Amfanin Citta Guda 13 Ga Lafiyar Dan-adam:



Amfanin Citta Guda 13 Ga Lafiyar Dan-adam

SHARE 🔔
☕☕☕☕☕☕☕☕☕☕☕☕☕☕☕
Ba wai kawai citta na cike da 'antioxidants' ba ne, amma ana yin amfani da ita wajen hada magungunan ciwon jiki da na inganta lafiya a dukan fadin duniya, daruruwan shekaru da su ka wuce. Misali al'ummar kasar Misra na amfani da Citta don maganin ciwon gabobi, zafin jiki, hana kumburi, da kuma hana amai da tashin zuciya.

Muna da kyakkyawan zaton cewa, mai karatu ba ya bukatar karin bayani game da citta saboda yadda mu ke mu'amala da citttar wajen girkin abincinmu yau da kullum. Sai dai amfanin citta bai tsaya ga sanya kamshi da dandanon abinci ba, kari kan haka citta na kunshe da wasu muhimman sanadarai inganta lafiyar dan adam, da kuma ba shi kariya da kamuwa daga wasu cututtuka.

Ba tare da bata lokaci ba, shafinku mai farin jini na "Lafiyar Iyali" ya jero mu ku amfanin citta guda goma sha uku (13) ga lafiyar dan-adam. Da fatan a yi karatu lafiya. Allah Ya sa mu dace, amin.


1. Maganin Ciwon Jiki.

Mun bayyana a sama cewa, shekaru aru-aru da su ka shuda, al'ummomi daban-daban na duniya ke amfani da citta don maganin ciwon gabobi, baya ga ciwon gabobi, har ila yau, su na amfani da citta don maganin ciwon jiki, kuma haka al'amarin ya ke har a gobe. Saboda citta na da wasu sanadarai da ke hana ciwon jiki sakamakon aikin karfi ko na gajiya da aka gudanar.

Ɗaya daga cikin binciken da aka wallafa a mujallar 'Journal of Pain' ya gano cewa, mutanen da ke wasannin motsa jiki na yin amfani da hadin da aka sarrafa daga citta don maganin ciwon jiki bayan sun kammala wasannin motsa jiki.

Hakanan, mutanen da ke son su wayi gari cikin kuzari da walwala, ba sa kwantawa barci ba tare da shan shayin da aka hada da citta ba. Yin hakan kan sa su wayi gari cikin kuzari da walwala.

2. Maganin Rudewar Ciki
Idan ka tattauna da wanda ya lizamci shan shayin da aka hada da citta, zai ba ka labarin yadda cikinsa ke kasancewa cikin koshin lafiya. Kuma kai kanka da za ka ke yin amfani da citta da za ka gane amfanin cittar wajen samar da lafiyar ciki, saboda ta na maganin rudewar ciki, tashin zuciya, kwarnafi da sauran su.

Wani mai wallafa rahotanni kan kiwon lafiya mai suna, Marissa Miller, ya bayyana amfanin citta ga lafiyar dan-adam da cewa, abin sha ne mai kyau da ya kamata mutane su ke sha, musamman bayan cin abinci mai nauyi.

"Shan Kofi daya na shayin citta, zai iya taimakawa mutum ya samu lafiyar ciki sauri, musamman a yanayin da ya ci abinci mai nauyi, don kuwa za ta taimaka ma sa wajen samun sassaucin cikinsa," inji Kamar Miller.


3. Maganin Ciwon Mara Lokacin Jinin Al'ada:

Saboda yadda masana ke kiran citta da "anti-inflammatory" ya sanya ta ke taimakawa wajen maganin ciwon marar mata lokacin da su ke jinin al'ada.

 Manazarta sun ce, dangane da maganin ciwon mara lokacin jinin al'ada citta na aiki kwatankwacin maganin nan na zamani mai suna 'Ibuprofen'. Wannan sakamakon wani bincike da aka gudanar ne a shekara ta 2009, sannan aka buga a wata mujalla mai suna "Journal of Alternative and Complementary Medicine".

Wannan wani labari ne mai dadi ga dukan matan da ke fama da ciwon mara a lokacin da suke jinin al'ada. Da zarar kin ji ciwon ciki idan al'adarki ta zo, shan kofi daya na shayin citta kawai zai iya taimaka miki ki samu sauki, kuma ki ci gaba da harkokinki.


4. Maganin Sanyi da Mura:

Hakika citta ta yi fice wajen maganin matsalolin sanyi da mura saboda wasu sanadarai da cittar ke kunshe da su, sakamakon haka ne ya sa cittar ke iya taimaka wa wajen yaki da sanyi ko kamuwa da cututtukan makogoro.

Domin maganin matsalar mura, "Ka zuba babban cokali biyu na tacaccen ruwan danyar citta, cikin ruwan zafi kofi daya, da lemon tsami guda daya, sannan ka zuba cokali daya na zuma," in ji Miller. ka sha wannan hadin citta safe da yamma. "Ko kuma, ka zuba citta babban cokali daya cikin romon da aka dafa kaza don maganin mura, ko kuma riga-kafin kamuwa da sanyi."

5. Inganta Lafiyar Kwakwalwa:

Wani bincike da manazarta su ka gudanar a shekara ta 2011, kuma aka wallafa a mujallar "Evidence Based Complementary and Alternative Medicine" ya nuna cewa citta na da wasu muhimman sanadarai da ke taimakawa kwakwalwa ta yi aikinta yadda ya kamata.

