Wasu Kurakuren Da Maza Suke Tafkawa A Lokacin Buga Soyayya:


Wasu Kurakuren Da Maza Suke Tafkawa A Lokacin Buga Soyayya:

#Tsangayarmalamtonga 

Wasu mazan suna batawa da matan da suke soyayyar aure dasu ne saboda wasu Kurakuren da suke tafkawa da kansu.

Soyaya kaman ko wani irin abu na rayuwa, muddin za a gudanar dashi ba bisa ka'ida ba, akwai yiwuwan samun matsala a gaba.
Ga wasu Kurakuren da samari ko maza suke yi a lokacin gudanar da soyayyar neman aure.

 
Rashin Sadarwa:

Wannan yana daya daga cikin babban matsalar da masoya suke fuskanta har ya kaisu ga rabuwa.

Haka nan koda aure aka yi da wannan matsalar na rashin sadarwan zai iya kashen auren.

Wasu mazan suna biyewa wacce suke soyayya da ita wani abu dake damunsa game da ita. Ko wasu maganganun da sukaji game da ita.

A soyayya na gaskiya kada masoya su boyewa junansu wani abunda sukasan zai iya zamemusu matsala a harkar soyayyar da suke masa fatan aure.

Tattaunawa na fahimta shine abunda ya kamata masoya su rika yi amma ba yin shuru ba a tafi a hakan. Duk namijin da yake son mace tsakaninsa da Allah, kada yaji nauyi, shakka ko kunyar magana akan dukkanin wani abunda yake neman sani ko yake so ta gyara.

Bata Lokaci:

Babu wata mace a duniyan nan da masonta bazai yi galaba akanta ba muddin yana bata lokaci. Haka nan cikin sauki ana iya rabaka da wacce kake so muddin bakada lokacinta.

Ita mace yawan mu'amalar da kake yi da ita a kullum gwargwadon kara shiga ranta da kake yi kenan. Don haka dole ne idan kana son ganin ka cimma burinka na auren macen da kake nema da aure dole ne ka bata lokaci.

Abubuwan Datake So:

Bai kamata ace kana neman auren mace har kuna buga soyayya da ita, amma ka kasa sanin ko fahimtar abubuwan datake son ayi mata a rayuwa da kuma wadanda take tsana ba.

Kuskure ne babba muddin zaka yi soyayya aure amma baka iya fahimtar abubuwan da take so ko take kinsu ba. 

A haka ne zaka yi ta mata Kyauta da abubuwan da bata so bata nuna farin cikinta kuma taki nuna maka murnar ta.
Yana da kyau ka gano abunda wacce kake soyaya da ita take so da abubuwan da bata so domin inganta soyayyar ku.

Rashin Yaba Mata:

Kuskure ne a wajen mata ga namijin da bai yabonsu.

Ka kasance mai yawan yabon budurwarka ta aure a duk lokacinda tayi abun yabo.
Ka nuna mata jin dadinka, farin cikinka da wannan abun.

Kada ka zama irin mazan nan da suke daukar duk abunda mace ta musu na kyautatawa tamkar dole ne sai tayi hakan daman.

Nuna Mata Akwai Abunda Ya Fita:

Wani kuskuren kuma da wasu mazan suke yi shine na nunawa wacce suke so da aure da akwai abunda ya fiye musu ita.

Babu shakka ba za a rasa ba. Amma fitowa ka fadawa budurwa cewa kana da abunda yafita mahimmanci cin fuska ne, kuma wannan zai iya jawo muku matsala.

Su mata tsabar son suga sune suka fi kowa mahimmanci a wajen mai sonsu da zaka ce mata mahimmancinta yafi na wacce ta haifeka dadi zata ji. To ina kuma ka nuna mata abunda bai kai wannan ba ya fita daraja a wurinka.

Post a Comment

0 Comments