NI MACE CE MAI MATSANANCIYAR SHA'AWA (MAZIYYI YANA YAWAN ZUBO MIN) SHIN YANA WAJABTA WANKA? SA'ANNAN SHIN ZAN IYA AMFANI DA HANNUNA, NONONA KO WANI ABU MAKAMANCIN HAKA NA GAMSARDA KAINA DAN GUJEWA SABAWA ALLAH?
*TAMBAYA*❓
Aslm alaikum malam Tambayata ta parko itace: macece takasance mai karpin shaawa kuma koda yaushe takan fidda farin ruwa (mazi) yakan zubo koda tana sallah ne, sannan idan ta kwanta barci takan yawaita mafarki saboda yanayin karpin shaawarta. Kuma aduk lokacin datake period shaawanta yana kara tsananta sosai. To tambayata anan shine duk lokacin dataga wannan ruwan sai tayi wanka ??? Kuma gameda karpin shaawarta maimakon taje tapada sabon Allah zata iya wasa da hannunta don gamsar da kanta, ko kuma breast dinta kodai makamancin hakan ?? Saboda tana gujewa sabawa mahallici. DAN ALLAH MAL. KABANI CIKAKKIYAR AMSA NGD DAGA DALIBARKA...
*AMSA*👇
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ.
Da farko dai Maziyyi baya wajabta wanka. Maziyyi yana fitowa ne a dalilin motsawar sha'awar Namiji ko Mace. Maziyyi yana warware alwala amma baya lalata azumi. A yanayi na yawan fitar maziyyi malamai sunce ya zama dole mutum ya tsarkake al'aurarsa da wajen da maziyyi ya shafa tareda yin sabuwar alwala aduk lokacin da zaiyi sallah. Idan kuma kika ga maziyi bayan kin gama sallah to zaki wanke muhallin amma bazaki sake sallah ba. Wato idan fitar maziyyin ya yawaita kuma ba kece kike janyo fitarsa ba ta hanyar chating da samari ko kallon hotunan batsa da sauransu, to koda kin fara sallah babu maziyyin saida kika kammala kika ganshi to ba zaki sake sallar ba saboda abin yafi karfinki. Saboda fadar madaukakin sarki (لا يكلف نفسا إلا وسعها) Allah baya kallafawa rai abun da ba zata iya ba. Amma fa ki sani idan fitar daga gare ki ne to kece ke bata sallarki da kanki. Saboda haka sai kisan mafita, kiji tsoron Allah ki tuba ki daina abubuwan da kike yi masu janyo fitarsa. Haka kuma idan kikayi sallah da maziyyi ajikinki acikin mantuwa, anan ma zaki wanke ne idan kin tina amma bazaki sake sallah ba. Idan maziyyi ya fito kuma kikayi sallah batareda kin wanke ba. Malamai suka ce sai kin sake sallah bayan kin wanke. Saboda shi Maziyyi najasa ne kuma fitarsa yana warware alwala. Amma kuma idan fitar tasa ya kasance koda yaushe hakane ba yanda zaki yi sallah ba tare da kinji ya fito miki ba kuma ya kasance ba kece ke janyowa kanki fitarsa ba to anan kam zaki ci gaba sallarki kamar yadda muka fada a sama:
(لا يكلف نفسا إلا وسعها)
Allah baya kallafawa rai abun dabazata iya ba. Saidai idan kika gama ki wanke gabanki ki wanke wajenda ya taba ko kiyi yayyafi, idan zaki sake wata sallah ki sake alwala saboda alwala kawai yake karyawa baya wajabta wanka. Akan wanke daukacin muhallin da maziyi ya shafa a jiki da sutura. Haka kuma za'a iya yayyafi a sutura a bigiren da maziyyi ya shafa kamar yadda yazo a hadisin tirmizi. (Ibn Qudaamah a littafinsa na Al-Mughni, 1/168). (Sahihul Tirmizi, 115, Albani ya ingantashi). (Al-nawawi, sharhin sahihul Muslim, 3/213)
*WASA DA FARJI DA YATSA, NONO, KO AMFANI DA WASU ABUBUWAN BIYAN BUKATA KAMAR SU; CANDLE, DILDO ETC*
Amfani da gaba dayan wadannan abubuwan dake a sama haramun ne. Dalili kuwa shine dukansu istamna'i ne wato mutum yai wasa da gabansa har maniyyi yafita mace ko namiji. Biyan bukata ba tare da mata ko miji ko kuyanga ba kenan. Wanda kuma haramunne a alqur'ani da hadisi. Ibnu kaseer rahimahullah yace : Imamu shafi'i da wadanda suka goyi bayansa yakafa hujja da haramcin wasa da gaba da fadin Allah madaukakin sarki.
(والذين هم لفروجهم حافظون إلا على أزواجهم أو ما ملكت أيمانهم فإنهم غير ملومين فمن ابتغى ورآء ذلك فأولئك هم العادون.