Baya ga taimakawa kwakwalwa yin aikinta yadda ya dace, haka kuma cittar ke taimawa wajen hana mantuwa, sakamakon inganta lafiyar kwakwalwarmu. A takaice dai ka iya cewa, citta na kara kaifin basira ga dan-adam.



6. Rage hadarin Kamuwa Da Cutar Daji
Akwai wasu bincike da masana da yawa su ka gudanar, kuma sun nuna cewa, citta na da wasu sanadarai da ke bai wa jiki kariya wajen kamuwa da ciwon daji, kuma binciken ya nuna citta na kunshe da wadannan sandarai ma su yawan gaske.

Wani nazari da masana kiwon lafiya su ka gudanar a shekara ta 2012, kuma aka buga a jaridar "British Journal of Nutrition", ya gano cewa, citta na da tasiri kwarai wajen hana kamuwa da ciwon daji. Kodayake, binciken na matakin farko ne, a lokacin da jaridar ta wallafa sakamakon binciken, amma ana fatan samun ci gaba a wannan fannin.

7. Saurin Narkar Da Abinci:

Wani lokacin mu kan samu kanmu cikin tsanani idan mu ka ci abinci, amma ya ki narkewa akan kari, Yanzu an gano za a iya amfani da citta don shawo kan wannan matsalar. Kofi daya na shayin citta zai iya taimakawa wajen narkewar abinci cikin sauri, kamar yadda Dokta Christy Brissette, wani likita a fanni abinci mai gina jiki ya bayyana.


8. Maganin Amai Da Tashin Zuciya
Wani bincike ya nuna cewa, citta na taimakawa wajen maganin amai da tashin zuciya, shin aman ko tashin zuciyar na larura ne da ke faruwa sakamakon wata rashin lafiya ko kuma amai ne ko tashin zuciya irin na mata ma su ciki ?. A kowanne yanayi citta na taimakawa.

Shan kofi daya na shayin citta, wanda aka hada da cokali daya na zuma na bayar da sakamako mai kyau, kamar yadda masanan su ka bayyana.

9. Ragewa Kwalastaral Maras Kyau
Wani manazarci mai suna, Brissette ya bayyana cewa, citta na iya taimakawa wajen rage yawan 'cholestero lLDL' marar kyau, wanda hakan kuma ke rage yawan hadarin kamuwa da cutukan zuciya. Wani binciken da aka gudanar kwanan nan ya tabbatar da sakamakon wannan binciken, inda ya nuna cewa, wani rukunin mutane da aka gudanar da binciken a kansu, sun kasance su na cin giram 3 na citta, kwatankwacin rabin karamin cokali, sau uku a rana sun sami raguwar 'cholesterol' a jikinsu fiye da rukunin da ba sa cin cittar.


10. Inganta Lafiyar Zuciya:

Kamar yadda ya ke rubuce a sama cewa, bincike ya tabbatar da yadda yin amfani da citta ke rage yawan Kwalastaral marar kyau a jikin mutum, sannan, binciken ya nuna cewa, yawan kwalastaral a jiki ko akasin haka na da kyakkyawar dangantaka da lafiyar zuciyar dan-adam. Saboda haka tun da citta na iya rage yawan kwalastaral marar kyau a jikin mutum, ba shakka hakan na kara inganta lafiyar zuciya, ta yi aikinta yadda ya kamata, sannan ta samu kariya daga cututtukan da kan shafi zuciyar.

11. Bunkasa Garkuwar Jiki:

Amfanin citta ga lafiyar dan adam ya hada da kara karfin garkuwar jikinsa. Bincike ya nuna cewa, amfani da citta na bunkasa garkuwar jikin mutum yadda za ta iya yaki da cuta idan har ta kawo wa jiki farmaki.

 Hakanan, cittar na taimaka wa mutum saurin murmurewa daga rashin lafiya.

Domin samun wannan fa'ida ta citta, sai ka zuba babban cokali biyu na ruwan citta da aka matse cikin kofi daya na ruwan zafi, sai ka zuba ruwam lemon tsami guda daya da ka matse, sannan ka zuba babban cokali daya na zuma mai kyau. Wannan hadin za ka sha sau biyu a rana, wato safe da kuma yamma kenan.


12. Maganin Ciwon Gabobi:

Tun a farkon wannan makala mun bayyana cewa, shekaru aru-aru da su ka shuda, al'ummomi daban-daban na duniya ke amfani da citta don maganin ciwon gabobi, to haka al'amarin ya ke har a gobe, ana amfani da citta wajen maganin ciwon gabobi. Saboda citta na da wasu sanadarai da ke hana ciwon gabobi sakamakon aikin karfi ko na gajiya ko kuma wasannin motsa jiki da mutum ya gudanar.

Ɗaya daga cikin binciken da aka wallafa a mujallar 'Journal of Pain' ya gano cewa, mutanen da ke wasannin motsa jiki na yin amfani da hadin da aka sarrafa daga citta don maganin ciwon gabobi, bayan sun kammala wasannin motsa jiki.


13. Maganin Kaikayin Makogwaro Da Toshewar Hanci:

A lokacin da mutum ke fama da toshewar hanci ko kaikayin makogwaro sai ya nemi citta ya sarrafa ta don samun sauki, sakamakon yadda bincike ya nuna cewa ta na da wasu muhimman sandarai da ke wannan aikin.

Yadda zai yi shine, ya hada shayi da danyar citta bayan ya kirba ko dandaka cittar, sai ya zuba ruwan lemon tsami guda daya da ya matse, sannan ya zuba zuma cokali daya ya sha.
🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾🌾

Post a Comment

0 Comments