Amfanin Kankana Ga Lafiyar Dan Adam:
🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉
SHARE 🔔
Hausawa na yiwa kankana kirari da cewa, "Kankana uwar ruwa" wannan kuwa ya dace duba da yadda manazarta da ma su bincike su ka tabbatar da cewa, fiye da kashi 90 cikin dari na kankana ruwa ne.
Sai dai, ba yawan ruwa ne ya sa kankana ta yi fice wajen yadda mutane ke mu'amala da ita ba, musamman a lokacin zafi. Baya ga haka kankana na kunshe da wadansu sanadarai ma su yawan gaske da ke da fa'ida wajen inganta lafiyar dan-adam.
Misali daga cikin amfanin da ake samu daga jikin kankana har da maganin ciwon olsa, maganin cushewar ciki da sauran su.
Na taba sauraron wata hira da wani gidan Radiyo ya gudanar da wani babban likita a daya daga cikin asibitocin kasar nan, da aka tambaye shi game da amfanin kankana ga lafiyarmu, sai ya ce, dukkan jikin kankana babu na yasarwa, kama daga kwallonta da kuma bawonta. Saboda haka, kamar yadda ya ce, dukkan ilahirin kankana na da amfani ga lafiyar jikin dan adam.
🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉
Misali binciken masana ya nuna cewa, Kwallon kankana na dauke da sanadaran proteins, vitamins, omega 3 and omega 6 fatty acids, magnesium, zinc, copper, potassium wadanda ke da matukar amfani ga lafiyar bil-adama.
1. Inganta Lafiayar Zuciya:🍉
Kankana na da amfani wajen inganta lafiyar zuciyar mutum, musamman ma kwallonta, wanda ke dauke da sanadarin magnesium, da kuma 'fatty acids'. Kamar yadda "American Heart Asociation" ta bayyana cikin wani bincike su wadannan sandarai kare wa mutum daga bugawar zuciya, da kuma rage kwalastaral na cikin jini da ke yi wa mutum illa a lafiya.
2. Gyaran Fata:🍉
Yawan cin kwallon kankana musamman idan an soya su, na da amfani wajen gyaran fata. Yana hana ko riga-kafin fitowar kurajen fata, ya na hana bushewar fata, da kuma dusashewarta, da kuma hana bayyanar alamun tsufan fata.
Wannan dalili ya sa yawan amfani da kwallon kankana na taimakawa wajen hana yankwanewar fata. Kuma wannan yana daya daga cikin dalilan da ya sa ya kamata mutane su ke cin kwallon kankana a kai a kai.
Baya ga yawan cin kwallon kankana don samun lafiyayyiyar fata mai sheki da laushi, hakanan masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa amfani da man kwallon kankana kan fata na kara inganta lafiyar fata ya hana fesowar kuraje da yamushewarta.
Hakanan, ana amfani da bawon kankana wajen gyara fuska ta yi kyau abin sha'awa. Ga mai son wannan fa'ida ta kankana sai ya ke goga bawonta a fuskarsa, idan ya bushe sai ya wanke da ruwan dumi ya shafa man Zaitun. Hakan na sa fuska tayi kyau cikin karamin lokaci.
Karanta: Yadda Za Ki Gyara Gashinki Ya Kasance Mai Tsayi, Laushi Da Kuma Sheki.
3. Karfin mazakuta:🍉
Kara dankon aure tsakanin ma’aurata, sakamakon kara karfin mazakutar namiji da zai samu damar gamsar da iyali. Binciken zamani ya tabbatar da cewa Sinadarin 'Arginine' da ke kunshe cikin kankana na kara karfin maza kamar yadda magungunan kara karfi na zamani ke yi.