Muminai sune wadanda dangane dafarjinsu suke kiyayeshi, sai ga matayensu ko kuyanginsu dan basu kiyaye farjinsu akansu ba, su ba'ababen zargi bane, duk wanda yanemi wata hanya bata aure ba kota kuyangarsa wannan mai ketara dokokin Allah ne. Imamu shafi'i acikin littafin Aure yace saiya kasance Allah yabayyana kiyaye farjinsu saifa akan matayensu ko abinda damarsu tamallaka, sai yazama haramun idan ba matar ka bace ko kuyangarka sai Allah ya karfafi maganar dacewa " wanda ya nemi koma bayan hakan yana cikin masu taka dokokin Allah" Bai halatta amfani da azzakari ba sai akan matarka baiwarka, bai halatta jindadi dashi da hannu ba wallahu A'alamu kitabul ummu na imamu shafi'i.
Wasu malaman sun kafa hujja taharamcin istimna'i da fadin Allah madaukakin sarki
(وليستعفف الذين لا يجدون نكاحا حتى يغنيهم الله من فضله سورة النور 33
Wadanda basu samu damar aure ba sukame harsai Allah ya wadata su daka falalarsa. Sukace: umarni da kamewa yana nuna hakuri da rashin samun yin auren ko kuyangar.
A sunnah kuwa sunkafa hujja da hadisin Abdullahi dan mas'ud Yardar Allah takara tabbata agareshi yace: Munkasance tare da Annabi sallallahu Alaihi wasallam muna samari bamu samu komai ba sai Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace damu "ya ku taran samari duk wanda yasamu halin daukar dawainiyar iyali yayi aure, domin ya nasa kamewa daka gani, yana kuma tsare farji, wanda kuma bai samu dama ba to nahore shi dayin azumi domin azumi yana kariya daka fadawa haram. Bukhari 5066. Sai shari'a ta shiryar lokacin da mutum yagajiya wajen yin aure saiya dunga azumi tare da wahalarsa, shari'a bata shiryar zuwa wasa da farji ba, tare da saukinsa akan azumi tare dahaka ba'a halatta shiba.
*YADDA MUTUM ZAI MAGANCE WANNAN DABI'A SUNE KAMAR HAKA*
1-Wajibine mutum yakubutar dakansa daka wannan al'ada dan nisantar abunda Allah ya haramta da kwatanta bin umarninsa da gujewa fushin sa. Yan mata ku daina irin chating dinnan da samari musamman irin wanda ke motsarda sha'awa tsakaninku.
2-kawar da wannan da lafiyar jiki shine aure saboda wasiyyar manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ga samari.
3-Kawar da hadurra da waswasi da zuciya zata dunga sakawa, da shagalta datunani cikin abunda zai amfaneka duniya da lahira, domin yawan waswasi datunani yanakai mutum zuwa ga aikata abu, sannan mutum yasaba tayanda zai masa wahalar gasken gaske wajen kubuta daka aikata shi .
4-Kamewa daka gane gane domin kallace kallacen wasu abubuwa da hotuna nazane damasu motsi rayayyu ko matattu yana kai mutum zuwa haram.
5-Shagaltuwa da ibadoji kala kala dakin barin sarari ga aikin sabo.
6-Izna da cutukan dake haifarwa jiki na raunin gani da gabbai da ciwan baya da sauransu.
7-Riko da maganin manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam shine azumi.
8-Lazimtar ladubban shari'a yayin bacci na karanta zikirori
9-Kaskantar dakai ga Allah daneman taimakonsa.
10-Gaggauta tuba da istigfari da aikata ayyuka na gari, tare da rashin debe tsammani daga Allah.
11- Mutum ya nisanci kwana kai kadai adaki domin Annabi sallallahu Alaihi wasallam yahana mutum yakwana adaki shi kadai.
Sa'annan maganar cewa kiyi wasa da hannu domin gujewa sabawa Allah to ai shima wannan sabawa Allah ne. Saboda haka yar uwa ba wata hujja da zaki dinga amfani da hannunki ko wani sashe na jikinki domin ki biya bukatarki. Abinda zaki yi shine kibi hanyar da shari'ah ta tanadar in shaa Allahu zaki samu waraka, hanyar kuma itace wadancan shawarwarin dake a sama musamman wadannan:
~ Idan kina chating da samari mai motsa sha'awa kiji tsoron Allah ki daina.
~Ki yawaita yin azumi
~Ki daina kallon hotunan batsa ko hirar batsa da maza ko mata yan uwanki
~Uwa uba kuma shine ki sanarda iyayenki kefa aure kike so ayi miki aure ki huta. Nasan yanzu haka kina da samari masu sonki sai ki ba daya dama ya turo iyayensa. Kinga shikenan an huta.
Allah ya qara kare mu.
والله أعلم،
Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. _Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH (Ɓarayin fasaha)_
0 Comments