Kamin Ki Bashi Damar Ya Turo Gidanku Ki Tabbatar Da Wadannan Abubuwan Guda 5:


Kamin Ki Bashi Damar Ya Turo Gidanku Ki Tabbatar Da Wadannan Abubuwan Guda 5:

#Tsangayarmalamtonga 

Duk da ana samun wasu iyayen suke zabawa 'ya'yansu mata mazan da zasu aura, sai dai mafiya yawan iyaye suke baiwa 'ya'yan nasu damar zaban wanda suke so su aura da kansu. Wannan kuma shi abunda musulunci ya aminta da shi saboda gudun kada ayiwa yarinya auren da bata so.

Sai dai kuma duk da irin daman da iyayen suke baiwa 'ya'yan nasu na zabin wanda suke so da kansu, iyaye basu damu su daura yaran nasu akan wani ma'aunin da zasu tabbatar da mijin daya dace dasu ba kamin su gabatar da shi ko bashi damar turo iyayensa. Mafiya yawan iyaye muddin 'yarsu tace ta samu wanda zata aura abunda suka fi damuwa da su sani shine idan tana son shi da gaske. Wanda tabbatar da hakan shikenan a wajen su ta samu miji tunda dai itace tace tana sonsa.


Wannan matakine ko sakacine da iyayen da suka maida soyayya zalla ya zama shine abun auna mijin da 'yarsu zata aura.


Da yake ita kuma wacce ake son babu wani tsani da aka daurata akai na alamun mijin da zata aura, duk wanda ya zo mata da iya magana, kwalliya ko kudi shi kenan a wajenta ta samu mijin aure. 

Kada ki baiwa namiji soyayyar ki. Kada ki bashi damar ya aureki. Kada kicewa namiji ya turo gidanku har sai kin tabbatar da wadannan abubuwan kamar haka:

#SHAWARA 
1: Dagaske Yana Sonki: Maza dayawa ba abun kunya bane su furta miki kalmar soyayya, amma ba hakan suke nufi ba. Akasarin maza mayaudara da sha'awa ce ke kawosu wajen mace da kalmar soyayya suke zuwa.

Shi kuma soyayya bada fatar baki ake furta shi ba a aikace ake nunawa mutum har sai na kusa dashi bama shi da ake son ba sun tabbatar da ana maki soyaya na gaskiya. 

A darusan mu na baya mun kawo hanyoyin da mace zata fahimci na miji dagaske yake sonta da dama. Don haka ba sai mun sake nanatawa ba.

Sai dai cikin abubuwan da zaki iya fahimtar namiji yana sonki dagaske sun hada da:

Zai damu dake da kuma bukatunki. A duk lokaci yana son ji duriyarki da halin da kike ciki. Yana shiga tashin hankali a duk lokacin da yaji wani abun maradadi ko mara kyau ya samenki. Duk inda yaga wani na kusa dake yana mutuntasu.

Da zaran kin fahimci wadannan abubuwan daga mai sonki da aure akwai alamun dagaske yake sonki. Sai dai soyayyar da yake miki kadai basu isa kice ya turo ba.

2: Zuriyarsa: Kada ki cewa mai sonki da aure ya tura gidanku har sai kin samu bayani akan gidansu.

'Yan mata dayawa suna kuskuren da sakacin barin wannan bangaren a hannun wasu su musu binciken, inda daga bisani sai a musu rufa rufa da bayanin sai bayan anyi aure, ta fara jin wasu labarai game da mijin nata, danginsa ko Iyayensa da babu dadin ji.

Gaskiya ne, nasan wasu zasu ce mace bazata iya wannan binciken ba, sai dai hakan mai sauki ne a wajen macen data saka abu a ranta musamman ma idan tana da wadatan shekarun da har zata iya zabawa kanta mijin aure.

Hanyoyin da mata suke bi domin gano wacce mijinta zai auro, wannan hanyoyin mace zata iya bi ta samu bayanin namijin da take son aurensa.

Duk da yake bamu da abunda ake kira (Private Dictators) anan kasar. Wadanda mutum zai yi hayarsu su masa wani bincike na sirri su biyashi. Akwai na kusa dake da kuke da fahimta da zai iya miki wannan aikin ko ya samo miki wanda zai miki. Don haka wannan bangaren sanin tarihin asalin wanda zaki aura yana da fa'ida matuka gurin macen da take son zaman auren da bazatayi dana sani ba.

