Wasu Dabi'un Mata Da Baka Iya Rabasu Dasu:


Wasu Dabi'un Mata Da Baka Iya Rabasu Dasu:

SHARE 🔔
#tsangayarnalamtonga 

Mace ba kamar namiji take ba, a halitta, dabi'a da tunani. Hakan yasa duk wani mutum da zai yi mu'amala da mace dole ne ya fahimci cewa bafa yadda yake son ganin lamarin haka zai kasance ba saboda su mata sunada yadda suke aiwatar da abubuwansu da kuma yadda suke kallonsu.

Ga wasu dabi'u na mata duk iya yinka ba zaka iya rabasu dasu ba:

 
1: Yanga: Ita mace tun tana karamarta da yanga, yauki, iyayi take tasowa.

Mata sukanyi amfani da yanga ne a matsayin dabi'a na jawo hankalin mai sonsu idan sun cika mata ko domin burge mai kallon su idan suna kanana.
Yanga ga 'ya mace dole ba babu yadda zaka iya rabata da shi ko mai zafinka.

2: Son Kyalekyele: Mace na iya cire kudi masu yawa ta sayi rigan nonuwa da kamfe masu tsada da ba kowa zai gansu ba saboda kawai ta burge kanta.

Mace bata cika mace sai taga ta zubawa yatsunta da wuyanta gwalgwalai. Mace burinta tayi shigar da duk taron mata babu wacce ta kaita tsadan kayan data saka.
 Hakan yasa duk iya yin mutu bazai iya raba mata da son kayan Kyalekyele na jikinsu dana ado a gidajensu ba.

3: Duk wata macen duniya tanason idan tayi kwalliya komai muninsa ka kalleta kace mata tayi kyau. Bama cikenkiyar mace ba. Koda karamar yarinyace ka gwada zakaga yadda zata nuna maka farin cikinta da zaran kace mata tayi kyau. Haka kuma duk tsufanta wannan kalmar na tayi kyau bayan kwalliya yana sata taji ta dawo 'yar 18. Don haka wannan kalmar baka iya raba mace da bukatar shi.

4: Buki: Ba komai yasa mata suke da yawan yin gori saboda yadda suke da dabi'a na son buki.

Duk wata mace takanso taje bukin da aka gayyaceta domin idan nata yazo ita ma a zo mata.

Mata sona son idan suka je buki suka kashewa mai bukin naira 100 suna saran idan nasu ya taso a kashe musu 1000.
Wannan na inada buki na dabi'an mata baka iya rabasu da ita.

 
5: Sumbata: Akasarin mata suna son a sumbacesu koda a kumatu ne, duk da ba duk bane zasu iya fitowa su nuna hakan ko su furta hakan. Amma wani dabi'a ne nasu da ba a iya rabasu da shi.

Mace bata sonka, amma tana iya barinka ka yi mata wasa da nonuwanta, amma da wuya macen da bata son namiji ta bari ya sumbaceta. Duk macen data amincewa namiji sumbata na tsotsan harshe da musayan yawu, babu tantama akwai kauna da hakika a tare da ita naka koda kuwa karuwace..

6: A Dinta Hakan Yake: Duk da ana samun mata makaryata da yaudara, akasarin mata A dinsu hakan yake musamman a bangaren soyayya.

Mace idan har tace maka A kuma bada gaske take ba, idan kana da hankali zaka gane. Soboda akwai wasu abubuwan da bazata rika maka su ba idan tana sonka, kamar yadda zata rika maka wasu abubuwan na alamun bata sonka.

Wannan dabi'ar na tabbatar wa namiji suna sonshi dabi'a ce da baka iya raba mace da shi.

7: Kwalliya: Akasarin mata sunfi baiwa kwalliyar da zasu fita unguwa mahimmanci fiye da kwalliyar da zasu yiwa miji idan masu aure ne. Haka suma yan mata sai sun tabbatar sun kure adaka kamin su fita unguwa ko fitowa wajen saurayi.

Mace yanada matukar wahala musamman budurwa ta bari namiji ya ganta a zahirinta na babu kwalliya. Shi yasa wasu matan ko daga bacci suka tashi kayan kwalliya na gefensu.

8: Sun Bada Umurni: Akasarin mata sunfi so a bi umurninsu. Shi yasa mata suke son namijin da bai ja yayye dasu.

Mace tanaso idan tace ga yadda za a yi to kawai ayi. Hakan na sa taga cewa ta isa da wanda take baiwa umurnin.

9: Rada: Akasarin mata suna son yin rada, duk da yake akwai su da son yin gulma, amma shi rada a gabanka ma sai kaga guda ta kawo kunnuwanta guda ta tsaigunta mata labari.

Baka Iya raba mata da wannan dabi'a na radda, hadi kuma da gulma.

10: Kishi: Wannan shine babban halin mata da aka fi saninsu da shi. Kashi 90 na mata cikin 100 sunada kishi, wannan yasa wasu suke samun matsala a rayuwarsu.

 
Da fatan maza zamu fahimci wadannan halayen na mata domin sanin yadda zamu zauna dasu cikin lumana.

Post a Comment

0 Comments