Da Zaran Matsala Ta kunno Kai A Zamantakewar Aurenku Ko Soyayyar Ku Kuyi Amfani Da Waɗannan Hanyoyin:


Da Zaran Matsala Ta kunno Kai A Zamantakewar Aurenku Ko Soyayyar Ku Kuyi Amfani Da Waɗannan Hanyoyin:

SHARE 🔵
#Tsangayarmalamtonga 

Soyayya na gaskiya a kullum aci samun matsalar ake. Zaman aure yana tattare ne da matsalar zamantakewa. Duk wasu ma'aurata ko masoyan da aka gani sunada tasu matsalar.

Sai dai kuma rashin iya amfani da dabarun shawo wannan matsalar tsakanin masoya ko ma'aurata yake sa karamar matsala ta dawo babba. Ko kuma abunda zasu gyara da kansu sai su bari har wasu suji.

Idan har matsala ga gifta tsakanin masoya ko ma'aurata, ga wasu hanyoyin da zaku bi domin sasanta kanku da kanku.

 
1: Kada guda ya hana guda fadin abunda yake damunsu a lokacinda aka samu bacin rai.
Haka nan yunkurin cewa dole sai guda yayi magana a lokacinda bai da bukatar hakan saboda bacin rai ba dace ba.

Akwai mutanen da idan aka bata musu rai basa iya magana. Wasu ma so suke su rabu da wajen. To idan masu irin hakan ne kada guda yace zai takurawa gudan dole yayi magana ko ya tsaya ko zama.

Kawai barshi ko ka barta tayi abunda take ganin zai sa zuciyarta ya samu sanyi.

2: A Lokacinda aka batawa guda rai cikin masoya ko ma'aurata. Mai laifin ya nuna tausayawa da nadamar abunda yayi. Hakan zai sanyayawa wanda aka bata jin sauki.

3:Kada masoya ko ma'aurata suce dole sai guda ya amsa laifinsa kamin maganar ya wuce. Akwai hanyoyin da mutum yake yarda yayi kuskure ba tare da ya furta ba.
Neman dole dole sai ya amsa laifinsa kamin a bar maganar nan ma neman karawa matsalar tsawo ne.

4:Kada samun matsalarku ku daina yarda da juna.
Babu wanda yafi karfin yayi kuskure, idan wannan shine karo na farko na aikata laifi sai a yiwa juna uzuri ya kuma yafiwa juna a wuce wurin. 

5: Duk da kun samu matsala da juna, wannan ba yana nufin zaku daina ganin mutuncin juna bane. Dole ne ku ci gaba da girmama juna bayan sulhu. 
 
Babban matsalar da ake samu ga masoya ko ma'aurata idan sun samu matsala shine na rashin baiwa juna dama domin kowa ya saurayi kowa. Hakan nan wasu bamasa tinkaran junansu domin tattaunawa sai kawai guda ya kama gasa da guda. Wanda hakan kara rura wutar matsalar hakan zai yi.

Zama a tattauna akan matsalar daya kunno kai a tsakanin masoya ko ma'aurata shine yake karawa matsalar girman zama babba. 

Don haka muddin ana bukatar a cigaba da rayuwa da juna, kada a boyewa juna kuskure, laifi rashin fahimtan da aka samu.

Post a Comment

0 Comments