Man kwakwa yana sa kaifin ƙwaƙwalwa da hana fata yamushewa.
~bbchausa.com
Man kwakwa yana ci gaba da yin tasiri sosai a shekarun baya-bayan nan faɗin duniya.
Man kwakwa yana da amfani a fannoni daban-daban, daga ciki akwai; amfani a gashin kai, man shafawa a jiki, har ma wajen yin girki da turaren jiki da sauransu.
Akwai man kwakwa daban-daban, cikin manyan mayukan da aka fi sani su ne, copra oil and virgin coconut oil.
Man kwa-kwa na da abubuwan gina jiki da dama da zai iya taimaka wa lafiyar jikin dan Adam, yana tattare da sinadari masu muhimmanci ga jiki.
Amfanin man kwakwa ga lafiyar dan Adam:
Man kwakwa na da sinadirai da za su iya taimaka wa wajen magance matsalolin lafiya daban-daban, kamar gyara gashi da hana lalacewar fata da buɗe ƙwaƙwalwa da taimakawa wajen bai wa jiki kuzari.
Ga dai wasu ƙarin bayani game da amfanin man kwakwa ga lafiya kamar yadda Mujallar Lafiya ta WebMd a Amurka:
Lauric acid is a type of saturated fat found in coconut oil, and in fact, this oil contains the highest levels of lauric acid in a natural source.
Lauric acid wani nau'in kitse ne da ake samu a cikin man kwakwa, kuma a takaice, man kwakwa yana ƙunshe da lauric acid mai yawa a cikinsa.
Bincike ya nuna cewa lauric acid yana tafiya zuwa hanta kuma yana canzawa zuwa kuzari maimakon a adana shi a cikin jikinku a matsayin kitse, wanda zai iya taimaka wa wajen rage ƙiba.
Sai dai duk da haka ana buƙatar ƙarin bayani don tabbatar da cewa man kwakwa yana ba da gudummawa musamman ga rage ƙiba da haɓaka zagayewar sinadirai a jiki ko ba da kuzari.
Inganta lafiyar fatar jiki da gashi
Mutane da dama na amfani da man kwakwa a cikin kayan kwalliyar su, domin gyara gashinsu da faratansu da fatarsu da kuma haƙoransu.
An gano cewa man ba shi da illa kuma yana da inganci wajen sanya fata taushi da magance wasu matsalolin fara da kuma hana fata bushewa.
Bugu da ƙari, man kwakwa na iya rage asarar sinadarin furotin a gashi, zai kuma iya inganta lafiyar gashin.
Man kwakwar na da dandado mai sha'awa wanda zai iya kara wa abinci dadi tare da kara wa abincin sinadirai masu gina jiki.
Ba kowane kitse ba ne yake da illa. An gano cewa man kwakwa na inganta kitse mai kyau da yake jikin wasu matan tare da rage kaifin kitse mara kyau da ke jikinsu.
Hadarin man kwakwa
Kwakwa
Man kwakwa yana da muhimmanci sosai kamar yadda aka fada tun farko, musamman wajen sanya fata taushi.
Amma duk da haka akwai wasu hadurra nasa ga lafiya kamar irin yawan kitsen da ke ƙunshe a cikinsa.
Ga dai wasu haɗarin lafiyar lafiyar ɗanyen kwakwa:
Haɗarin Kamuwa da Ciwon Zuciya ko Bugun jini
Ko da yake wasu bincike sun nuna cewa man kwakwa na iya ƙara yawan cholesterol mai kyau da kuma rage mara kyau, wasu bincike sun nuna cewa idan aka kwatanta da sauran mayuka kamar man zaitun, man kwakwa yana ƙara yawan sinadarin LDL cholesterol mai cutarwa.
Yawan sinadarin LDL cholesterol na iya haɓaka haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya ko fama da bugawar zuciya.
Ƙungiyar Kula da Ciwukan Zuciya ta Amurka ta ba da shawarar cewa kar ka ci kitsen da bai wuce giram 13 ba a abincinku.
Kamar yadda aka fada a baya, man kwakwa ya ƙunshi fiye da haka (giram 14) a cikin abinci guda ɗaya, ma'ana abu ne mai sauƙi a wuce gona da iri wurin cin kitse a cikin abinci idan aka dafa shi da man kwakwa.
Cin kitse mai yawa a abinci ka iya ƙara haɗarin kamuwa da ciwon zuciya da mutuwar ɓarin jiki.
0 Comments