

10: Ka Sake Ni: Akasarin matan da suke neman saki idan ransu ya baci sune kuma suke neman komai idanuwan su a bude idan sun huce.

Shi saki ba nemansa ake yi da dole ba. Zuwa yake idan lokacinsa yayi ko ana son zama ko ba a so. Don haka kada ki kuskura ki furtawa mijinki kalmar ya sakeki saboda kawai ranki Yana bace. 

 
Wadannan kalmomin ne da suke matukar tasiri a zuciyan wanda aka furtawa su koda kuwa bayan komai ya lafa ne. Don haka mata ku kiyayesu.

Post a Comment

0 Comments