Amfanin Jima'i Ga Lafiyar Ma'aurata:
Mai karatu barkanmu da wannan lokaci, da fatan ka na cikin koshin lafiya, Allah Ya sa haka amin. A wannan rana shafinku mai farin jini na Sirrin rike miji zai kawo ma ka wata tsarabar ma'aurata, mai taken, "Amfanin Jima'i Ga Lafiyar Ma'aurta".
Ta yiwu mai karatu ya yi mamakin wannan makala, ko ma ya tambaya "wannne amfani kuma jima'i ke da shi ga lafiyar ma'aurata ?. Idan ka na da wannan tambaya a cikin zuciyarka, to yau za ka samu waraka, Insha Allahu Ta'ala.
Ga wani jawabi da wani masani ya yi dangane da amfanin jima'i ga lfiyar ma'aurata, ka karanta shi, kuma shi mu ka zaba ya kasance shimfidar wannan makala, kafin daga bisani mu jero sakamakon binciken da mu ka gudanar kan amfanin jima'i ga lafiyar ma'aurata. Da fatan a sha karatu lafiya.
Shugaban kungiyar "Bunkasa tsarin iyali' Dakta Ejike Orji, ya ce, yawan jima'i na karawa ma su yin sa kuruciya, idan aka kwatanta su da sa'annunsu da ba sa aikata hakan.
Ya ce, yawan yin jima'i na kara bunkasa garkuwar jilikn dan-adam, ya sanya fata ta yi sheki sannan kuma ya rage matsananciyar damuwa.
Dakta Orji, ya bayyana haka yayin wata tattauna da kanfanin dillancin labarai na Najeriya ya yi da shi a wannan ranar Larabar da ta gabata a birnin tarayya Abuja
Sai dai Likitan ya ja hankalin wadanda ke yin jima'i ta hanyar amfani da kwayoyi da cewa, a irin wannan lokacin ba a hayyacinsu su ke ba, don haka ba za su samu amfanin da yawan jima'in ke bayarwa ba.
Ya kara cewa, akwai wani sanadari da ake kira 'Endorphins' da ke fita daga jikin dan-adam yayin jima'i wanda ke bunkasa garkuwar jiki.
Hakanan, ya ce,ma'auratan dake yawaita jima'i kan yi tsawon rai fiye da ma'auratan da ba sa aitaka hakan.
Hakazalika, ya ce, wannan sanadarin 'Endorphins' da jiki ke fitarwa yayin jima'i kan inganta sassan jikin dan-adam wanda hakan ke karawa ma'abota jima'in kuruciya.
Dakta Orji ya danganta wannan batu da wani bincike da wasu masana suka gudanar a birnin London na kasar Birtaniya.
Binciken ya nuna cewa,ma'auratan da ke yin jima'i sau biyu a sati, kan samu rigakafin kamuwa da cutukan da su kan shafi zuciya da kashi 45.
To mai karatu ka ji abin da wannan Likita ya bayyana da kuma yadda ya danganta wannan magana tasa da binciken wasu masana na kasar Birtaniya. Mu na ganin ko anan mu ka tsaya, ba shakka mai katatu zai gamsu cewa, jima'i na da amfani ga lafiyar ma'aurata. Sai dai karin kan haka akwai wasu amfanin da dama, da su ka hada da:
1. Jima'i Na Saukar Da Hawan Jini.
Binciken ya nuna cewa, yin jima'i da ma'aurata ke yi na taimaka mu su kwarai da gaske wajen saukar da hawan jini, ga ma'auratan da ke da shi hawan jinin. Idan kuma ba su dukkan su ko dayan su b su da hawan jini to jima'i na rage mu su hadarin kamuwa da shi.
2. Jima'i Na Samar Da Isasshen Hutu ga Jiki.
Duk lokacin da maigida ko ango ya dawo daga wajen harkar neman abincinsa, kasuwa ce, ofis gona ko masana'anta, ya kan kwaso gajiya, wani lokacin ma ya ji kamar an yi ma sa dukan tsiya. Maganin kawar da wannan matsala shine jima'i.
