ILLOLIN TSARKI DA SABULU GA MACE:
Barkan mu da wannan lokaci, 'yan uwa fatan kuna cikin koshin lafiya, Allah Ya sa haka, amin. A wannan makon, shafinku mai farin jini, zai muku tsokaci ne kan illolin da tsarki da sabulu kan haifar wa 'yan uwa mata.
Bisa kyakkyawan zato, mafi yawan mata kan yi tsarki da sabulu ne da manufar tsaftace jikinsu, sai dai, kash, rashin sani ya sa su ke aikata hakan, domin da sun san irin lahanin da ya ke mu su da ba su yi tsarki da sabulu ba.
Wani kwararren likita a asibitin koyarwa na Jami'ar Ibadan, Imran Morhason-Bello, ya ce, wasu abubuwa da muta ke aikata wa cikin rashin sani, kamar amfani da turare ko sabulu a al'aurarsu, na rage mu su jin dadi yayin saduwar aure.
Saboda da haka sai likitan ya shawarci 'yan uwa mata kan su guji yin amfani da sabulu ko turare a al'aurarsu da nufin tsabtace wajen, don kuwa a maimakaon gyara hakan na iya janyo mu su mummunar illa, inda zai haifar da rashin jin dadin jima'i da mai gida.
Dokta Morhason-Bello, ya ba da wannan shawara ne a wata makala da ya gabatar wajen wani taro da aka gudanar da nufin dakile al'adar yi wa mata kaciya a Najeriya.
Taron, wanda Ma'aikatar Lafiya ta Tarayya ta shirya tare da taimakon Ƙungiyar (UNPFA) ta majalisar dinkin Duniya, da Jami'ar Ibadan an gudanar da shi ne a birnin tarayyar kasar nan, Abuja.
Kwararren likitan ya bayyana cewa, ba kaciyar mata ce kawai ke haifar da mummunar illa ga al'aurar mata ba wajen jin dadi da gamsuwar jima'i, har ma da amfani da sabulu ko turare da mata ke yi da nufin tsaftace al'aurarsu ko kuma amfani da wasu magungunan karin ni'ima don gamsar da mai gida yayin jima'i.
Ya ce, lokacin da mace ta saba da yin amfani da sabulu ko turare wajen tsaftace gabanta, ko kuma yin amfani da magungunan karin ni'ima, to sannu kan hankali hakan zai yi tasiri a al'aurarta, sannan daga bisani sai ya yi mata mummunar illa ta hanyar hana ta jin dadin jima'i.
A cewarsa, "fatar jikin dan-tsakan mace da ta tsakiyar farjinta ba ta da kauri, kuma cike suke da jijioyoyin jini ma su yawan gaske, sakamakon yawan amfani da sabulu ko turare ko kuma kayan sanya dadin jima'i da mata ke yi, sai fatar ta duskure ta gaza kai sako ga kwakwalwa a karshe sai hakan ya haifar wa mace rashin jin dadi yayin da mai gidanta ke saduwa da ita.
Dokta Morhason-Bello ya kara da cewa, domin kubuta daga wannan matsala, dole ne mata su guji cusa magungunan karin dadi a farjinsu, ko kuma sanya magungunan zamani ba tare da iznin likita ba, hakanan su guji yin amfani da turare, ko sabulu, saboda hakan zai hana su jin dadin jima'i, baya ga haka ma zai iya haifar mu su da cututtuka a farjinsu.
"A gaskiya, wasu daga cikinsu na amfani da hannayensu wajen cusa waɗannan magungunan cikin farjinsu , abin da ba su sani ba shine, idan su ka dauki tsawon lokaci su na aikata hakan, sai ya haifar mu su da matsewar farjinsu fiye da kima. Mun sha samun matsalolin rufewar kofar farjin mace gaba daya saboda amfani da wadannan kayayyaki da mu ka ambata a sama.
"Idan mace ta samu kanta cikin wannan matsala, don warkar da ita akwai buƙatar a yi ma ta aikin tiyata nau'i daban-daban ko kuma ayi kokarin samar ma ta da wata sabuwar kofar farji. Kafin a samu nasarar hakan kuma dole matar ta zauna a asibiti tsawon watanni ma su yawa.
"Saboda haka, abin da ya fi dacewa ga mace don tsaftace farjinta shine ruwa mai tsabta kawai. Idan ta yi amfani da duk wani abu da yake dauke da wani sanadari kamar sabulu ko turare, zai iya kashe kwayoyin halittar da Ubangiji Ya halitta mata don farjinta ya zauna lafiya, sannnan ta samu jin dadin jima'i da gamsuwa.
Amma yayin da ta lahanta kwayoyin halittar da Ubangiji Ya yi ma ta, sai kwayoyin cuta su samu damar shiga gabanta. A karshe irin Wadannan mata za su fara fitar da gurbataccen ruwa ta gabansu, "inji shi.
Ya ci gaba da bai wa mata shawarar cewa, kamata ya yi su ke wanke farjinsu da ruwa mai tsafta kadai, kuma "kar mata su damu da wani wari da ke fita daga farjinsu saboda wannan warin dabi'ar da Allah Ya halicci wajen ne, matukar ba wari ne na cuta ba, wanda shi kuma warin cuta ya na kasancewa mai yawa ne".
0 Comments