3: Sana'ar Ko Aikinsa: Akwai mata da dama sai bayan sun auri mutum suke fahimtar sana'ar sa na gaskiya ko aikinsa. Yadda mutane masu alaka da garkuwa domin neman kudin fansa yayi yawa, yana da kyau kiyi kokarin fahimtar ainihin sana'ar mutum na zahiri wanda da shine zaki aunashi, ki kuma auna rayuwarsa domin ganin ko yayi daidai da yadda yake zuwa miki.

Misali Dan sanda bai wuce mai ingiya biyu ba ko uku amma yana hawa motar miliyan 5, ana miki kyautan kudi masu yawa. Kinsan wannan dai ba albashinsa bane.

Haka wasu da Sana'o'in nasu bai kai ya kawo ba amma sai manyan hidima suke yiwa wacce zasu aura, su kuma saboda kwadayi sai su fada soyayya ba tare da la'akari da abunda zai je ya zo ba.

#Shawarace 
Hadari ne babba ki amincewa namiji yaga iyayenki baki tabbatar da aiki ko sana'ar da aka sanshi da su ba.

4: Addini Da Akida: Akwai mutane da dama da a zahiri ana musu kallon Musulmai ne kuma ana mu'amala dasu a matsayin musulmai amma sam ba musulmai bane.

Irin wadannan mutane komai nasu na musulumci ne. Wasu kakanninsu da iyayensu duk musulmai ne, amma su saboda wasu dalilai basa musulumcin a gaskiyance sai domin ganin idanuwan mutane. Ko kuma suna amsa sunan musulumcin amma babu ibada ko guda ba addinin da suke yi.

Akwai wasu musulman ne, suna komai na musulumci amma da zasu bayyana miki akidarsu a musulunci bazaki amince dasu ba.

Irin wadannan sai bayan mace ta auresu ne sannan zata fara fahimtar wasu abubuwa sabbi a wajenta. Wanda hakan zai iya sawa kodai soyayyar datake masa yasa ta biye masa ta koma akidar nashi ko kuma rabuwa ya zama itace abunyi dole wanda shine abun gujewa tun a farko.
Yana da kyau ki fito fili ki tattauna da mai sonki da aure akan zahirin addinin dayake yi da kuma akidarsa domin fahimtar juna tun kamin ki bashi damar zuwa yaga magabatanki.

5: Lafiyarsa: Wasu matan saboda suna ganin mai sonsu da aure bai taba kwanciya ciwo ba tunda suka san juna suke dauka neman sanin lafiyansa ba wani abun damuwa bane.

Sanin tarihin lafiyar wanda zaki aura yanada matukar amfani tun kamin ma ki turashi ganin iyayenki.

Banda ma maza masu kananan cututtuka da za a iya maganinsu kamin ko bayan auren ne. Akwai mazan da sun sa bazasu iya haihuwa ba, amma suke zuwa neman aure. Akwai masu ciwon kwakwaluwa. Banda wanda jininku bazai bari ku haifi 'ya'ya masu lafiya ba.

Don haka ki tabbatar kin samun takardun shedar lafayan wanda zaki aura tun ma kamin ki turashi wajen na gaba dake. 

#tsangayarnalamtonga 
Sakaci da mata ko 'yan mata suke yi da irin wadannan abubuwan idan sun tashi aure suke jefasu a kullum suke danasani kuma suke kukan maza sun yaudaresu.

Abun haushi akasarin mata sun gwammace suyi aure kona mako guda ne su fito maimakon su hakura suyi auren daya dace. Mafiya yawan mata ba matakan zaman auren suke dubawa kawai kwanciyar auren shine abunda suke zumudinsa.

Abunda yasa ki tabbatar da wadannan abubuwan da kanki kamin ki amincewa mai sonki shine, ba kowa zai tsaya ya miki wadannan abubuwan ba sai idan kinyi sa'a iyaye ko magabata masu kula.

Wasu iyayen ko magabatan daman kin ishesu kawai su suke kiyi aure duk abunda zai faru kawai ya faru.

Ki sani, illar kiyi aure ki fito yafi illar zama ba auren sauki. Don haka idan ke baki tausayawa kankiba ba kowa ne zai tausaya miki ba, har na tare dake..

Da fatan zaku daure kuyi amfani da wadannan shawaran domin amfanin kanku.

Post a Comment

0 Comments