Wasu Mahimman Abubuwa Da Yakamata Budurwa Ta Sansu Kamin Tayi Aure:
SHARE 🔔
#tsangayarnalamtonga
Yan mata da dama suna kosawa da aurene jim kadan bayan yin aure da wasu shekaru saboda rashin fahimtar zaman aure yana da bambamcin zaman budurci.
Wannan rashin sanin yasa yan mata da dama dasunyi aure sunga sabuwar rayuwar da basu saba da ita sai kawai su kosa da zaman auren.
Ga wasu Mahimman abubuwan da ya kamata duk wata budurwa ta sansu kamin tayi aure.
1: Soyayyar Kamin Aure Daban Yake Dana Bayan Aure: 'Yan mata da dama suna dauka yadda namiji yake rawan jiki dasu hakan nan zai ci gaba dayi ko bayan aurensu. Da zaran ta bukaci wani abun babu bata lokaci ake mata amma bayan auren hakan bazai samu.
Yana da kyau kisani abubuwan da yake miki a yanzu na hidima da kula ba zai iya ci gaba da yi miki kamar kamin kuyi aure ba.
Da farko dai yanzu dashi kike kwana dashi kike tashi zumudinki ya ragu, zamanda kuke yi a yanzu babu ranar rabuwa don haka dole ya rage miki hidima. A baya kuwa ba kullum kuke haduwa ba cikin sauki zai iya tanadin abunda kike bukata kamin yazo.
2: Rashin Damar Yin Komai: Yana da kyau kamin kiyi aure ki fahimci cewa, idan fa kikayi aure yin son ranki yadda kike so a lokacinda kike so ya kau.
Daga lokacinda kikayi aure kinada takaitancen 'yanci ko ra'ayin da zakiyi gaban kanki irin yadda kike yi a baya kamin kiyi auren.
Don haka duk wata budurwa ta fahimci cewa yadda take saba gyale ta yi gabas sai lokacinda ta dawo ga irin yan matan nan da basu da mafadi, to a auren hakan bazai yiwu ba.
3: Dogara Da Miji: kamin kiyi aure kina dogara ne da iyayenki, 'yan uwanki ko samarin da suke sonki. Daga lokacinda kika yi aure wannan ya kau ya dawo kan mijinki.
Duk wasu bukatunki baki da damar nema a wajen wani sai mijinki. Ya dace kisan da hakan.
4: Ladabi Dole: Baki da zabi irin kamin kiyi aure sai kinyi ra'ayi kamin ki yiwa saurayinki ladabi. Amma a zaman aure ya kamata ki fahimci yiwa miji ladabi ya zama dole.
Dole ki iya amsa kira, idan mijinki ya kiraki. Dole ne ki koyi yadda ake mikawa miji abu da yadda ake karba daga hannunsa.
Gaisuwar safe daban, na rana daban haka ma na dare. Fatan Alheri idan zai fita nema dole ki iya. Idan yace miki baida shi yana da kyau kisan irin amsar da zaki bashi.
Wadannan abubuwan duk ba dolenki bane kamin kiyi aure, amna daga lokacinda aka shafa dole ne kiyi ko ki iya.
5: Hakkin Iyayenki Na Kanki: Kamar yadda hakkin iyayenki yake kanki kamin aure, haka ma bayan aure. Wasu matan suna sakaci da damuwa da iyayensu bayan da sukayi aure, hakan babban kuskure ne.
Duk irin wanda kike aure komai matsayinsa dole ne ki kula da bukatun iyayenki wannan dole ne. Wasu na daukar cewa miji yafi uba ba gaskiya bane. Iyaye har mace ta koma ga mahalincinta wajibi ne ta kula da bukatunsu da yi musu ladabi.
Don haka ki sani babu namijin da zaki aura ki mance da iyayenki.
6: Duk Nasa Naki Ne: Idan a baya baki shiri da wasu abokansa ko 'yan uwansa, daga ranar da aka daura muku aure daga wannan lokacin kowa nasa ya zama naki.
Dole ne ki koyi zama da kowa lafiya koda kuwa makota ne ba nakusa da miji bane. Bakida zabin nunawa wasu so wasu kuwa kiyayya.
7: Sanin Girki: Idan ma a baya baki damu da shiga kicin ba, ki sani idan kikayi aure dole ne yiwa miji girki. Bama girkin kawai ba, irin wanda shi yake so yaci dole ne ki koyi irinsa tun ma kamin ki shiga gidansa.
Don haka ki sani dole ne ki ajiye kiwa ko rashin iya girki a gefe domin muddin kikayi aure sai kinyiwa miji girki.
8: Haihuwa: Babu makawa idan kikayi aure kina iya samun ciki, kuma dole ki haihu, don haka ki fahimci aihuwa a aure dole ne ba zabi bane idan ke baki son haihuwan shi mijin naki yana so. Duk da yake kamin auren kuna iya fahimtar juna, amma mazan da suke aure domin samun haihuwa sunfi yawa. Don haka ki sa a ranki dole ne ki haihu.
9: Babu Boye Boye: Duk da yake mace nada 'yancin yin sirri ko tana da aure, amma a zaman aure ba gaskiya ma'aurata basa boyewa junansu komai nasu.
Idan a baya kina da hali irin na nuku nuku, to ki sani bayan aurenki dole ne ki zama mai budeddiyar ciki da bazaki boyewa mijinki wasu abubuwan da kike niya yin ba ko kuma kike yi.
Hakan yana zama dole ne saboda halin yau da gobe. Akwai mutuwa, kina iya samun matsalar da zaki so ya shiga maganar, don haka fitowa ki bayyanawa mijinki gaskiya ba tare da boye boye ba shine zai taimaka miki wajen zaman aure na gari.
10: Jima'i: Ki sani idan kinyi aure mijinki yana da hakkin saduwa dake a duk lokacin da bukatar hakan ya taso haka kema kina iya bukatarsa a duk lokacinda kike da bukata.
Kamin aure kin ki yarda ya tabamiki ko hannuwarki, amma yanzu ki sani duk ilahirin jikinki nasa ne, zai saffarashi yadda kike so ko yadda yake so.
Wadannan abubuwan sunada matukar mahimmanci duk wata budurwa ta fahimcesu ta kuma yi shirin tinkaransu.
0 Comments