┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈
Zaka gane kana da cikakkiyar tsaftar al'aura ne abinda ake kira Genital hygiene:
1. Idan ya zamto baka sunsuna wandonka kafin ka yanke shawarar ciresa ka canza wani ko wankesa.
2. Idan ya zamto inka jima azaune ka tashi zufa ya nishi gun kai da kanka baka jin alamun tsami ko hamami na tasoma.
3. Idan kana ware gajerun wandunan buga kwallo daban tare da wankesu kullum ka dawo, Ba barinsa ya bushe ajika ba kuma ka cigaba da zama da abinka matsayin wandon yau da kullum
4. Idan ya zamto bazakaji kunya ba da ace budurwarka da kake So zata gansa ayanayin da yake. Bawai ka fito ta ganka ba.... A'a amma ya zakaji inda zata gani ace wannan itace tsaftarka
5. Idan ya zamto wajen aski ba iya saman mararka kaɗai kake askewa ba, Aah kana hadawa har tsakanin matse-matsi da bakin dubura ka aske fes.
6. Idan ya zamto baka wuce sati uku, a ka jima sati 4 batare da kai aski ba, hammata da duk wani loko
7. Idan ya zamto wajen tsarki ba iya gabanka kake wankewa ba kurum kana hadawa har dubura
8. Idan ya zamto cikin Maza ko Mata al'aura ake fara wankewa kafin dubura, tare da kaucewa kuma dawo da hannun al'aurar.
9. Idan baka bin Matan Banza, ko ina kana tura halittarka batare da amfani da koda kwaroron roba ba.
SHAWARAR DA ZAN QARA MUKU DA ITA SHINE:
1. Inda hali kar kake shaving da reza fiye da sau 1 ko 2 batare da ka canza ba.
2. Ga Maza ko Mata idan ya zamto ana samun kuraje bayan askin toh ake samun ruwan dumi sai azauna aciki akalla minti 5 ko 10 sannan sai ai shaving din. In akwai powder ana iya amfani da ita.
3. Ba'a son fesa turare a matse-matsi ko fata kai tsaye saboda wani nada alcohol da ana iya samun irritation... Don haka atube boxer din ko pant din afesa turaren ajikinsa yadda akeso bayan seconds 30 zuwa minti 1 sai asa ajika shikenan.
4. Idan ma bazaka iya canza gajeren wando kullum ba toh de kar yake wuce awa 48 ajikinka. Me tsafta shine wanda gajeren wandon da yake yini dashi daban, sannan inyamma tai yai wanka zai kwanta gajeran wando baccinsa ma daban ne.
5. Bayan fitsari banda gagawar mikewa ake istinja'i (wato tatso ragowar fitsarin ahankali) sannan ai tsarki, yin haka zaisa wandonka bazaike yin staining ba, musamman inbaka barin gashi buzu-buzu har ya riqa ƙari ko bashi, domin gashinan na can kasa wajen dubura da matse-matsi shike taimakawa wajen sa gajeren wando wari inya haɗu da zufa galibi bawai wannan me yawan na saman al'aura ba, shyasa kar araina kankantarsa ake askewa koda duk sati-sati ne.
6. Ka kiyayi maganin qara karfin jima'i haka kurum babu wani dalili don son birge Mace ko don abokinka yace maka. Ka tsaya daidai abinda jikinka zai iya, kar matsalar zuciya ta sameka tunda kuruciyarka ina me tabbatarma zakai mutuwar farat daya inkai wasa.
A karshe ka tuna: Matarka ma naso tajika kana kamshi kamar yadda kakeson ta zamo tsaf ko yaushe.
✍🏻
Ibrahim Y. Yusuf
0 Comments