Kodayake, bayanmagidanci ya yi wanka, kuma ya ci abinci ya dan kishingida ya huta zai samu sauki kadan. Sai dai masanan sun ce, da zarar ya kusanci iyali ko shakka babu zai samu wani irin hutu da wani irin barci mai dadi da za su yi awon gaba da duk gajiya da wahalar da ya kwaso daga waje ya neme ta ya rasa.
Hakan sai ya sa ya wayi gari garau kamar ba shi ya dawo gida a gajiye ba.
3. Inganta Garkuwar Jikin Dan-adam.
Ma'auratan da ke yawan jima'i kan samu garkuwar jiki mai karfi fiye da mutanen da ba sa yin jima'i. Sakamakon ma'auratan da kan yi jima'i akai-akai kan samu yawan sinadarin 'antibiotics' a cikin jikinsu fiye da wanda basa yin jima'i.
Ma su binciken sun ce, amfanin wannan sinadarin shine kare jikin dan adam wajen kamuwa daga cututtuka da ke kai farmaki jikin, wanda idan su ka yi tasiri sai mutum ya kamu da rashin lafiya.
4. Jima'i Na Sabunta Maniyyi Ma'aurata.
Bincike ya nuna cewa, ma'auratan dake saduwa da junansu maniyyinsu na kara inganci da lafiya, sakamakon yadda jima'in kan haifar wa ma'aurata sabuntuwar maniyi bayan da su ka fitar da tsohon maniyyi yayin saduwar aure.
Hakanan dai ya na taimakawa wajen saurin samun juna biyu ga ma'auratan.
Sannan a gefe guda jima'i na kara wa uwar gida ko amarya sha'awa da ni'ima, wanda hakan kan haifar da saukin saduwa da kuma gamsar da juna lokacin saduwar aure.
5. Maganin Ciwon Gabobi:
Masanan sun bayyana cewa, jima'i na rage ciwon jiki ko gabobi ga ma'aurata. Su ka ce, a lokacin da mutum ke saduwa da iyali, idan ya yi inzili jikinsa na samar da wani sinadari da ake kira "Homone oxytocin" da turanci wanda ke taimakawa jiki ya fitar da wani sanadari mai suna "Endorphins" a turance,shi kuma ya na aiki jikin mutum kwatankwacin yadda kwayar maganin "aspirn" ko "Panadol" ke yi wajen maganin radadi ko ciwon gabobi.
6. Jima'i Na Rage Kiba/Teba:
Kamar yadda binciken masana ya nuna, jima'i wani nau'in motsa jiki ne, saboda yadda su ka ce, yin jima'i na kone wasu sanadarai, wandanda idan su ka yi yawa a jiki ba tare da amfani ba su ke haifar da kiba. Jima'i na tsawon rabin awa na kone irin wadannan sanadarai kimanin kashi 75 ko 150 na sinadarin.
Hakanan, anyi kiyasi cewa, mutum na kone kimanin wannan sanadarin har 129 ayayin da yake tafiya a kasa na tsawon rabin awa.
Kuma mun san yadda masana kiwon lafiya ke danganta yawan kiba da yin illah ga lafiya, sakamakon yadda ya ke haddasa cutuka kamar na zuciya ciwon suga da sauran su. Saboda haka yawan jima'i na taimaka wa jama'a ma su fama da kiba su rage kiba kpo teba.
7. Gyaran Fata. Yin jima'i na sa fatar jiki tayi kyau da sheki. Kuma bayani ya gabata a sama kamar yadda Likita ya bayyana ma na a shimfidar wannan makala.
8. Jima'i Na Gyara Mafitsara. Yana gyara mafitsarar mata domin ta kasance yadda ya kamata.
0 Comments