RASHIN AURE DA WURI GA SAMARI DA YAN MATA:



RASHIN AURE DA WURI GA SAMARI DA YAN MATA:


An yi mummunar fahimtar ma’anar yin aure da wuri yayin da wasu suka dauka shi ne yi wa yarinya karama aure koda kuwa ba ta isa zaman aure ba kamar yadda muke gani a mafi yawan kauyuka da zamu ga ana yi wa yara mata aure da ba su san ma’anar rayuwa ba. Wannan lamari ya kawo yaduwar karancin ilimi cikin al’umma, da karancin sanin yadda ya kamata a tarbiiyantar da yara manyan gobe, domin idan matar gida ta kasance ba ta san ma’anar rayuwa ba to ba ta da wata kwarewar yadda zata yi tarbiiyar ‘ya’yan da ta haifa. Masu wannan tunanin sun dogara da tarihin da wasu marubuta suka kawo na cewa annabin rahama (s.a.w) ya tare da A’isha tana shekara 9 ne alhalin mafi ingancin magana tana kusan shekaru 18 ne.

Sannan ga matsalar cututtukan yin aure da wuri da suke haifuwa ga ‘yan mata da yana daga cikin abubuwan da suke teburin tattaunawa a gun likitoci da hakkin ‘yan mata, da yawa irin wadannan halaye sun salwantar da rayuwar ‘yan matan ko illantarwa. Amma wani lokaci kuma akan samu wasu mutane da sukan dade ba su yi aure ba har samartakarsu ta tafi, masu ilimi sun kawo wasu abubuwa da sukan kawo jinkirin aure kamar haka:

1- Tsawon muddar lokacin karatu ta yadda saurayi ko budurwa kafin ya kai ga kammala jami’a ya kai shekara talatin zuwa talatin da biyar a mafi yawan lokuta, sau da yawa wannan yakan jefa wasu cikin halin da suka katse karatu idan ba zasu iya hada biyun ba, don haka yana kan al’umma da gwamnatocinsu su yi tunanin maganin wannan koda ta hanyar tallafi ne ga ‘yan makaranta. A wasu kasashen akan yi irin wannan taimakon, a Farisa kakan samu masu ikon kasa sukan yi kokarin yi wa dubunnan daliban jami’a aure a kyauta kowace shekara tare da ba su tallafi.

2- Samun Damar yin Alakar Haram: Sau da yawa yawaitar gidajen karuwai da wajajen fasikanci yakan sanya wasu samari su ga ya fi musu sauki su je su yi mummunar mu’amala ta haram da matan banza na wani dan lokaci tsawon rayuwar samartakarsu. Wannan ma wani abu ne da musulunci ya sanya mafita gare shi ta hanyoyi da dama kamar haka.

a- Tallafin aure da wuri daga Baitul Mali ga duk wanda ba zai iya aure ba kuma da bukatar hakan domin ya balaga.

b- Tarbiiyantarwa ta hannun malamai da kafafen watsa labaru da jaridu da makarantu.

c- Hana gidajen fasadi da kulle duk wani waje da ake ashararanci, ko yi musu gyara ta yadda zasu koma gidajen aure mai lokaci.

d- Wayar da kan mutane a ilmance domin su san illar wannan mummunan hali da abin da yake jawowa.

e- Idan ma’abota wannan halin ba a shirye suke su yi aure ba koda kuwa suna da yalwa, to musulunci har yanzu ya ba su damar yin auren mutu’a, don haka ne ma idan irin wadannan wajajen ba zasu kullu ba, sai wadannan mata masu zaman kansu su tuba daga wannan aiyuka, maimakon su rika zina sai su yi auren mutu’a da duk wanda suke so, bayan muddar ta kare sai su yi idda.

Wasu malamai suna ganin gwamnatin musulunci tana iya mayar da gidajen banza su koma gidajen shari’a ta wannan hanya, musamman gudun cewa idan aka kori irin wadannan mutane to zasu koma suna fasikanci a boye, maimakon haka sai su tuba su bi hanyar da shari’a ta gindaya musu.

