Wasu Dabi'un Dake Koran Maza A Wajen Budurwa:


Wasu Dabi'un Dake Koran Maza A Wajen Budurwa:

SHARE 🌋💏
#tsagayarmalamtonga 

Ba duk maza bane suke zuwa neman auren mace da wasa ba. Sai dai duk kyankyawan niyar da wasu mazan suke dashi akan wacce suke so da aure. Wasu matan mugayen halayensu ke sa maza suke guje musu bayan sun soma soyayya dasu.

Ga wasu munanan halayen da 'yan mata suke yi dake suke koran samari:

 
1: Naci: Shi namiji idan kika nace masa, kika nuna masa baki iya rayuwa sai dashi. Kullum idan baki ganshi ba bazaki iya cin abinci ko bacci ba.

Ko duk inda yake sai kinje kin sameshi. Muddin zaki nacewa namiji da hakan watarana zaki nemeshi ki rasa.

Duk irin son da kika yiwa namiji kada ki nace masa idan kina son ya kamu da soyayyar ki.

2: Yawan Saka Hotunanki A Shafukan Zumunta: Duk budurwar dake da dabi'ar caba ado da kwalliya ta rika turawa a a shafukan ta na sada zumunta bayan tasan tanada wani mai sonta da gaske. Tana iya yin biyu babu.

Yawan saka hotunanki a Shafukan sadarwa akasarin maza suna daukar mace mai irin haka batada kamun kai. Mace ce dake tallan kanta wajen maza. Hakan zai sa namiji ya fasa niyarsa na aurenki.

3: Mu'amala Da Kawayen Banza: Babu namijin da zai aureki muddin ya fahimci kawayenki ba masu kamun kai bane. 

Mai son aurenki yana sone ya rika ganin ki da kawayen kirki a tare dake. Hakan zai tabbatar masa da kema ta kirkince. Amma idan akasin hakan ya gano, zai iya cikawa wandonsa iska ya kara gaba. 

 
4: Yawan Roko: Muddin kika zama mai yawan daurawa mai sonki nauyi da rokonsa kudi, kina iya koran wannan saurayin naki cikin sauki. 

Wasu 'yan matan bama bukatunsu kadai ba, matsalar gidansu gaba daya suke daukowa su daurawa mai sonsu da aure, hakan kuma ba daidai bane. Domin kina iya koransa koda kuwa mai hali ne shi.

5: Tara Samari: Yawan tara samari dabi'a ne da yake saurin koran namiji wajen mace.

Tara maza yana alamta kodai mace mai kwadayi ce ko kuma mazinaciya. Wannan yasa duk namijin daya zo aurenki dagaske kuma yaga kina tara samari zai arce nan da nan. 

6: Kazanta: Shima yana koran namiji wajen mace daya zo nemanta da aure. 

Mace 'yar kwalliya ce da ado. Da zaran namiji ya fahimci wacce yake so kazamace tana iya koransa.

 
Wadannan wasu ne daga cikin halayen da suke koran maza a wajen macen da suka zo neman aurenta. Da fatan mata zasu kiyaye.

Post a Comment

0 Comments