4. Taimakawa Ma Su Hawan Jini:🍉
Yawan shan kankana na matukar taimakawa mutanen da ke fama da hawan jini wajen saukar sa, musamman ma kwallon kankana. Kamar yadda mu ka bayyana a sama kwallon daga cikin sanadaran da kwallon kankana ke kunshe da su akwai,yana 'vitamins, niacin, folate, thiamine, vitamin B6 and pantothenic acid. Wadannan sandarai na taimakawa ma su hawan jini ta hanyar inganta hanyoyin jini.
5. Maganin Kasala Da Samar Da Kuzari Ga Jiki:🍉
Masana na danganta yawan shan kankana da sanya kuzari a jiki. Saboda haka shan kankana musamman tare da kwallonta na kara wa jiki kuzari.
Yadda mutum zai yi amfani da kankana don samun karin kuzari shine, ya ke matse wa ruwan kankanan ya na asha, yin haka na kara kuzarin jiki, baya ga kara wa maza karfin mazakuta lokacin jima'i.
6. Yawan shan kankana na sanya rauni ko wani ciwo da mutum ya ji ya warke cikin gaggawa.
7. Gyaran Gashi:🍉
Sanadaran Protein, Iron, magnesium da copper na daga cikin muhimman sanadaran da ka iya kiransu abincin gashi. Ita kuma kankana Allah Ya hore ma ta wadannan sanadarai ma su yawan gaske a cikinta. Saboda haka ne yin amfani da kankana akai-akai a kan inganta lafiyar gashinki, musamman ma ga matar da ke fama da zubewar gashi.
Kamar yadda binciken ya nuna, sanadarin 'Protein' na kara yawan gashi, shi kuma 'magnesium' yana hana zubewar gashi, yayain da shi kuma sanadarin 'Copper' ke ƙara sheki da yalyalin gashi.
8. Saurin Murmurewa Daga Lafiya; Lokacin da mutum ya warke daga wata rashin lafiya da ya yi, idan ya juri amfani d kankana jikinsa zai yi saurin farfadowa.
🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉
9. Yawan Shan Kankana na taimaka wa mutum ya sam isasshen barci.
10. Kara Karfin Garkuwar Jiki; Kamar yadda bincike ya nuna kankana na kunshe da sanadarin Bitamin C, wanda ke kara karfin garkuwar jiki, sakamakon haka sai kare jiki daga kamuwa daga cututtuka.
11. Karawa Mata Ni'imar Jima'i:🍉
Kankana ta shahara wajen karawa mata ni'ima yayin saduwar aure. Idan mace na fama da rashin ni'ima ko bushewar gaba, sai ta yi amfani da kankana don maganin wannan matsala.
Yadda kankana ke karawa mata ni'ima shine, uwargida ki samu kankana ki yanka ta sannan ki cire wallon ki samu dabino ki saka daga nan ki markada su, sai ki samu zumarki mai kyau marar algus, ki zuba sannan ki hada da madara, sai ki adana kayanki cikin furej yayi sanyi ki sha. Daga bisani sai ki samu kobawon kankanar ki shanya shi har sai ya bushe, bayan kin yi wanka sai ki turara farjinki da shi. Wannan hadi na saurin karawa mace ni'ima sannan ya na kara ma ta sha'awa da kuma gamsar da mai-gida. Don karin bayani game da magungunan karin ni'ima karanta makalar da mu ka rubuta mai taken "Magungunan Karin Ni'ima Don Ma'aurata"
12. Yawan shan kankana na kara inganta lafiyar Koda:🍉
13. Daga cikin amfanin kankana ga lafiyar dan adam, akwai kare wa mutum daga hadarin kamuwa da ciwon daji.
14. Maganin Gyambon Ciki (Ulcer); kamar yadda mu ka ambata a farkon wannan makala, daga cikin amfanin kankana ga lafiyarmu har da maganin olsa wato gyambon ciki. Idan mutum na son amfanuwa da kankana wajen maganin gyambon ciki, sai ya ke shanta kullum da safe kafin ya ci abinci.
15. Shan kankana na rage hadarin kamuwa da ciwon zuciya.
🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉🍉
0 Comments