3- Rashin Yalwa da Talauci da Tsadar Aure: Yana daga cikin abin da kan kawo jinkirin aure ga samari, don haka bai kamata ba a bi al’ada da kuntatawa da tsanantawa ga kudin aure da zata kai ga wannan jinkiri har zukatan samari da ‘yan mata su gurbata da zogin bakin ciki ko miyagun halaye, sau da yawa jinkirin yana faruwa sakamakon wasu abubuwa kamar haka.

a- Sanya sharuda masu wahala ga saurayi.

b- Yawan kudin da zai kashe kan kayan tanadin gida da sauransu.

A game da matsalar farko, al’umma ne ya kamata su sanya hannu wajen warwareta, amma matsala ta biyu al’umma da hukuma ne zasu sun sanya hannu wajen maganinta.

4- Karancin amintuwa da juna tsakanin saurayi da budurwa, musamman akan samu wasu da yawan munana zato ga duk wanda suka hadu da shi, ta yadda yakan yi musu wahala su yarda da shi[1].

Ta wani bangaren kuma wani lokaci jinkirin yakan taso ne saboda ruwan ido ko kuma tsanantawa wajen sharudan saurayi ko budurwar da zasu aura wanda wannan ya kan daukar musu tsawon lokaci ba su samu mai wannan sharudan ba ko ma su kasa samun mai wadannan sharudan. Mu sani binciken halin wanda za a aura saurayi ne ko budurwa yana da kyau, amma kada ya kai ga matsananci da zai fita daga matsakaicin lamari. Warware wannan matsalar yana hannun samari da ‘yan mata ne.

Matsaloli Kafin Aure

Wasu daga Matsalolin da saurayi ko budurwa kan iya fuskanta kafin aure da sukan iya yin tasiri kan auren ko su kai ga fasa kulla shi, wannan matsalar wani lokaci saurayi da budurwa sukan fuskanci matsala ne daga su kansu, wani lokacin kuwa daga danginsu ko wasu jama’a da suke da tasiri kan lamarin ko da kuwa ba danginsu ba ne.

1- Burin da kowane bangare da iyayen saurayi da budurwa, ko su kansu saurayi da budurwa suke ci kan junansu. Kamar kayan daki da yake tunanin a kawo ta da shi da sauransu ko kuma kayan da take tunanin ya kai gidansu.

2- Nau’in sadakin da ake aiyanawa ko kuma in ce kayan mun gani muna so da lefe a al’adunmu da ake sanyawa a kan saurayi idan suna da yawa yakan sanya jinkirin aurensa.

3- Kudaden kashewa domin bikin aure da sau tari zamu ga al’ada ce take kallafa su, kuma sau da ya wa suna zarta asalin abin da shari’a ta gindaya.

4- Tsanantawa wajen binciken laifuffukan juna ta yadda wani lokaci za a fake da wani karamin laifi domin tarwatsa lamarin, ko kuma a yi auren amma sai ya zama karamin laifin ya zama abin korafi. Wani lokaci ma yana iya zama sanadin fasa auren idan aka samu wadanda ba sa son kulla shi a tsakiya.

5- Binciken matsayin dangin juna ta fuskacin wani mukami ko dukiya, wannan yana faruwa idan gidan da ake neman ‘yarsu suna ganin kansu a matsayin ajin farko na masu matsayi a al’umma, ko kuma iyayen ango su rika korafin dansu zai yi aure a karamin gida.

6- Makahon so da zai rufe idanuwan juna da zai sanya kowanne ya kasa ganin laifin dayan domin a lokacin suna kishirwar juna, amma da zaran sun kawar da wannan kishirwar sha’awar sai a gane laifin juna. Da man burinsa shi ne ya san ta a matsayin ‘ya mace shi ke nan sai ya yi wurgi da ita.

