Ilimin yadda ake yin Jima'i kashi na daya.





Ilimin yadda ake yin Jima'i kashi na daya.




Yar uwa ya na daga ilimin da ya kamata a dinga sanar da mutanen da su ka mallaki hankalin kansu shi ne ilimin jima’i a Musulunci.



Manzon Allah (saw) ya ce, kada dayanku ya afka wa matarsa, kamar yadda jaki ya ke afkawa jaka.


Idan dayanku zai je wa iyalinsa, ya kamata ya aika dan aike, wato ya kamata a ce kafin ya kwanta da matarsa su gabatar da duk wani wasa da zai motsa musu sha’awa, domin samun gamsuwar su kansu ma’auratan.



Sannan idan mutum ya sadu da matarsa, bai kamata ya yi gaggawar fitar da gabansa daga cikin matucinta ba har sai wannan matar ta sami gamsuwa daga gare shi, saboda wata matar ba ta samun gamsuwa a daidai lokacin da shi mijin ya sami gansuwa, har sai ya jira ita ma matar ta sami tata gamsuwar.


Wani mutumin ba ruwansa; da zarar ya sami gamsuwa da matarsa koda a iya wasan da su ke yi ne, to fa shi ya gama, ba ruwansa da ita. Shi ba abinsa ya yi ma sa zafi. Kun ga wannan shi ne karshen rashin adalci.

Wata matar kuma ta na da doguwar sha’awa, saboda haka, idan mijinta bai yi wasa da ita ba, sannnn bai jira ta samu gamsuwa daga gare shi ba, to maniyyin da ya ke jikinta ba zai sauko ya hadu da nasa ba, sai dai ya tsaya ma ta a mararta. Daga nan kuma sai ciwon mara, sai ciwon ciki, sai ciwon kai, sai warin gaba.


Mu hadu a kashi na biyu.


Post a Comment

0 Comments