Abin da ke jawo warin al'ura da yadda za a magance shi.
@BBCHAUSA.
1. Kula da tsafta
Wanke tsakiyar ƙafafunki. Ku samu dan ƙaramin tsumma ki goge al'aurarki, zai iya taimaka wajen wanke matacciyar fata da zufa da kuma datti.
Za ku iya amfani da sabulu mara ƙarfi ku wanke wajen al'aurar, ban da cikinta.
Kar ki wanke can cikin al'aurar da sabulu don yana iya kashe ƙwayoyin halittar da ke kare wajen daga kamuwa da cututtuka. Gara kawai ki yi amfani da isasshen ruwa ki ɗauraye cikin.
Al'aura tan tsaftace kanta da kanta.
Ku guji amfani da sabulu mai kamshi, kamshin sabulun da sinadiran da ke cikin sabulun na iya sauya yanayin lafiyar al'aurar. Amfani da ruwa zalla ma ya isa ya wanke al'aurar mace.
2. Ki guji sa turare a wajen
Dole sai kin guje wa sanya turare a al'aurarki. In har so kike ki yi ƙamshi sai dai ki dan shafa a tsakanin cinyoyinki, amma sa wa a cikin al'ura illa ce sosai da ka iya jawo maki wata cutar.
3. Sauya ɗan kamfai a kai- akai
Idan kuna yawan amfani da kamfai da aka yi da siliki ko leda ko na roba to lokaci ya yi da za ku koma kamfai na zallar auduga mai laushi.
Auduga mai laushi na taimakawa wurin bai wa al'aura iska kuma tana yin kyakkyawan aiki a wurin kawar da gumi da ruwa daga jikinku.
Yawan danshi zai iya sa ku kamu da ƙwayoyin cuta da za su yi wa al'aurarku illa.
Sannan ya kamata ku kula da yawan sauya kamfai da siket saboda idan suka yi datti kuma kuka maimaita su to akwai yiwuwar su haifar da warin al'aura.
kamfai na zallar auduga mai laushi.
Auduga mai laushi na taimakawa wurin bai wa al'aura iska kuma tana yin kyakkyawan aiki a wurin kawar da gumi da ruwa daga jikinku.
Yawan danshi zai iya sa ku kamu da ƙwayoyin cuta da za su yi wa al'aurarku illa.
Sannan ya kamata ku kula da yawan sauya kamfai da siket saboda idan suka yi datti kuma kuka maimaita su to akwai yiwuwar su haifar da warin al'aura.
Sanin lokacin ganin likita:
Idan wannan warin yana tare da alamun da ba ku saba gani ko ji ba, ya kamata ku guji yin magani a gida ku tuntubi likitanku.
Misali, idan warin al'aurarku ya fi na al'ada ƙarfi kuma kun lura cewa yana kara ƙarfi, to kuna bukatar ganin likiti.
Haka nan, idan ku nji al'aurarku ta fara wari kamar na "kifi" wannan dalili ne na ganin likita. Wari mara kyau alama ce ta kamuwa da cutar al'aura.
Wadannan warin na iya zama alamun matsala. Kuna iya bukatar likitanku don ya rubuta magani ko hanyoyin magance matsalar.
Ba za ku so ku jinkirta magance matsalar ba domin cutar al'aurar da ba a nemi maganinta ba kan iya jawo matsalar rashin haihuwa idan ta daɗe ana fama da ita.
Wasu ruwa da ke fitowa daga al'aurar mace na iya zama na ka'ida. Idan kun lura da canji a launin ruwan, misali launin da ku ka saba gani fari ne ko bai da kala amma sai ku ka fara ganin wani launin daban, to zai iya yiwuwa kun kamu da cuta.
Yawanci kaikayin al'aura ba matsala ba ce, amma idan ku ka fara jin kaikayin ya fara yawa ko kuma ya fara zafi da radadi, to alama ce na babbar matsala.
Hanyar magance sake fuskantar warin al'aura:
Da zarar kin kawar da warin al'aura wanda ba a saba ji ba, kiyaye wadannan shawarwari don hana wata matsalar:
Kula da cin lafiyayyen abinci mai sinadiran gina jiki. Yawaita cin ƴaƴan itace, da kayan lambu. Daidaitaccen abinci yana samar da lafiyayyen jiki, kuma hakan ya hada da al'aurarku.
Kasance mai yawan shan ruwa. Shan ruwa mai yawa yana da amfani sosai a dukkan jiki ba sai ga fata ba kawai.
Yana iya taimaka wa ga lafiyar al'aurarku, kuma, ta hanyar karfafa gumi mai kyau da sakin ruwa.
Guji wanke al'aurarku da sabulu, likitoci sun ba da shawara a kan ka da ku taba wanke cikin al'aurarku da sabulu.
Za ku yi zaton cewa sabulu zai wanke al'aurar da kyau amma sabulu kan iya jawo cuta. Ku bar jikin ku ya yi aikin da ya kamata, saboda al'aurarku na wanke kanta.
Ku dinga wanke al'aurarku kafin saduwa da kuma bayan saduwa. Jima'i kan iya jawo yaduwar ƙwayoyin cuta, da kuma abubuwan waje kamar man shafawa da maniyyi daga kwaroron roba.
Ku daina amfani da matsattsun kaya. Tufafi masu matsewa ba sa barin al'aurarku ta sha iska. Samun isasshiyar iskar oxygen na da mahimmanci ga lafiyar al'aura.
0 Comments