7- Zargin juna da sukan yi ko son gaskiya ne ko na karya tsakanin duka bangarorin biyu na saurayi da budurwa, ta yadda dayansu yakan ji tsoron ko son gaskiya ko na karya dayan yake yi masa, ta yadda a nan gaba dayan su zai yi watsi ya yi wurgi da abokin zamansa[2].

Matsalolin Rashin Aure

Sau da yawa mukan ga samari da ‘yan mata da yawa sun samu lalacewa sakamakon rashin yin aure da wuri, domin idan mutum ya balaga yakan zama kamar danyar itaciya ce da idan ba a shayar da ita ba sai ta bushe. Sau da yawa wannan al’amari na halitta ya sanya wasu suka kasa juriya, suka gajiya gaban sha’awarsu, suka sallama mata, al’amarin da yakan janyo fasadi mai girma a cikin al’umma.

Daga cikin irin wannan fasadi zamu yi kokarin kawo misalin abin da yake daya ne daga ciki da ake cewa da shi istimna’i. Istimna’i wata mummunar dabi’a ce da takan samu samari ko ‘yan mata masu tashen balaga da sukan yi amfani da jikinsu ko hannunsu ko kayansu ko wani abu domin fitar da maniiyi daga gare su. Babbar musifar da istimna’i yake jawowa ta hada da:

1- Rauni da rashin karfin jiki;

2- Raunin kwakwalwa da kasa rike karatu ko kadan;

3- Rasa gani da makancewa daga karshe;

4- Karkarwar jiki;

5- Rashin nutsuwa;

6- Yawan tunani;

7- Son warewa waje daya, da kebewa;

Maganin Istimna’i

Malamai sun kawo wasu abubuwa da suke maganin wannan mummunan ciwo mai haifar da miyagun halaye da munanan dabi’u kamar haka.

1- Nisantar duk wani abu mai kawo sha’awa, kamar kallon fila-falai da mata suke rawa ko suke sanya kayan da bai dace ba da duk abin da ya san yana sanya shi jin sha’awa.

2- Shagaltar da kansa da wasu abubuwan, kamar tsara lokutansa na karatu da na zuwa filin wasa, ya kuma rika yin wasan motsa jiki da karanta littattafai kamar na ilimi ko jaridu, da zuwa wajan hutawa da shakatawa domin ya samu saukin kuncin ransa, da ware lokacin da zai rika yin yawace-yawace a lokacin da ba shi da komai, da yawan karanta Kur’ani koda fatiha ce a kan hanyarsa, da zuwan wajen tarurrukan wa’azi da shirya irinsu, da yawaita zuwa masallaci a lokacin kowace salla.

3- Sanya wa kansa aiyukan da zasu cike lokacin hutawarsa.

4- Kula da wasannin motsa jiki kamar gudu a filin wasa, daga abubuwa masu nauyi, iwo a ruwa, da sauransu;

5- Idan akwai lokutan da ya saba aikata wannan mummunan hali a cikinsu sai ya kirkiro wa kansa wani abu daban da zai shagaltar da shi a irin wadannan lokutan kamar zuwa hawan sukuwar doki ko iyo da sauransu.

6- Ya nisanci zama shi kadai har abada koda bacci zai yi to ya kasance cikin mutane ta yadda idan ba wani abu na lalura ba kamar kama ruwa da bahaya to ba yadda za a yi ya kasance shi kadai.

7- Da zarar ya samu yalwa da dama to ya yi maza ya yi aure kada ya jinkirta ko kadan.

8- Raya karfin ruhinsa ta hanyar jin cewa zai iya maganin wannan halin da taimakon Allah.

9- Nisantar masu irin wannan halin nasa.

10- Cin abinci mai kyau da tsara lokutan cinsa ta yadda ba ko da yaushe ne zai ci wani abu ba, da kuma wanka da ruwan sanyi a wasu lokuta, da nisantar sanya tufafi masu matse masa jiki.

