Wasu Abubuwa Da Maza Suka Fahimcesu A Baibayi Game Da Matantakan Mace:


Wasu Abubuwa Da Maza Suka Fahimcesu A Baibayi Game Da Matantakan Mace:

 
Idan da zaka samu namiji dan shekaru 70 ko sama kuyi hira dashi akan Matantakan mata, zaka fahimci da akwai abubuwa da ya fahimcesu ba daidai ba duk da wannan tsawon shekarun da yayi yana mu'amala da mace ko mata. 

Misali shine, maza da dama suna daukan cewa duk macen data yi karatu mai zurfi dole ne ana zina da ita ko kuma ta taba zina. Wannan haka nan kawai mutane suka kirkiro wannan tunanin suka cusa shi cikin mutane kuma mutane suka yiwa harkar maraba. Kamar yadda duk wata mace take dauka duk namijin da ya mata kyauta ko taimako dole akwai wani dalilinsa na yin hakan. Mata basu cika yarda cewa namiji na iya musu abu saboda Allah sai dai idan akwai abunda yake bukata daga wajenta. Wannan tunanin yayi tasiri matuka a zuciyan mata.

Ga wasu abubuwa nan da ba duk maza bane suka musu fahimta na hakika ba game da Matantakan mata (Women Sexuality):

#tsangayarnalam 

1: Ba duk maza bane suka yarda cewa mace na iya rasa budurcinta ba tare da tayi Jima'i ba.

Wasu mazan basu yarda shi tantanin budurcin mace na iya buduwa saboda wasu dalilan da bana Jima'i ba.

2: Ba duk maza bane suka fahimci cewa yiwa mace ciki daban, haka kuma gamsar da ita a Jima'ince shima daban ne ba.
Wasu mazan idan mace ta musu korafin cewa bata samun gamsuwa a Jima'i da shi. Sai kaji suna cewa "Amma kuma nake miki ciki". Maza da dama sun kasa bambamce shigan ciki da jiyar da mace dadin Jima'i.

3: Yawancin maza basu fahimci mata suna shiga wani mawuyacin kunci ba a lokacinda aka sadu dasu aka kasa gamsar dasu ba.

Wasu mazan suna dauka muddin idan su sun samu gamsuwa to ita ma macen ta gamsu don haka sun fitar batunta.

4: Akasarin maza suna dauka mata suna samun gamsuwa ne ta yawan zuwan kan da suke yi.

Inda zaka ji wasu mazan na cewa sun kawo sau 5 ko sau 8. Duk wannan wahalar da kai muddin baka iya gano lagon matarka ba na yadda zaka gamsar da ita ba.

5: Ba duk maza bane suke da illimin sanin kashi 60 cikin 100 na mata basa gamsuwa ba tare da an yi musu wasa da dantsakansu ba ko sunyi wasa da shi a lokacin da ake saduwa dasu ba.

Mafiyawan maza sun tafi a tunanin cewa shigan da fitan azzakari cikin farjin mace shike sata samun gamsuwa wanda abun ba haka yake ba.


6: Tarin mazan da zaka tada dasu da wahalar gaske ka samu mafiya yawansu sun fahimci cewa amfanin dantsakan mace shine ya jiyar da ita dadin Jima'i kawai amma baida wani amfani banda wannan.

7: Yawancin maza basu fahimci cewa mace tana kara girma da tsufa, tana kara sha'awar Jima'i ba. Ba kamar maza ba, suna girma karfinsu na raguwa.

Saboda hakan ne masana illimin Jima'i suke shawaran kada a samu tazara mai yawa tsakanin namiji da macen da zai aura. Domin shekaru kadan zai kasa gamsar da ita a dai-dai lokacinda ita kuma take tsakiyar bukatar sa.

Domin ita mace tana girma dantsakanta na kara tsawo, shi kuma namiji yana girma, gabansa na kankancewa.

8: Maza da dama suna daukar mace mai karancin shekaru tafi mai yawan shekaru jin dadin Jima'i. Sam abun ba haka yake ba. Asali ma ita mace mai karancin shekaru bazata soma sanin dadin Jima'i ba har ta soma zuwan kai sai ta dauki tsawon wasu lokuta ana saduwa da ita.

 Wasu sai bayan sunyi haihuwa 2 zuwa 3 daga wannan lokacin suke soma jin dadin Jima'i da mazajensu.

9: Mafi yawan maza har da wasu matan ma suna daukan cewa girma ko kaurin azzakari suke sa mace taji dadin Jima'i. Sai dai wannan tunanin sam ba haka yake ba. Gamsar da mace a Jima'i ince ya ta'allaka ne a yanayin fahimtar da namiji yayiwa matar tasa a Jima'ince.

10: Mafiya yawan maza suna daukan cewa duk wata mace na son ayi wasa da gabanta. Sai dai abun sam ba haka yake ba. Da akwai mata da damar gaske muddin aka tsutsi gabansu ko yi musu sakace, daga wannan lokacin an kwantar musu da sha'awar su na Jima'i.

Wannan yasa muddin namiji na son ganin yana gamsar da matarsa dole ne ya tabbatar da abubuwan da take so da wadanda bata so, kamin, lokacin da kuma bayan kammala Jima'i domin amfani dasu da kuma kauce musu.

#Tsangayarmalamtonga

Wadannan wasu daga cikin daruruwan abubuwan da maza suka kasa fahimtar su a tare da Matantakan mata.

Post a Comment

0 Comments