Idan Zaka Yiwa Budurwarka Wadannan Abubuwan Babu Wani Namiji Da Zata Saurara:


Idan Zaka Yiwa Budurwarka Wadannan Abubuwan Babu Wani Namiji Da Zata Saurara:

SHARE 🔔
#Tsangayarmalamtonga
 
Rashin tabbacin ko saurayinta da gaske yake sonta da aure shike sa wasu matan sun baiwa wasu mazan damar yin soyayya da wani bayan saurayin da suke dashi. 

Akwai wasu halaye da dabi'un da duk namijin da zai yiwa macen da zai aura tsakaninta da maza sai da gaisuwa ko wani harka na daban. Wadannan abubuwan sun hada kamar hakan.

 
1: Duk macen da mai sonta zai bata lokaci a duk lokacin da take bukatarsa. Baya barinta cikin kadaici, wannan namijin zai mata katutu a zuciyar ta. 

Wasu lokutan kadaici yake sa wasu mazan suke galaba a wajen macen da take da wanda take so. A lokacinda take son hira kuma bakada lokacinta, idan wani yayi dacen wannan lokacin ya kawo mata hari zata bashi dama. Don haka a duk lokacinda budurwarka ta nemi zama da kai muddin ba a lokacin neman taro bane.
 Amsa kiranta.

2: Ba kawai lokaci zaka Bata ba idan kana son ta daina kula wasu mazan. Nuna mata soyayyar ka a zahiri.

Tabbatar mata kana sonta da gaske ta baka da kuma a aikace. Nuna mata a duk fadin duniyan nan babu namijin da zai sata farin ciki da kwanciyar hankali irinka.

Muddin mace ta tabbatar da wadannan kalaman naka a zahiri, ba zata kula wasu mazan ba da sunan soyayya. 

3: Idan zaka yawaita nunawa macen da kake so kula ba sanin halin da take ciki akai akai ta hanyar waya ko sakon text zaka cusawa mace sonka a zuciya.

Sau tari wasu matan sunada matsala amma rashin yawan neman halin da suke ciki yake sa wani yayi gamo da katar ya sameta cikin wani bukatar da yana warware mata shi kawai sai taji hankalinta ya kama da shi.

Don haka mace tana bukatar bibiya a lokaci lokaci domin sanin halin da take ciki.

4: Idan kana soyayya na gaskiya da mace kada ka jira sai ta nemi kudin kashewa a wajenka. Ka zama namiji mai fahimtar yanayi, kana kuma mata toshi a lokaci zuwa lokaci ba tare da sai ita ta nema ba.

Yawancin matan da ake kwacesu daga wajen samarinsu saboda abun hannune ko kyautuka na musamman da wani zai mata. Kaima ka zama namiji wanda yake da kyauta ba sai an nema ba. Ka kuma iya sayo mata gift a lokuta na musamman da kuma kyautan bazata.

5: Idan kana so macen da kake nema ta maka kallon Autan maza, ka nuna mata yarda da amince. Ka kauda duk wani zargi daga gareta. Ka mata gyara idan ka fahimci wani kuskuren da take so tayi ko tayi ko take yi.

Ba duk maza suke da akida na yarda da Yan matansu ba. Amma kana nunawa budurwa da zaka aura ka aminta da ita, zata maka kallon na daban cikin maza, wanda hakan zai hanata baiwa wasu mazan dama akanta. 

6: Duk wata mace tana burin zama da namiji mai saukin kai. Kada ka zama irin samarin nan dake da takurawa mace saboda suna so su aureta.

Idan ka kira bata dauka ba, ka rika mita, idan ka aika sako bata baka amsa ba ka dinga fada kenan. Idan aka kirata a waya sai ka san was ya kira kuma Mai yake so ko take so. Mata basu son irin haka.

Ka zama mai saukin kai amma ba wanda zai zama gailo wajen kasa magana akan abunda akayi ba daidai ba. 

7: Bama macen da kake so ka aura, ko kare ne na gidanka Yana son a girmamashi.
Nunawa wacce kake neman girmamawa da kuma mutunta. Ta fahimci kai ba irin mazan nan bane dake daukan mace baiwa idan sunyi aure.

Kana nunawa wacce kake so da kai da ita duk ibada zakuyi idan kunyi aure zata kasa kwatuwa daga wajenka.
Sau da dama wasu mazan kamin su auri mace suke lanlabata suke girmamata, da zaran anyi aure kuma ko murmushin miji an daina gani sai idan yana da bukata.

 Nunawa taka sam ba haka kake ba. Zaka bata dukkanin hakkokinta dake kanka bayan aurenku.

8: Idan ka kasance irin mazan nan ne masu yiwa mace gyara cikin natsuwa bada hauragiya ba, zakayi saurin yin kaca-kaca da birnin zuciyarta yadda ba zata samu gurbi ajiye wani namijin ba.

Akwai mazan da tun kamin aure basu da ragayya. Idan mace ta musu kaifi sai sun mata cin mutunci da tozartawa. Wasu harda zagi da kuma duka. Duk macen data aminta da irin wannan mijin tun kamin aure ta zabawa kanta zaman kunci ba zaman aure ba.

9: Kada ka tursasawa macen da kake so da auren dole sai tayi akidarka ko amfani da fahimtarka.
Muddin zaka baiwa mace daman fadi da yin ra'ayin wadanda ba illa ne dasu ba. Wannan macen bazata iya rabuwa da kai ba, bare ma har wani ya samu galaba akanta ya rabaku.

10: Idan zaka tallafawa ko karfafawa macen da kakeso da aure gwaiwa akan abunda ta sanya a gaba ko burinta da take son ta kai gaci, mai rabaka da ita sai mutuwa.
Akwai mazan da mace tana karatu suke cireta kawai saboda suna son su aureta. Wasu suce sai sun daina aiki ko sana'ar da suke yi kamin su auresu. Wannan zamanin dane a lokacinda Malaman wannan zamani suke nunawa miji yafi uban mace daraja.

A wannan zamanin duk wani alkawarin da namiji ya daukarwa iyaye kamin aure, amma yana aurenta duk sai ya soke su da tunanin yansu shine mijinta sai abunda yace. Karya ne, jahilci ne yasa iyaye na lokacin suke barin yarsu a gidan miji bayan karya alkawuran da ya dauka. Har yanzu akwai wasu maza masu wannan akidar daya ci karo da addinin islama.

A wannan lokacin mata suna bukatar namiji ne wanda zai karfafa musu gwaiwa ya kuma talaffamusu cimma burinsu. Idan wacce kake so ta fahimci hakan kake, babu mai shiga tsakaninsu.

 
Duk kuwa da kana iya yiwa mace dukkanin wadannan abubuwan amma wani ya rabaka da ita. Wacce za a kasa rabaku idan zaka mata wadannan abubuwan sunfi yawa.

Kada kuma ku manta, neman aure ba a yinsa da son rai. Abune da ake baiwa Allah zabi. Kila kai wacce kake so da aure ba alheri bace a rayuwarka. Wannan da kake ki din nan dai ita wacce zata zamemaka matar rufin asiri. Don haka a ajiye son rai wajen neman aure a baiwa Allah zabi.

Post a Comment

0 Comments