11- Addu’a da neman taimakon Allah, da jin cewa Allah yana ganin sa duk inda yake koda ya shiga daki ya rufe ne shi kadai, ya ji cewa kuma Allah zai yafe masa abin da ya yi, kuma ya daukar wa Allah alkawarin ba zai sake ba[3].

Wasu Hanyoyin

Wasu malamai sun kawo hanyar maganin wannan mummunar dabi’a ne kamar haka:

1- Ya san cewa istimna’i yana daga zunubai da aka yi alkawarin azaba ga mai yin sa[4].

2- Ya san cewa mutane zasu kyamace shi idan suka san yana yin sa[5].

3- Ya taimaka wa kansa da yin azumi domin dawo da karfin iradarsa.

4- Ya shagaltu da mudali’ar littattafai da nau’o’in wasanni kamar wasan gudu da tseran doki da sauransu.

5- Iyaye su kula da tarbiiyar ‘ya’yansu tun farkon rayuwarsa ta yanda zasu kula da duk halayensu domin gyara da ba su tarbiiya ta gari.

6- Dole ne al’umma da hukuma su bayar da muhimmanci na musamman kan sha’anin aure.

7- Mai wannan halin ya duba irin bala’in da yake fada masa na cututtukan ruhi da na jiki kamar cututtukan fata, rashin jin cikakken dadin kusantar mace, rashin matsayi a al’umma saboda matsalar jijiyoyi da gajiyawar jiki da sauransu[6].

Mu sani yawan duba littattafan hikima da na ilimi[7], da yawan tafiye-tafiye[8], da wasannin motsa jiki[9], da koyon harbe-harbe, da koyon sukuwar doki, da iyo a ruwa, suna daga cikin abubuwan da suke karfafa ruhin mutum[10], kuma suna kawo lafiyar jiki da ta ruhi da nishadi ga rayuwar mutum kamar yadda suna kawo farin ciki da annashuwa.

Sha’awa Mai Yawa

Daga cikin shawarwari da aka bayar ga mai yawan sha’awar da ta fita daga al’ada, musamman wadanda sha’awarsu ta kai su ga lalacewa da babu wani haramun da ba zasu iya bari ba ta hanyar biyan bukatarsu ta haram, sun hada da:

1- Tunawa da munin wannan hali, da abin da yake haifarwa na cututtukan ruhi da jiki da jawo wa mai wannan hali saurin tsufa da mutuwa a rayuwarsa ta duniya.

2- Karya karfin sha’awarsa da yawaita yin azumi, da zama da yunwa, da karanta cin abinci[11].

3- Kokarin ganin ya yi maganin duk wata hanya da takan iya kai shi ga jin sha’awa, kamar; tunanin abubuwan da sukan jawo masa sha’awa, da magana da mata, da kallon mata, da kebewa da mace, da kallon fila-filan banza, da duk wani abu da zai iya sanya shi jin sha’awa.

4- Yin amfani da hanyoyin da zasu hana shi aikata haram da sha’awarsa kamar gaggauta yin aure da zaran ya samu dama; auren da’imi ne ko kuma na mutu’a.

5- Tuna ni’imar da Allah yake ba wa wanda ya bar sha’awarsa ya ki aikata haramun da ita saboda Allah.

6- Sanin cewa wannan siffa ce ta dabbobi shi kuwa mutum ne bai kamata ba ya zama kamar dabba domin shi an halicce shi ne domin kamala.

7- Ya yi duba da tunani da lura zuwa ga ayoyin Kur’ani da ruwayoyi da suka kwadaitar da tuba suka kuma zargi mai wannan hali[12].

8- Ya yawaita karatun Kur’ani da karanta litattafan ilimi na hikima, da yawaita addu’a da jin cewa shi zai iya barin wannan hali, hada da matakan da muka ambata a sama.

 

Hafiz Muhammad Sa’id

Haidar Center for Islamic Propagation

Post a Comment

0 Comments