Maganin basir kowanne iri da alamomin sa:



Maganin basir kowanne iri da alamomin sa:
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

 MENENE BASUR? 



Da farko dai a cikin duburar 'dan Adam akwai jijiyoyin jini wadanda wani lokacin suna samun matsatsi da talala mai takurasu. A lokacinda suka samu takurawa da yawa, sai su kumbura.

Kumburin wadannan jijiyoyin jini da kara matsi da takura a garesu cikin dubura shi ya ke sa wa kaga wani tsiro ya fito maka a bakin dubura, wanda jijiyar jini ce.



Za ka ji ciwo, ko kai-kayi koma zubar jini. 



Wannan shi ake cewa BASIR-MAI-TSIRO. Da akwai kuma nau'in Basur mai sanya yawan fitar hutu wato tusa da kuma mai sa cushewar ciki ko yin kashi mai tauri. Wani basir din kuma har yana sa tsatstsagewar dubura yayin fitar bayan gida. 

ALAMUN DA MUTUM ZAI GANE YANA DAUKE DA BASUR

.
Mutum zai rika fama da wadannan matsaloli


★ Kaikayi a dubura da bacin rai.

★Fitar jini idan ana bayan gida amma ba tare da anji zafi ba.

★ Ciwon jiki da rashin sakewa.

★Kumburar dubura.

★Fitar kashi curi-curi ko dunkule-dunkule tare da wahala. 



RIGA-KAFI YA FI MAGANI:

Wanda yake gudun kamuwa da cutar Basur sai ya yawaita shan dauri da daci, kamar gauta da sassaqen mangwaro ko sassaqen 6aure ko madaci, ko mur da makamantansu. Saidai a kula, kada a matsawa shan daci saboda matsalolin hanta. 

MAGANIN BASUR KOWANNE IRI.


A samu sassaqen itacen mangwaro, da sassaqen kadanya, da sassaqen dorawa, da sassaqen madaci amma madacin kadan ake bukata.


Sai a hade su wajedaya a wanke a zuba jar kanwa kadan.


A tafasa, kullum a sha rabin kofi sau uku kafin a ci abinci.


Idan kuma basur din mai tsiro ne ko wanda ake fitar baya, to idan an tashi sai a tafasa magungunan a zuba ruwan a cikin babban mazubi. Sai ka tsuguna, tururin ya dinga shiga karkashinka, idan ya dan huce kuma sai a shiga ciki a zauna tsawon yan mintuna ko kuma a dinga kama ruwa da shi.


Insha Allahu indai an hada wannan ana sha ana shiga ciki, to lokaci kadan za a rabu da basur kowane iri ne. 

SHARE 🌺

Post a Comment

0 Comments