MAGUNGUNA KARIN KIBA MAZA DA MATA:
kwanciyar hankali da nutsuwa tareda kulawar miji sune kan gaba wajen saka mace murmurewa tayi kyau amma kuma akwai hanyoyi Biyu Dana kawo a wannan shafin kuma jama'a sunyi cikin ikon allah anyi nasara sunzo sunyi godiya saboda haka idan baki ganiba karanta yanzu:
(1) hanya ta farko kisamu yayan hulba ki tafasasu har sai ruwan ya canja saiki tace ruwan ki zuba masa Zuma farar saka da madara peak da born vita ki ajiye acikin firji da safe kafin kici abinci saikisha kafin mako Biyu zakiga abun mamaki
(2) ita kuma hanya ta biyu waken soya alkama gyada tareda aya zaki samu anaso kiyi garinsu saiki damasu kamar koko ki zuba madara peak kinasha wannan shima nabaki mako Biyu zakiga kin canja....
Maganin Karin Kiba:
Barkanmu da wanna lokaci sauda dama mutane kan Bukaci magani da zai rage musu kiba, amma a wani bangare da ban kuma mutanan suke neman kibar ido rufe.
Muna samun sakonni da dama kan maganin karin kiba, musan man daga yan uwa mata don haka yau shafin bincikensa ya biyo ta bangaren MAGANIN KARIN KIBA.
Ina fata zaa karanta wannan Darasai a nutse kuma a turawa yan uwa da abokan arzuka ta kafar WhatsApp ko Facebook.
Abubuwan da zaku buka suna hadar da.
🍎 Waken soya cokali 2.
🍏 Ridi cokali 2.
🌿 Dabino cokali 1
🍎 Hulba cokali 1
🍏 Gyada dai dai misali.
🍎 Madarar garin cokali 5
Yadda za'a hada maganin.
Da farko kusamu waken soya dinku mai kyau (Ku gyarashi sosai a fitar da tsakuwar jikinsa) saiku soyashi har sai ya fara kamshi, saiku sauke shi, bayan yayi sanyi saku dakashi sosai yazama Gari.
Haka zalika kusamu Ridin ku mai kyau (Ku gyarshi yadda zai zama babu wani datti a ciki) shima saiku soyashi yadda ya kamata saiku sauje bayan yayi sanyi saiku dakshi ya zama Gari.
Haka zaku samu Dabino dinku bushashe mai kyau shima ku dakashi yazama Gari.
Gyada kuwa saiku hada kunun Gyada da ita, bayan kun gama saiku dinga diban wadancen abubuwa da muka lissafa kuna sawa a cikin kunun Gyada din kuna sha kullum har tsawon sati biyu zuwa uku insha Allahu zaa baki labarin kibar da kika kara.
SHARE 🌐
0 Comments